Buhari ya raba wa jihohi biliyan ɗaya na tallafin korona

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Akwai yiwuwar Trump ya sake tsayawa takara

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi amfani da jawabin da ya yi karon farko tun bayan da ya sauka daga kan mulki wajen jaddada aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.

    Trump na fatan yin takarar shugaban ƙasar ce ƙarƙshin jam'iyyar Republican a 2024.

    Ya faɗa wa taron ƴan siyasa masu ra'ayin riƙau da aka yi a Florida cewa ba shi da wasu tsare-tsare na ƙaddamar da sabuwar jam'iyya kuma zai ci gaba da mara wa ƴan Republican baya kamar yadda suka mara masa baya.

    Mista Trump ya soki shugaba Joe Biden kan soke wasu manyan manufofi na hana baƙi daga ƙasashen da ke fama da ta'addanci shiga Amurka.

    Ya kuma sake nanata iƙirarin da ya sha yi a baya cewa shi ne ya lashe zaɓen watan Nuwamba da aka yi.

  2. Mutum 240 sun kamu da korona a Najeriya, biyu sun mutu

    Korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 240 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Lahadi.

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, cutar ta yi ajalin ƙarin mutum biyu.

    Jihar Anambra ce ke kan gaba a jerin jihohin da aka samu ɓullar cutar da mutum 85 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

    Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 82 a jihar Legas da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.

    Mutum 17 kuma sun kamu da korona a Osun, dake Kudu maso yammacin Najeriya, sai Ogun mai mutum 10, da jihar Kwara da aka gano mutane 9 da gwajin da aka yi musu ya tabbatar da cewa sun kamu da cutar.

    A Abuja, babban birnin Najeriya, an gano mutane 8 da suka kamu da cutar korona ranar Lahadi.

    NCDC ta ƙara da cewa an sallami mutum 512 daga cibiyoyi daban-daban da ke faɗin Najeriya - 170 a jihar Legas.

    Ya zuwa yanzu, alƙaluman masu cutar ta korona a ƙasar sun kai 155,657, an sallami 133,768 jumulla, sannan mutum 1,907 sun mutu tun bayan da cutar ta ɓulla a Najeriya.

    Ga yawan wadanda aka samu a wasu jihohi:

    • Kano-7
    • Abia-6
    • Borno-4
    • Edo-2
    • Bayelsa-2
    • Kaduna-2
    • Rivers-1
  3. Maraba

    Umar Mikail ke muku maraba da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na Litinin - Mande Tushen Aiki.

    Za mu fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar - ba za mu bar sauran sassan duniya ba.

    Mu je zuwa in kun shirya!