Za a iya janye tallafin man fetur a kowanne lokaci a Najeriya - NNPC

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran ƙasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. 'Saudiya na min barazana kan binciken kisan Jamal Khashoggi'

    Google

    Asalin hoton, Google

    Ofishin hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da wani bayani da kwararriyar da ke jagorantar binciken kwakwaf kan kisan dan jaridar nan na Saudiyya Jamal Khashoggi, na zargin cewa wani babban jami'in Saudiyya ya yi mata barazana ga rayuwarta.

    Kakakin hukumar Rupert Colville ya tabbatar da cewa bayanan da aka wallafa a jaridar Guardian gaskiya ne kan baranar da aka yi wa Agnes Callamard, cikin wani sakon email da aka turawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    A ranar Talata ne jaridar Guardian ta ruwaito Callamard na cewa wani babban jami'in Saudiyya ya mata barazanar cewa za a yi maganinta matukar "ba ta dakata da" gudanar da bincike ba kan kisan da aka yi wa dan jaridar.

    Colville ya kara da cewa ofishin ya sanar da Callamard cewa hukumomi da kuma bangaren tsaro na MDD na sane da abin da ya faru.

  2. 'Yan bindiga sun kona makarantu da asibitoci a jihar Tillaberi

    Bayanan sautiLatsa nan don sararon rahoto kan harin da aka kai jihar Tillaberi a Jamhuriyar Nijar

    'Yan bindiga sun kai hari a garin Zibane na yankin Anzourou a jihar Tillaberi da ke Jamhuriyar Nijar inda ke iyaka da kasar Mali.

    Maharan sun kashe mutane da dama tare da kona azuzuwan makarantu da asibiti.

    Sai dai zuwa yanzu gwamnati ba ta tabbatar da labarin ba. Hakan na zuwa ne yayin da kasashen duniya suka fara bayyana kudurinsu na kara kawo taimako ga jamhuriyar Nijar game da shirinta na yaki da ayyukan ta’addanci a kasar.

    Kasa ta baya-bayan nan da ta bayyana kudirin kawo taimako ga Nijar din ita ce Beljiyum, ta bakin jakadanta a lokacin wata ganawa da Fara-ministan ta Nijar a Yamai babban birnin kasar.

  3. An hukunta mutum 22 bisa samunsu da laifin lalata a Edo

    BBC

    Gwamnatin jihar Edo da ke kudancin Najeriya ta yankewa mutum 22 hukunci bisa samunsu da laifin lalata, kuma za ta gurfanar da wasu 160 gaban shari'a.

    Wani babban darakta kare hakkin 'yan kasa a ma'aikatar shari'a ta jihar Mista Oluwole Iyamu ne ya bayyana hakan a Benin yayin wani taron masu ruwa da tsaki da wata gidauniyar agazawa mata ta shirya.

    Iyamu ya kara da cewa yana da kwarin gwiwar gurfanar da wadannan masu laifin da aka yi zai taimaka wajen rage cin zarafi a jihar.

    "Mun samu nasarar gurfanar da mutum 22 tun daga watan Satumbar 2020, kuma muna nan muna kokarin gurfanar da wasu 160, hakan dai zai taimaka wajen dakile harkokin a jiharmu." In ji Iyamu.

  4. Budewa

    Barkanmu da safiya tare da fatan an wayi gari lafiya a duk inda kuke a fadin duniya.

    Buhari Muhammad Fagge ne ke fatan kawo muku labarai da rahotanni da dumi-duminsu a wannan yini.

    Labaran da suka shafi nahiyar Afrika da Turai da Asiya har da Amurka, ku kasance da mu.