Mutuwar Magufuli: An ɗauke tauraruwa mai haske daga Afirka - Goodluck Jonathan

Asalin hoton, @GEJonathan
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi alhinin rasuwar shugaban Tanzania John Magufuli, yana mai bayyana shi da "abokin dimokuraɗiyya" kuma "ɗan kishin ƙasa wanda ya so ƙasarsa".
Jonathan ya miƙa ta'aziyyar ne a shafinsa na Twitter. "An ɗauke wata tauraruwa mai haske daga Nahiyar Afirka," in ji Jonathan.
A jiya Laraba shugaban ya mutu sakamakon ciwon zuciya kuma nan gaba a yau za a rantsar da mataimakiyarsa Samia Suluhu domin shugabantar Tanzania.
Idan ta sha rantsuwa, za ta zama shugaba mace ta farko a ƙasar sannan kuma mace ta farko Musulma a matsayin shugabar ƙasa a Afirka.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X




