Mata sun fi fuskantar cin zarafi daga abokan zamansu - WHO
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Fauziyya Kabir Tukur and Awwal Ahmad Janyau
Masarautar Birtaniya ta ce ta damu kan batun Yarima Harry da matarsa
Masarautar Buckingham ta ce batutuwan da aka taso da su a tattaunawar da aka yi da Yarima Harry da matarsa Meghan, abin damuwa ne musamman kan batun wariya.
Wannan shi ne karo na farko da masarautar ke mayar da martani tun bayan haska tattaunawar a ranar Lahadi.
Sanarwar a madadin Sarauniya Elizabeth, ta ce duk da cewa tunaninsu na iya banbamta, batun da ya taso kan wariya ba abin wasa ba ne, don haka an dauke shi da muhimmanci domin shawo kan matsalar a cikin gida.
Sannan ta ce Harry da Matarsa da kuma jikanta za su ci gaba da samun soyayya daga iyalan masarautar.
A lokacin tataunawar Meghan ta bayyana irin kunci da ta shiga a zamanta a masarautar da musamman nuna mata wariyar launin fata da kuma abin da ta haifa
Daga ciki har da tambayar yadda kalar dansu zai kasance na bakar fata da tunanin kashe kanta da ta rinka yi a wannan lokacin saboda akuba.

Asalin hoton, HARPO PRODUCTIONS - JOE PUGLIESE
Mata sun fi fuskantar cin zarafi daga abokan zamansu - WHO

Wani sabon rahoto na Hukumar Lafiya ta Duniya ya gano cewa kashi ɗaya bisa uku na matan duniya na fuskantar cin zarafi a wani mataki na rayuwarsu.
Rahoton shi ne mafi girma da aka taɓa yi kan cin zarafin mata, kuma an tattaro wasu bayanan ne tun daga abubuwan da suka faru daga shekarar 2000 zuwa 2018.
Rahoton kuma ya ce akwai yiwuwar tasirin annobar korona zai ƙara yawan wannan cin zarafin.
Rahoton kuma ya ce cin zarafin abokan zama ya fi yawaita, inda ya shafi sama da mata miliyan dari shida da arba'in a duniya.
Kashi ɗaya cikin huɗu na matan da ke tsakanin shekara 15 zuwa 24 sun riga sun fuskanci cin zarafin daga abokan zamansu, a cewar rahoton.
Matsalar ta fi ƙamari a yankin kudancin Asiya da kasashen kudu da Saharar Afirka da Oceania
Sojojin Najeriya sun kashe ƴan Boko Haram 33 a Borno

Asalin hoton, Reuters
Rahotanni daga Najeriya sun ce sojojin ƙasar sun yi artabu da mayaƙan Boko Haram a yankin ƙaramar hukumar Marte a jihar Borno arewa maso gabashin ƙasar.
Jaridar PRNigeria ta ce sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta’addan a ranar Talata yayin da suka ƙaddamar da farmaki domin kakkaɓe mayaƙan na Boko Haram a garuruwan Hausari da Missene da Chikungudu da ke cikin ƙaramar hukumar Marte.
Sai dai jaridar ta ruwaito cewa an kashe sojojin Najeriya biyu yayin da bakwai suka samu rauni.
Amma dakarun na Najeriya sun yi nasarar ƙwato bindiga ƙirar AK47 guda 27 da wasu manyan bindigogi masu harbo jirgin sama guda uku da motocin yaƙi biyu daga hannun mayaƙan
Ƙaruwar matasa marasa aikin yi a Najeriya babbar barazana ce ga tsaro - Sarkin Kano
Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya ce akwai babbar barazanar tsaro a Najeriya ganin yadda ake samun karuwar Matasa a kasar da ba su da aikin yi.
Sarkin na Kano Alhaji Aminu ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da BBC a yau Talata inda ya alakanta rashin sanar da matasa irin shirye-shiryen da gwamantin ta tanadar musu ya sa da yawa daga cikin su ke zaune babu aikin yi.
Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne yayin da yake cika shekara ɗaya akan gadon sarautarKano, bayan da gwamantin Kano ta sauke dan uwansa, Muhammad Sanusi II.
Sarkin ya kuma ce ya ce yana ƙoƙarin bin sahun iyayensa wajen hada kan gidan sarautar Kano da ake ganin ya rabu sakamakon tuɓe Sarki Sanusi na II.
Ku saurari hirar Sarkin da wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji.
Bayanan sautiƘaruwar matasa marasa aikin yi babbar barazana ce ga tsaro - Sarkin Kano Asabar za a fara duba watan Sha'aban - Fadar Sarkin Musulmin Najeriya
Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya Mal Alfarma Sa'ad Abubakar III ta buƙaci al'ummar Musulmi da su fara duba sabon watan Sha'aban na kalandar musulunci daga daren Asabar.
Kwamitin ganin wata na Najeriya a fadar Sarkin Musulmi ya ce ranar Asabar ce za ta zama 29 ga watan Rajab i daidai da 13 ga watan Maris na 2021.
Sanarwar da aka wallafa a shafin kwamitin ganin watan na Twitter ta buƙaci mutane da su kai rahoton ganin watan ga dagaci ko mai unguwa mafi kusa da su domin isar da saƙon ganin watan ga Sarkin Musulmi.
Sanarwar ta kuma ƙunshi lokatun faɗuwar rana da fitowatr alfijir a ranakun Asabar da Lahadi na dibon watan Sha'aban wanda daga shi sai watan azumi na Ramadan.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Shugaba Buhari ya ƙaddamar da gyaran titin jirgin kasan Fatakwal zuwa Maiduguri

Asalin hoton, TWITTER
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gyaran titin jirgin ƙasan Fatakwal zuwa Maiduguri zai farfaɗo da ayyukan gyara tattalin arziki a yanzkin arewa maso gababshin kasar da matsalar rashin tsaro ta lalata.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne ranar Talata a bikin ƙaddamar da ayyuka uku wato gyara titin jirgin ƙasan na fatakwal zuwa Maiduguri da tashar jirgin ruwa ta Bonny da Tashar Jiragen ƙasa ta masana'antu a Fatakwal.
Shugaban ya ce burin kasar shi ne a samar da hanyoyin sufuri sannan a inganta titunan jirgin kasa don tabbatar da ciyar da safarar kaya tsakanin kasashen Yammacin Afrika cikin sauki.
Haka kuma, shugaban ya ce waɗannan ayyukan za su samar da ayyuka masu yawa ga ƴan Najeriya.
Ya kuma ce ayyukan za su samar da kudaden shiga gagwamnatin tarayya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ja hankalin yan kasuwa da masu masan'antu su ci gajiyar aikin wajen faɗaɗawa da kafa sabbin masana'antu. Ya ce waɗannan ayyukan za su ɗaukaka martabar tattalin arzikin Najeriya a idon duniya.
An sace 'mata 50' a Katsina cikin kwana biyu
Rahotanni daga jihar Katsina a arewacin Najeriya na cewa 'yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mata kimanin 30 daga wani kauye a kudancin jihar da tsakar daren jiya.
Hakan ya zo ne bayan da wasu bayanan kuma suka ce maharan sun sace wasu matan fiye da 20 daga wasu kauyukkan biyu a shekaran jiya ranar Lahadi.
Sai dai jami'an tsaro a jihar ba su tabbatar da faruwar lamuran ba kawo yanzu.
Ku latsa lasifikar da ke kasa don sauraron rahoton Haruna Shehu Tangaza:
Bayanan sautiRahoton Haruna Shehu Tangaza kan sace mata a Katsina Gwamnan Ondo ya dakatar da ayyukan NURTW a jihar

Asalin hoton, TWITTER/AKEREDOLU
Gwamnatin jihar Ondo a Najeriya ta dakatar da ayyukan Kungiyar Direbobin Motocin Haya, NURTW bayan wata mummunar karawa tsakanin mambobinta da safiyar Talata.
babban mai taimakawa Gwamna Rotimi Akeredolu, Dakta Doyin Odebowale ya bayyana cewa an umarci duka mambobin kungiyar su fice daga tashoshin mota a fadin jihar.
Gwamnatin ta bayyana karawar a matsayin rashin ɗa'ar shugabanninta da ya janyo mummunan hari kan mabobinta da sauran mutanen gari da ba su ji ba, ba su gani ba.
Dakatarwar dai ta sai baba ta gani ce, a cewar Dakta Doyin.
Shugaban Senegal ya bukaci ƴan ƙasar su kwantar da hankalisu bayan munanan zanga-zanga
Shugaba Macky Sall na Senegal ya yi kira gaƴan kasar su kwantar da hankalinsu a karon farko tun bayan da rikici ya ɓarke a kasar a makon jiya bisa tsare wani ɗan majalisa na ɓangaren adawa Ousmane Sonko bisa zargin fyaɗe.
Haka kuma, shugaban ya yi alla-wadai da rikicin inda a kalla mutum biyar suka mutu sannan ya yi kira ga ƴan kasar su kwantar da hankulansu.
Ɗan Majalisa Sonko, wanda ya musanta zargin aikata fyaɗe, ya yi kira da a ci gaba da zanga0-zanga bayan sakinsa da aka yi ran 8 ga watan Maris.
"Za mu ci gaba da zanga-zangar lumana," a cewarsa.
Ya kuma yi kira da a gaggauta sako duka ƴan siyasar da ke tsare sannan a gudanar da bincike mai zurfi kan mummunar zanga-zangar.
Sonko ne ya zo na uku a zaɓukan 2019 kuma ya ce zargin fyaɗe da ake masa bita da ƙullin siyasa ne.
Labaran BBC cikin Minti Ɗaya
Bayanan sautiMinti Ɗaya da BBC na Rana 09-03-2021 Rundunar sojin Najeriya ba ta fahimci kalamaina ba ne- Sheikh Gumi

Asalin hoton, FACEBOOK
Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi ƙarin haske kan kalaman da ya yi bayan da rundunar sojin Najeriya ta gargaɗe shi kan abin da ta ce kalaman da ka iya tada husuma.
Sai dai Sheikh Gumi ya ce rundunar sojin ba ta fahimce shi ba ne.
Ya ce batun da ya yi na cewa akwai bara-gurbi a rundunar, yana nufin a shekarun 2010 zuwa 2015 ne.
"Da nake magana kan matsalolin da ke rundunar sojin Najeriya, ina nufin lokacin shekarun 2010 zuwa 2015 ne, lokacin da wasu mutane da ke rike da madafun iko a rundunar suka bari mugayen abubuwa su kai ta faruwa."
"A lokacin ne aka rika sa abubuwan fashewa har muka rasa wani babban Janar ɗin soja. Ni kaina na tsallake rijiya da baya da aka sa min abin fashewa," ya shaida wa BBC.
Sheikh Gumi ya bayyana wa BBC cewa yana da kyakkyawar fahimta da rundunar sojin Najeriya kuma babu abin da ya sauya.
Najeriya da Burtaniya sun sa hannu kan yarjejeniyar dawo da kuɗin da James Ibori ya sata

Najeriya da Burtaniya sun rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya don mayar wa da Najeriya fiye da fam miliyan huɗu da .
Ministan shari'ar kasar Abubakar Malami da kuma Babbar Jakadar Burtaniya Catriona Laing ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar.
Kuɗin wadanda tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori ya sata zuwa Birtaniya ne.

Mutanen da aka yi wa riga-kafin korona na iya fita ba takunkumi a Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar da ke kula da yaɗuwar cutuka a Amurka ta sanar da cewa mutanen da aka yi wa allurar riga-kafin cutar korona na iya fita ba tare da sa takunkumi ba.
Sabbin dokokin da hukumar ta fitar sun ce mutanen da aka yi wa cikakkiyar allurar na iya yin mu'amala da waɗanda aka yi wa allurar da wani rukuni na mutanen da ba a ayi wa allurar ba.
CDC ta ce mutanen da aka yi wa allurar na da cikakkiyar kariya daga cutar, makonni biyu bayan an yi masu allurar ta biyu.
Sai dai CDC ta ce akwai yiwuwar mutanen da aka yi wa riga-kafin na iya yaɗa cutar ga mutanen da ba a yi wa allurar ba.
Hukumar ta ce ya fi dacewa mutane su ci gaba da sa takunkumi da barin tazara musamman tsakaninsu da mutanen da ba su yi allurar ba da waɗanda ke da wasu cutuka da ka iya jefa su cikin haɗarin kamuwa da cutar.
Gwamnatin Neja za ta ba ƴan banga bindigogi don yaƙi da masu garkuwa da mutane

Asalin hoton, Twitter
Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya yi alƙawarin bai wa kungiyar yan sa kai bindigogi don yaki da yan bindiga da suka addabi jihar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya gana mayaƙan sa kan sama da 200 a unguwar Kasuwan Garba, inda ya tabbatar masu da cewa zai ba su bindiga don su iya tunkarar "maƙiyan" jihar.
Ya kai ziyara yankin ne don karfafa wa ƴan sa kan gwiwa.
Hare-haren ƴan bindiga da kashe-kashe da satar mutane don kuɗin fansa sun zama ruwan dare a jihar, inda a baya-bayan nan ma aka yi garkuwa da wasu ɗalibai a makarantar sakandire ta Kagara.
Wasu ƴan bindiga a jihohin Neja da maƙwabtanta a yankin arewa maso yammacin sun buƙaci mayakan sa-kai su ajiye makamai idan ana so su mika wuya su daina kai hare-hare.
Ana aikin nemo gawarwakin yaran da suka nutse a teku a Ghana

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da ayyukan ceto a gaɓar teku ta Apam da ke kudancin Ghana inda wasu ƙananan yara 12 suka nutse yayin da suke ninkaya a wani wuri da aka hana shiga.
Wata tawagar ƴan sandan kasar na aiki tuƙuru don gano gawarwakin yaran da yawansu ya kai 20.
Yaran da shekarunsu ke tsakanin 14 zuwa 17 sun shiga ɓangaren ruwan da aka hana shiga don yin ninƙaya don kar a gan su saboda an rufe wurin dalilin annobar cutar korona.
Zakuna sun kashe wani mai kula da su a Afrika ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Wani mutum da ke kula da namun daji a wani gandunsu a Afrika ta Kudu ya mutu bayan da wasu zakuna biyu suka kashe shi, kamar yadda hukumomi suka bayyana ranar Litinin.
Malibongwe Mfila mai shekaru 27 na aiki ne a matsayin mai sa ido kan dabbobin a gandun namun daji na Marakele, kuma yana aikin duba su ne a lokacin da zakunan suka kai mai hari ranar Asabar.
Ƴan sanda sun ce yana tuƙi ne a wata mota yana duba dabbobin kamar zakuna da giwaye.
Daga nan sai ya yanke shawarar ci gaba da duba dabbobin ta hanyar taka wa da ƙafa kuma a lokacin ne zakunan suka afka masa.
Ƴan sanda sun ce an kashe zakunan bayan da suka kai harin.
An yanke wa wani matashi hukuncin kisa bayan ya kashe mahaifinsa a Akwa Ibom

Asalin hoton, Getty Images
Wata babbar kotu a Akwa Ibom da ke zama a Ƙaramar Hukumar Ikot Ekpene ta yanke wa wani mutum mai shekara 31 mai suna Edidiong Ototi hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa am yanke wa Edidiong hukuncin ne bisa kisan mahaifinsa Mista Pius Ototi kan zargin yana maita.
A wani jawabi da ya yi wa ƴan sanda, Edidiong ya bayyana cewa ya kashe mahaifin nasa ne sannan ya binne shi a masai ran 18 ga watan Nuwamba shekarar 2018.
A lokacin da ya ke jawabin yanke hukuncin ranar Litinin, Justice Augustine Odokwo ya ce an kama Edidiong da laifin kisa wanda hukuncinsa shi ne kisa kamar yadda dokokin kasar suka tanada.
Justice Odokwo ya ba da umarnin a rataye Edidiong ta wuyansa har sai ya mutu.
Ƴan bindiga a Somaliya sun kashe mutum biyar kan leƙen asiri
Ƙungiyar Al-Shabab ta harbe mutum biyar da ta yi zargi da leƙen asiri da kisa a garin Bu'ale a kusa da yankin Jubba a kudancin Somalia.
Kafar yada labaran kungiyar, Radio Andalus, ta ruwaito cewa al-Shabab ta kashe mutanen ne a bainar jama'a a garin Bu'ale.
An kashe huɗu daga cikin mutanen ne ta hanyar harbi yayin da aka sare wa na biyar dinsu kai.
A farkon watan nan ne ƴan kungiyar al-Qaeda suka kashe mutum biyar da suka yi zargin suna yi wa Amurka leken asiri a garin Jilib.
Saliyo ta amsa rukunin farko na riga-kafin korona karƙashin shirin Covax

Asalin hoton, Getty Images
Rukunin farko na allurar riga-kafin cutar korona 96,000 sun isa Saliyo karkashin tsarin Covax.
Riga-kafin ta kamfanin Oxford-AstraZeneca na zuwa ne makonni bayan isar allura 200,000 daga China.
Wani bincike da aka gudanar ya nuna kashi 43 cikin 100 na mutanen da ke babban birnin Saliyo ne ke son yin allurar.
Ƙasar ta tabbatar da kamuwar mutum 3,920 da cutar da mutuwar wasu 79.
