An yi wa gwamna El-Rufai allurar rigakafin korona

Wannan shafi ne da yake kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur

  1. Za a fara yi wa mutane allurar riga-kafin cutar korona a Kano

    Gwamna Ganduje

    Asalin hoton, KANO GOV

    Gwamnatin jihar Kano ta karbi allurar rigakafin Korona 209, 520.

    A lokacin da yake karbar allurar rigakafin a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano, a madadin Gwamna Ganduje, kwamishinan lafiya, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce allurar rigakafin kashin farko zai fi mayar da hankali ne kan ma’aikatan lafiya da ke jahar.

    Jami’ar hulda da jama’a ta ma'aikatar lafiya a Kano, Hadiza Namadi ta tabbatar wa da BBC karbar riga-kafin.

    Sannan nan ba da jimawa ba za a yi wa gwamanan jihar Abdullahi Umar Ganduje allurar rigakafin.

    Sai dai kwamishinan ya ce kwamitin yaki da cutar ta korona a jihar nan gaba zai sanar da lokacin da za a fara riga-kafin ga kowa da kowa a jihar.

  2. Mutum 346 sun kamu da cutar korona a Najeriya ranar Talata

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 346 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Talata.

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, a wannan rana, jihar Legas ce ke kan gaba a jerin jihohin da aka samu ɓullar cutar da mutum 86 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

    Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 64 a Bauchi, da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.

    A Kaduna da Kwara, mutum 26 sun kuma kowacce jiha sai Birnin Tarayya Abuja da aka samu mutane 24 da aka tabbatar sun kamu da Rivers da aka samu mutum 23.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Buɗewa

    Barkanku da safiya. Da fatan kun wayi gari lafiya.

    Ku kasance da wannan shafin mai kawo maku labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran kasashen duniya.