Masu zanga-zanga sun tsere wa samamen ƴan sanda a Myanmar

Asalin hoton, Getty Images
Dubban masu adawa da sojojin Myanmar sun ce sun yi nasarar tserewa samamen cikin dare da jami'an tsaro suka yi a wata gunduma mafi girma a Yangon, babban birnin ƙasar.
Masu fafutuka sun tsinci kansu a maƙale a gidajen da ke Sanchaung bayan ƴan sanda sun sanar a ranar Litinin cewa za su bi gida-gida su yi bincike don gano waɗanda ba ƴan gundumar ba.
Sun yi gargaɗin hukunta duk wanda suka kama yana bai wa masu zanga-zanga mafaka.
Rahotanni na cewa an tsare kimanin mutum 50.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta jagoranci kiraye-kirayen a dakatar da matakin.
Wasu daga cikin waɗanda suka tsere sun yi alƙawarin ci gaba da zanga-zangar da suke yi.
