Buhari ya raba wa jihohi biliyan ɗaya na tallafin korona

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah ya kai mu

  2. An tura magudun adawar Nijar Hama Amadou gidan yari

    Hama Amadou

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa an kai jagoran adawan ƙasar Hama Amadou gidan yari, bayan ya miƙa kansa ga ‘yan sanda ranar Juma’a.

    Wata majiya da ke da kusanci da Hama Amadou ta tabbatar da tsare jagoran adawar na Nijar a gidan yari.

    Kamfanin dillacin labaru na AFP ya ce an ɗaure Hama Amadou bayan ya sha tambayoyi tsawon kwanaki uku kan zarginsa da hannu a zanga-zangar da ta ɓarke bayan bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

    Ko da yake, zuwa yanzu hukumomi ba su ce komai game da wannan al’amari ba.

  3. Ƴan bindiga sun kashe mutum 15 a Sokoto

    Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da harin da ƴan bindiga suka a ƙauyen Amarawa da ke cikin ƙaramar hukumar Illela ta jihar Sokoto

    An kashe mutum 12 a artabu bayan harin da ‘yan fashin daji suka kai ƙauyen

    Mutanen ƙauyen tun da farko, sun shaida wa BBC cewa mutum 15 suka yi wa jana’iza.

    Sun ce akwai ƙarin gawa biyu da ba su ɗauko ba zuwa tsakar rana, bayan jama’a sun yi yunƙurin ceto wani mutum da maharan suka sace daga gidansa a wayewar garin yau.

    Kakakin rundunar ƴan Sandan ASP Sanusi Abubakar ya tabbatar da faruwan lamarin amma ya ce suna gudanar da bincike.

  4. Masu fafutika a Nijar sun shigar da ƙara kan toshe intanet

    Wasu ƙungiyoyin masu fafutika sun kai gwamnatin Nijar ƙara kotu da kamfanonin wayoyin salula kan toshe intanet a biranen ƙasar saboda rikicin da ya biyo bayan zaɓen

    Jaridar ActuNiger ta ambato Ali Idrissa Nani, na ƙungiyar Rotab a Nijar na cewa sun yanke shawarar shigar da kara “saboda hana su ƴancinsu na neman bayanai da sadarwa da kuma aiki, matakin da ya hana bankuna aiki wanda kuma ya saɓa wa ƴancin dan adam.”

    A ranar 24 ga Fabrairu aka toshe hanyoyin sadarwa da Intanet a manyan biranen Nijar saboda tarzoma da ta ɓarke bayan sanar da sakamakon zaɓen da aka gudanar ranar 21 zagaye na biyu.

  5. Buhari ya raba biliyan ɗaya ga kowace jiha na tallafin korona

    Gwmnatin Najeriya ta ce ta raba wa jihohin ƙasar 36 haɗi da Abuja naira biliyan ɗaya kowacce na tallafin korona.

    Gwamnatin ta faɗi a shafinta na Twitter cewa shugaba Buhari ya amince da sakin kuɗaɗen a 2020.

    Kuma jihar Kano ta samu naira biliyan 5 yayin da Legas kuma ta samu naira biliyan 10.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Gwamnatin Jihar Benue ta mayar da shanu 210 ga masu su

    Getty Image

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Jihar Benue a Najeriya ta mayar da shanu 210 da ta kama a Makurdi a Karamar Hukumar Guma a jihar ga masu su.

    Kwamandan da ke lura da harkokin kiwo a jihar Linus Zaki ne ya bayyana hakan ga manema labarai, yana cewa an mayar da shanun ne bayan masu su sun biya tara wadda takai ta kimanin naira miliyan biyar.

    Zaki ya gargadi makiyayen game da karya dokar kiwo a ko ina a cikin jihar wanda ya ci karo da dokar da aka kafa a 2017.

    "Mun kama shanu 140 a Mbala a ranar 11 ga watan Fabrairun 2021, sai kuma guda 70 a Gbajimba a ranar 16 ga watan, duka su 210 an mayar da su ga masu su a yau."

    An saki shanun ne bayan biya wa ko wacce daya daga ciki naira 2,000 wanda hakan ya tashi kusan naira miliyan biyar.

    Da yake bayani a madadin makiyayan sakataren kungiyar Miyetti Allah Ibrahim Galma ya nemi a yi sassauci ga umarnin da aka bai wa makiyayen na su samarwa kansu wuraren kiyon dabbobinsu, yana mai cewa wannan matakin ya yi tsauri kuma cike yake da kimiyya.

  7. Ya kamata Buhari ya yi alfahari da abin da Salihu Tanko Yakasai ya fada - Sule Lamido

    SuleLamido/Twitter

    Asalin hoton, SuleLamido/Twitter

    Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya ce abubuwan da Salihu Tanlko Yakasai yake fada game da gwamnatin Buhari, daidai suke da abubuwan da wadanda ke kan mulki a yanzu suka rika fadi a kan gwamnatin da ta gabata.

    Sule Lamido ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a shafinsa na Fecabook, kan kora da kuma tsarewar da ake ci gaba da yi wa mataimaki na musamman kan harkokin yada labaran Ganduje.

    Cikin sanarwar ya ce, idan da akwai wasu masu laifi to mutanen APC sune manyan masu laifi.

    Yace kamata ya yi shugaba Buhari ya yi alfahari da abin da Tanko Yakasai ya yi na kwaikwayon irin gwagwarmayarsa.

    "Salihu ya rasa aikinsa saboda karfin zuciyarsa. Yadda aka raine shi ya taso ba zai iya zama kamar Garba Shehu ko Adesina ba, wadanda suke ganin ana yin rashin gaskiya amma suka yi shiru.

    "Idan har barazana da cin mutunci da zaman gidan yari da tsarewa suka gaza dakatar da Tanko Yakasai babba, to banga dalilin da za su iya dakatar da Salihu Yakasai ba," in ji Lamido.

  8. Masu zanga-zanga sun fusata 'yan sanda a Hong Kong

    ANTHONY KWAN/GETTY IMAGES

    Asalin hoton, ANTHONY KWAN/GETTY IMAGES

    Masu fafutikar kare hakkin demokradiya a Beijing sun bazama kan manyan tittuna inda suka shirya gagarumar zanga-zangar adawa da sabuwar dokar tsaron kasa irinta mafi girma a cikin watanni.

    Daruruwan mutane sun yi cuncurundo a wajen kotun da ke yi wa yan adawa 47 shari'a kan hadin-baki wajen yin zagon-ƙasa ga sabuwar dokar.

    Ƴansanda sun datse su tare da gargadin cewa za su iya fuskantar hukunci idan suka tsallake iyakar da ka yi musu.

    Ministan harkokin wajen Burtaniya ya yi Allah-wadai da tuhumar mutane, tare da shaida cewa an kirkiro dokar ce domin tauye yancin siyasa a yankin da kuma karya dokokin da aka cimma da Beijing lokacin da aka mayarwa China Yankin.

  9. 'Yan bindiga sun kashe mutum 15 a Jihar Sokoto

    Bayanan sautiLatsa nan don saurarar rahoton Zahradeen Lawal

    Wasu masu garkuwa da mutane a Najeriya sun kashe akalla mutum goma sha biyar sannan mutum takwas sun jikkata a garin Amarawa cikin karamar hukumar Illela a jihar Sokoto, bayan da mutanen garin suka yi yunkurin ceto wani attajiri da maharan suka sace daga gidansa yau da asuba.

    Jihar Sokoto dai tana da iyaka da jihar Zamfara inda aka sace ɗalibai mata 'yan sakandire fiye da ɗari uku a garin Jangebe.

  10. Tarayyar Turai za ta ƙaddamar da katin shaidar rigakafin korona

    Shugabar Hukumar Tarayya Turai, Ursula von der Layen, ta ce a wannan watan hukumar za ta gabatar da tsarin samar da katin shaida ga mutanen da aka yiwa allurar rigakafin korona.

    Ta ce shaidar da za a riƙa amfani da ita za ta tantance mutanen da ba a yi wa rigakafin ba da kuma bai wa mazauna Turai damar balaguro cikin tsaro a ciki da wajen kasashensu.

    Mambobi a Kungiyar da ke karbar baki sosai 'yan yawon bude ido, ciki har da Girka da Spaniya, sun nuna goyon-bayansu ga tsarin.

    Sai dai duk da haka akwai wadanda suka nuna damuwa kan nuna bangaranci.

  11. Tsohon Shugaban Faransa Sarkozy zai sha ɗaurin shekara uku saboda cin hanci

    Nicolas Sarkozy

    Asalin hoton, Getty Images

    An yanke wa tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy da abokan aikinsa biyu hukuncin shekara uku a gidan yari saboda laifin cin hanci da rashawa.

    Sarkozy mai shekara 66, an kama shi da laifin yunƙurin bai wa wani alƙali cin hanci mai suna Gilbert Azibert ta hanyar yi masa alƙawarin babban aiki a Monaco a madadin wasu bayanai da yake so ya ba shi game da binciken da ake yi wa jam'iyyar Sarkozy ɗin.

    Tsohon lauyan Sarkozy, Thierry Herzog, da kuma Azibert sun samu irin wannan hukuncin.

    Sai dai Sarkozy zai iya yin hukuncin a gidansa.

    Da yake bayar da hukuncin, alƙalin ya ce Sarkozy zai iya yin ɗaurin a gidansa amma sanye da na'ura. Sai dai ana sa ran zai ɗaukaka ƙara.

    Shi ne shugaba na biyu da aka taɓa yanke wa hukuncin rashawa a Faransa bayan hukuncin shekara biyu da aka yanke wa Jacques Chirac a 2011, wanda kuma ya mutu a 2019.

  12. An yi wa shugaban Ghana da mataimakinsa rigakafin korona

    Shugaban Ghana

    Asalin hoton, NANA AKUFO-ADDO

    Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da mataimakinsa Bawumia sun zama na farko da aka yi wa rigakafin cutar a ƙasar a yau Litinin.

    An yi wa shugabannin allurar ne kai-tsaye a kafar talabijin domin a ƙarfafa wa 'yan Ghana gwiwar cewa rigakafin ba ta da wata illa.

    Cikin jawabin da ya yi wa ƙasar a jiya Lahadi, shugaban ƙasa ya ce Ghana ce ƙasa ta farko da ta karɓi rigakafin AstraZeneca ta hannun shirin COVAX na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

    Ya zuwa yanzu ƙasar ta karɓi rigakafin guda 600,000 tun ranar 24 ga watan Fabarairu.

  13. Labarai cikin minti ɗaya

    Bayanan sautiDanna hoton sama ku saurari Minti Ɗaya da BBC na Rana 01/03/2021
    • Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin intanet na musamman domin yin rajistar samun allurar rigakafin cutar korona. Wannan na zuwa ne yayin da ya rage ƙasa da awa 24 kafin rigakafin ta isa Najeriya, wadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) za ta bai wa kasar ta cikin shirin COVAX.
    • Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da mataimakinsa Bawumia sun zama na farko da aka yi wa rigakafin cutar a ƙasar a yau Litinin. An yi wa shugabannin allurar ne kai-tsaye a kafar talabijin domin a ƙarfafa wa 'yan Ghana gwiwar cewa rigakafin ba ta da wata illa.
    • Rahotanni daga kudancin Najeriya na cewa an fara samun tashin farashin kayan abinci da na masarufi biyo bayan yajin aikin da dillalan kayan abincin suka fara. Kungiyar ‘yan kasuwar na neman diyya ne game da asarar kayan da aka haifa wa mambobinta a zanga-zangar EndSARS da kuma rasa rayuka a rikicin kabilanci tsakanin Hausawa da Yaraba a Jihar Oyo ta kudancin Najeriyar.
    • "Yar Najeriya da Amurka, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, ta shiga ofishinta a matsayin shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya wato World Trade Organisation (WTO) a yau.
  14. Gwamnatin Najeriya ta buɗe shafin rajistar rigakafin cutar korona

    Rigakafin korona

    Asalin hoton, Reuters

    Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin intanet na musamman domin yin rajistar samun allurar rigakafin cutar korona.

    Shafin yana ƙarƙashin kulawar hukumar lafiya a matakin farko wato National Primary Health Care Development Agency (NPHCDA), wadda ita ce za ta jagoranci yi wa 'yan Najeriya allurar rigakafin.

    Kuna iya latsa nan domin shiga shafin - BBC ba za ta ɗauki alhakin abubuwan da wasu shafuka suka ƙunsa ba.

    Wannan na zuwa ne yayin da ya rage ƙasa da awa 24 kafin rigakafin ta isa Najeriya, wadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) za ta ba ta ta cikin shirin COVAX.

    Ministan Lafiya Dr. Osagie Ehanire ya ce ma'aikatan lafiya da ke kan gaba a yaƙi da cutar za a fara yi wa allurar.

    A jiya Lahadi ne Sakataren Gwamnati kuma Shugaban Kwamitin Yaƙi da Korona, Boss Mustapha, ya bayyana cewa Najeriya za ta karɓi rigakafin korona kusan miliyan huɗu ranar Talata.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Archbishop na Canterbury ya yi wa ɗaliban Jangebe addu'ar kuɓuta

    Buhari da Justin Welby

    Asalin hoton, NG Presidency

    Shugaban ɗarikar Anglican na addinin Kirista, Archbishop of Canterbury Justin Welby, ya bayyana sace ɗaliban makarantar Jangebe ta Jihar Zamfara a matsayin "abin takaici".

    Cikin wani saƙon Twitter da ya wallafa a shafinsa, Archbishop ɗin ya ce gazawar harkokin tsaro "bala'i ne".

    "Yawan sace ɗalibai a Najeriya abin takaici ne," in ji shi. "Gazawar ɓangaren tsaro bala'i ne."

    Ya ƙara da yi wa ɗaliban addu'ar cewa: "Ina addu'ar dawowar yaran cikin ƙoshin lafiya da kuma malamansu - da fatan tsaro da adalci da zaman lafiya a Najeriya".

    A jiya Lahadi ne wasu kafafen yaɗa labarai a Najeriya suka yaɗa jita-jitar cewa 'yan bindigar da suka sace yaran a daren Juma'a sun sako su, sai dai gwamnatin Zamfara ta ƙaryata batun sakin nasu.

    Kwamishinan Ilimi na Zamfara Ibrahim Abdullahi Gusau ya yi wa BBC ƙarin bayani kan abin da ake ciki game da yunƙurin ceto ɗaliban zuwa yanzu.

    • Halin da ake ciki kan ceto ƴan matan sakandaren Jangebe
    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Ngozi Okonjo-Iweala ta fara aikin shugabancin WTO a yau

    Ngozi Okonjo-Iweala

    Asalin hoton, WTO

    "Yar Najeriya da Amurka, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, ta shiga ofishinta a matsayin shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya wato World Trade Organisation (WTO) a yau Litinin.

    Tsohuwar ministar kuɗi kuma ta harkokin waje a Najeriya, ita ce mace ta farko kuma baƙar fatar Afirka da ta taɓa riƙe shugabancin ƙungiyar.

    Okonjo-Iweala ta ce kawo ƙarshen matsalolin lafiya da kuma na tattalin arziki ne abin da ta saka a gaba biyo bayan ɓarkewar annobar korona a faɗin duniya.

    Ngozi Okonjo-Iweala

    Asalin hoton, WTO

    Ana nuna damuwa game da tsare-tsaren kasuwanci na ƙasar China da kuma irin ƙarfin ikon da WTO ke da shi na daƙile matsalar.

    Ana kallon matar a matsayin mai son kawo sauyi, sai dai muradun ƙasashe mambobin ƙungiyar za su kawo mata cikas.

  17. An yi wa Firaministan Indiya Modi rigakafin korona

    Narendra Modi

    Asalin hoton, @narendramodi

    Firaministan Indiya Narendra Modi ya wallafa wani hotonsa a shafin Twitter da ke nuna shi ana yi masa allurar rigakafin cutar korona.

    Ya buƙaci duk wanda ya cancanci a yi ma allurar da ya je a yi masa sannan ya yaba wa likitocin ƙasar da masana kimiyyar da ke ba da gudummawa a yaƙin da ake yi da annobar.

    An yi wa sama da mutum miliyan 12 rigakafin cutar a ƙasar kuma ana sa ran faɗaɗa shirin domin yi wa mutanen da suka haura shekara 60.

    Indiyan na cikin ƙasashen da ke samar da allurar rigakafin ta korona ga wasu ƙasashe.

  18. Yajin aikin 'yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya

    Kasuwar kayan gwari

    Asalin hoton, Getty Images

    Yajin aikin da dillalan kayan abinci suka fara na ƙungiyar Amalgamated Union of Foodstuff and Cattle Dealers of Nigeria (AUFCDN), ya janyo tashin farashin kayayyaki a yankin kudancin Najeriya, a cewar rahoton Daily Trust.

    Ƙungiyar ta AUFCDN wadda ɓangare ne na ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa wato NLC, ta fara yajin aikin ne a ranar Alhamis biyo bayan ƙarewar wa'adin da ta bai wa Gwamnatin Tarayya na kwana bakwai da ta biya mata buƙatunta.

    Ƙungiyar na neman a biya ta diyyar naira biliyan 475 sakamakon ɓarnar da aka yi wa mambobinta a lokacin zanga-zangar EndSARS da kuma kashe Hausawa 'yan kasuwa da aka yi a rikicin ƙabilancin da ya auku a kasuwar Shasa ta Jihar Oyo.

    Haka nan ta buƙaci a janye dukkan shingen duba ababen hawa daga kan manyan tituna, inda ake cin zarafin mambobinta ta hanyar kaɓar kuɗi daga hannunsu.

    Yajin aikin ya sa an tsayar da duk wata jigilar kayan abinci daga Arewa zuwa Kudu, waɗanda suka haɗa da dabbobin yanka da kuma kayan miya.

    Rahoton jaridar ya ce mahautan da ke da naman a jihohin kudu sun yi amfani da wannan damar sun tsauwala farashi, su ma masu kayan miya ba a bar su a baya ba, inda farashinsu ya tashi sosai.

    Akasarin kayan abinci da suka haɗa da nama da kayan gwari, 'yan kasuwa ne kan yi safararsu daga arewacin ƙasar zuwa kudanci.

  19. 'Yan fashi sun kashe mutum bakwai a Kaduna

    Bandit

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum bakwai a yankunan jihar ranar Lahadi sakamakon hare-haren 'yan fashi.

    Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi, inda ya ce 'yan bindigar sun kashe mutum biyu a ƙauyen Kajinjiri na Ƙaramar Hukumar Igabi sannan an raunata mutum ɗaya kuma yana kwance a asibiti.

    Kazalika, 'yan fashin sun kashe wasu mutum biyu a ƙauyen Rago, shi ma a Igabi.

    Haka nan, maharan sun far wa tashar Kutura da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru kuma suka kashe mutum uku.

    Kwamishinan ya ƙara da cewa Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya shafa.

  20. Aung San Suu Kyi ta gurfana a gaban kotu ta bidiyo

    Aung San Suu Kyi,

    Asalin hoton, EPA

    Hamɓararriyar shugabar Myanmar, Aung San Suu Kyi, ta bayyana a gaban kotu ta bidiyo, inda ta buƙaci ta ga lauyoyinta.

    Lauyoyin nata sun ce wannan ne karon farko da suka haɗu da wadda suke karewar tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi mata ranar 1 ga Fabarairu.

    Ƙasar ta hargitse da zanga-zanga tun daga lokacin, inda 'yan sanda suka kashe mutum 18 a ranar Lahadi.

    An yi kashe-kashen ne bayan 'yan sanda da sojoji sun yanke shawarar tarwatsa masu zanga-zangar da ƙarfin tsiya ta hanyar harba harsashi mai kisa da na roba.

    Har wa yau, masu zanga-zangar sun sake fantsama kan tituna a yau Litinin, suna masu buƙatar a dawo da mulkin dimokuraɗiyya da Suu Kyi ke jagoranta.

    Sojojin sun ce sun ƙwace mulki ne saboda an yi maguɗi a zaɓen da ya gabata, wanda jam'iyyar NLD ta Suu Kyi ta lashe. Sai dai ba su bayar da wata hujja ba.