An 'ƙirƙiri' wata dabba a ɗakin gwaji a Amurka

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. An sa dokar hana fita a Gombe kan rikicin sarauta

    Inuwa Yahaya

    Gwamnatin jihar Gombe a Najeriya ta sa dokar hana fita ta awa 24 a ƙaramar hukumar Billiri ta jihar saboda rikicin da ya ɓarke a garin na Billiri bisa naɗa sabon sarki.

    A lokacin da yake magana da manema labarai ran Juma'a Sakataren gwamnati Farfesa Njodi ya ce an sa dokar ne don tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

    Farfesa Njodi ya ce gwamnati a shirye take ta kare rayuka da dukiyoyi.

    "Gwamnati ta dakatar da gudanar da duk wasu taruka a Billiri kuma an bai wa duka hukumomin tsaro umarnin tabbatar da an bi dokar," a cewarsa.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu mata da ƙananan yara daga garin Billiri da kauyuka masu makwabtaka sun tare hanyar Gombe da Yola tsawon kwanaki uku, suna zanga-zangar abin da suka ce gwamna Inuwa Yahaya ya ki naɗa sabon sarki wanda suke kira Mai Tangale.

    Tare hanyar ya janyo cunkuson motoci da dama a hanyar ta Adamawa da Taraba da Benue da ma wasu jihohin ƙasar.

    Mutanen yankin na Billiri na zargin gwamnan da son sanar da wani Dakta Musa Idris Maiyamba, wanda ba shi ne zabin mutanen ba.

    Har yanzu gwamnati ba ta ce komai kan wannan zargi ba.

  2. An 'ƙirƙiri' wata dabba a ɗakin gwaji a Amurka

    Ferret

    Asalin hoton, USFWS

    Masana kimiyya a Amurka sun yi nasarar 'ƙirkirar' wata dabba da irinta ta kusa ƙarewa a duniya ta hanyar amfani da ƙwayoyin halittar wata dabba irinta da aka sa a ƙanƙara tun 1988.

    Wannan ne karo na farko da aka 'ƙirƙiri' wata dabba da ta kusa ɓacewa a doron ƙasa a Amurka.

    Masana kimiyya sun ce wannan ƙirƙirar za ta taimaka a ƙara yawan wannan dabbar a duniya.

    An haifi dabbar ne ran 10 ga watan Disamba kuma an raɗa mata suna Elizabeth Ann.

    An ƙirkiri Elizabeth Ann daga ƙwayoyin halittar wata dabba irinta mai suna Willa.

    Kafin gano Willa da wasu ƴan uwanta a 1981 a wata gona a garin Wyoming, an ɗauka irinsu sun ƙare gaba ɗaya a duniya har abada.

    Ba za a saki Elizabeth Ann a daji ba. Za a ajiye ta a wata cibiya a jihar Colorado inda a nan aka haife ta don masu bincike su ci gaba da sa ido a kanta.

  3. An tsare wani mai fafutukar kare haƙƙin bil Adama bisa wallafa labarin ƙarya kan Shugaba Idriss Deby

    Wata kotu a Chadi ta yanke wa wani mai fafutukar kare haƙƙin bil Adama hukuncin ɗauri shekara 3 ranar Alhamis bisa laifin rubuta wani labari da ke cewa shugaban ƙasar mai mulkin kama-karya yana nan a kwance rai a hannun Allah.

    Idriss Deby ya yi mulki Chadi tsawon shekara 30 kuma yana neman wa'adi na shidda a zaɓukan da za a yi a watan Afrilu.

    An kama Baradine Berdei Targuio, shugaban hukumar da ke kula da hakƙin bil Adama ta Chadi ran 24 ga watan Janairun 2020 bisa wani saƙo da ya wallafa a Facebook inda ya ce shugaba Deby na Faransa a halin rai kwakwai mutu kwakwai.

    Ƙungiyar Amnesty International ta ce wasu mutane masu ɗauke da bindiga sun rufe fuskokinsu ne suka kama Baradine Targuio.

    Targuio ya daɗe yana sukar Deby.

    A makon jiya ne gwamnatin Chadi ta haramta zarga-zangar nuna ƙin jinin gwamnati kafin zabukan da za a gudanar a watan Afrilu.

  4. An tsare mutumin da ya kashe wata mai juna biyu a Afrika ta Kudu

    Kisan Kai

    Asalin hoton, KEBA99

    An yanke wa wani mutumi hukuncin ɗauri shekara 20 kan kisan wata mata mai juna biyu wadda kisanta ya janyo zanga-zanga a Afrika ta Kudu har shugaban kasar ya yi jawabi.

    An gano gawar Tshegofatso Pule mai shekara 28 tana lilo a jikin wata bishiya a watan Yunin bara, da rauni a jikinta.

    Mzikayise Malephane mai shekara 31 ya amsa laifinsa a wata kotu a Johannesburg.

    Ya zargi saurayinta da biyan shi kuɗi ya kashe ta.

    Ƴan sanda sun ce sun kama shi.

    Malephane ya bayyana cewa tsohon saurayin matar ya ba shi Rand 7,000 don ya kashe ta amma ya ƙi. Sai dai ya kara masa kudin zuwa Rand 70,000 kafin ya amince da yin kisan.

    Tshegofatso Pule na da tsohon ciki wata takwas lokacin da ta ɓata ran 4 Yuni.

    An gano gawarta bayan kwana 4 a wata unguwa a Johannesburdg.

  5. Whatsapp na ci gaba da shirin kawo sauyi a manhajar kamar yadda ya tsara duk da ce-ce-ku-cen da ya janyo

    Whatsapp

    Asalin hoton, Getty Images

    Whatsapp na ci gaba da shirye-shiryen kawo sauyi a tsare-tsarensa da ya jawo ce-ce-ku-ce amma zai zai sauya yadda zai ria gaya wa masu amfani da shi bayan yi masa ca.

    Bayan sanarwar da ya yi ta farko a watan Janiaru, miliyoyin masu amfani da manhajar sun daina mafani da ita.

    A baya, manhajar mallakin Facebook ta ce mutane sun yi wa sauye-sauyen mummunar fahimta.

    Amma yanzu WhatsApp ta ce za ta amince ba ta fitar da bayanai game da sauyin yadda ya dace ba.

    Kalaman da aka yi amfani da su wajen sanar da sauyin sun sa fargaba a zukatan masu amfani da shafin inda suka yi tunanin Whatsapp zai rika yaɗa bayanan masu amfani da shi tare da Facebook.

    A zahiri ba haka batun ya ke ba.

    Kuma ya na ba masu amfani da manhajar shawarar karanta sauye-sauyen sosai kuma su fahimce shi.

    Za a fara amfani da sabbin sauye-sauyen ne ran 15 ga watan Mayu.

  6. Bidiyon jana'izar Dokta Junaidu Muhammad a Kano

    Bayanan bidiyo, Jana'izar Dokta Junaidu Muhammad a Kano
  7. MDD ta buƙaci UAE ta ba da shaidar cewa Gimbiya Latifah ƴar Sarkin Dubai na nan a raye

    Gimbiya Latifah

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dinkin Duniya MDD, ta bukaci ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa wato UAE su bayar da shaidar cewa Gimbiya Latifah, yar sarkin Dubai na nan a raye.

    Wani hoton bidiyo da aka naɗi gimbiyar a boye, wanda BBC ta samu ta shaida cewa ana rike da ita a kulle a masarautar sannan tana fargabar hallakata.

    Mai magana a madadin hukumar kare hakkin bil adama ta MDD ta ce bidiyo abin ɗaga hankali ne.

    A shekara ta 2018 aka cafke Gimbiya Latifa lokacin da ta yi kokarin tserewa daga Dubai.

    Har yanzu dai UAE ba ta ce komai ba.

  8. Yarima Harry da matarsa sun kammala ajiye aiki a hukumance da gidan sarautar Burtaniya

    Harry da Meghan

    Asalin hoton, PA Media

    Jikan sarauniyar Elizabeth ta Ingila, Yarima Harry da matarsa Meghan sun kammala ajiye aiki a hukumance da gidan sarautar Burtaniya.

    Wannan sanarwar ta kawo karshen mukamin da Harry da Meghan ke rike da shi a masarauta.

    Matakin dai bai yi wa masarautar Buckingham daɗi ba, sannan masarautar ta ce Yariman da matarsa za su rasa mukamin masarautar Burtaniya na Duke da Duchess din Sussex, sai dai za su cigaba da kasancewa yan gida da nuna musu matukar auna.

    A tasu sanarwar, ma'auratan sun ce za su ci gaba da gudanar da tafiyar da rayuwarsu mai ƴanci.

  9. Harbe-harbe ya ɓarke a Mogadishu na Somalia

    Motar sojoji

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙazamin faɗa ya ɓarke a babban birnin Somalia, Mogadishu yayin da shugabannin 'yan adawa suka yi fatali da dokar hana yin zanga-zanga game da zaɓen da aka dakatar.

    Wa'adin shugaban ƙasar ya ƙare a makon da ya gabata kuma ƙin zaɓar sabon shugaba ya jefa Somalia cikin rikici.

    Gwamnati ta ce wasu 'yan bindiga sun kai wa sojoji hari a sansanoninsu da ke kusa da fadar shugaban kasa.

    An rufe akasarin titunan birnin sannan an girke dakaru na musamman.

    Ana sa ran Shugaban Ƙasa Mohamed Abdullahi Mohamed zai gana da shugabannin yankunan ƙasar guda biyar a yaunƙurin kawo ƙarshen matsalar.

    Sai dai an yi ta jinkirta shi a makon nan, inda shugaba ɗaya ne kaɗai ya isa birnin, a cewar wakiliyar BBC Bella Sheegow.

  10. Ba a saki ɗaliban makarantar Kagara ba - Gwamnan Neja

    Sani Bello

    Asalin hoton, NSG

    Gwamnan Jihar Neja ya musanta rahotannin da ke cewa an saki ɗaliban makarantar Kagara da 'yan bindiga suka sace ranar Talata.

    Cikin wani jawabi da aka yaɗa kai-tsaye, Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce babu gaskiya a rahotannin da suka fara yawo a shafukan zumunta da safiyar Juma'a cewa an saki mutanen.

    Ya yi taron manema labaran ne bayan ya gana da Sheikh Ahmad Gumi, wanda yake ƙoƙarin haɗa kai da shugabannin 'yan fashin daji domin a saki waɗanda aka kama ɗin.

    Jumillar ɗalibai 27 aka sace da malamai tara da ma'aikata uku da kuma iyalan malaman guda tara yayin harin na daren Talata.

  11. Ana bikin buɗe kasuwar Tahoua a Nijar

    Tahoua
    Bayanan hoto, Yau Alhamis ne ake ƙaddamar da sabuwar babbar kasuwar birnin Tahoua da ke jamhuriyyar Nijar
    Tahoua
    Bayanan hoto, Kasuwar ta ƙunshi shaguna 1,157, inda aka gina su sama da ƙasa
    Kasuwar Tahoua
    Bayanan hoto, Kasuwa ce irin ta zamani da aka ɗauki tsawon watan 11 ana aikin gina ta
  12. Labarai cikin minti ɗaya

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari Minti Ɗaya da BBC na Rana 19/02/2021
    • Fitaccen malamin Musulunci a Najeriya Sheikh Ahmad Gumi ya ce ya gana da wasu 'yan bindiga a dazukan Jihar Neja, inda suka yi alƙawarin taimakawa wurin ceto ɗaliban makarantar Kagara da aka sace. Malamin ya ce 'yan bindigar da ya gana da su sun faɗa masa cewa za su nemi waɗanda suka sace yaran domin tattaunawa da su.
    • Hukumar yaƙi da yaɗuwar cutuka a Najeriya ta NCDC ta saka Najeriya a "mataki na tsakatsaki" na yiwuwar ɓullar annobar cutar Ebola bayan ɓullar cutar a ƙasar Guinea. NCDC ta ce an ɗauki matakin ne saboda kusancin Guinea da Najeriya da kuma sauran ƙasashen Afirka ta Yamma.
    • An kashe mutum na farko a zanga-zangar Allah-wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar Myanmar, inda aka harbi wata matashiya a ka. Tun a makon da ya gabata ne aka jikkata Mya Thwe Thwe Khaing mai shekara 20 a lokacin da 'yan sanda suka yi yunƙurin tarwatsa masu zanga-zangar da ruwa da harsashin roba da kuma mai kisa.
    • An dakatar da jirage daga sauka a filin jirgin sama na birnin Mogadishu na Somalia biyo bayan harbe-harben da aka yi a kusa da filin jirgin. Wani wakilin BBC a Mogadishu y ace majiyoyi a filin jirgin sun tabbatar da cewa an soke jirgin kamfanin Ethiopian Airlines da ya kamata ya sauka a safiyar yau Juma’a.
  13. Sheikh Gumi ya tattauna da 'yan bindiga kan ɗaliban Kagara da aka sace

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari cikakkiyar hira da Sheikh Ahmad Gumi

    Fitaccen malamin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya ce ya gana da wasu 'yan bindiga a dazukan Jihar Neja, inda suka yi alƙawarin taimakawa wurin ceto ɗaliban makarantar Kagara da aka sace.

    Cikin wata hira da BBC, shehin malamin ya ce 'yan bindigar da ya gana da su sun faɗa masa cewa za su nemi waɗanda suka sace yaran domin tattaunawa da su.

    "Sun ce ba su san waɗanda suka ɗauki yaran ba saboda suna cikin daji (lokacin da abin ya farau) amma za su neme su tun da dai ana maganar sulhu ne," in ji shi.

    "Sun ce san waɗanda suka sace matafiyan nan a motar safa ta gwamnatin Neja kuma sun yi hakan ne saboda motar gwamnati ce domin gwamnatin ce ke kai musu hare-hare.

    Malamin ya ce sun faɗa masa cewa buƙatunsu su ne kawai a daina kai musu hare-hare a daji da kuma cikin gari, "idan aka yi haka za su saki duk mutanen da ke hannunsu".

  14. Ya kamata a tattauna da 'yan fashin daji - Gwamnan Neja

    Gwamnan Neja Sani Bello

    Asalin hoton, Niger State Government

    Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello ya sauya ra'ayi kan tattaunawa da 'yan fashin daji sannan ya goyi bayan saka dokar ta-ɓaci a kan matsalar tsaro a Najeriya.

    Gwamnan wanda ya yi wa 'yan jarida jawabi jim kaɗan bayan ganawarsa da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a jiya Alhamis, ya ce ya yi wa Buhari bayani kan halin da ake ciki tare da alwashin ci gaba da aikin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatocinsu.

    "Na fuskanci wasu daga cikin 'yan fashin nan na buƙatar a tattauna da su, a ba su kulawa saboda sun gaji," a cewar gwamnan.

    "Idan gwamnati ta yarda kuma ta karɓi buƙatunsu, ina ganin a shirye suke su sauya rayuwarsu." Sai dai gwamnan bai bayyana ƙarara cewa a yi musu afuwa ba.

    Bugu da ƙari, gwamnan ya ce yana goyon bayan kiran da Majalisar Dattawan ƙasar ta yi ga Shugaba Buhari na saka dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro.

    "In ka kula akwai matsalar tsaro a kowane ɓangare na ƙasar nan. Saboda haka, e ina goyon bayan a ƙaddamar da wani tsari na dokar ta-ɓaci a kan matsalar tsaro," in ji shi.

    Wanann matsayi nasa ya sha bamban da wanda aka san gwamnatinsa a kai kafin yanzu, inda shi da kuma gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, suka haƙiƙance cewa ba za su yi wata tattaunawa da 'yan fashin ba.

    Kazalika, gwamnan ya bayyana ranar Laraba cewa gwamnatinsa ba za ta biya kuɗin fansa ba game da yunƙurin ceto ɗaliban makarantar Kagara da malamansu guda 42 da 'yan fashin suka sace a daren Talata.

  15. Barazanar da 'yan fashin daji ke yi wa ilimi a arewacin Najeriya

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bayanan da Fauziyya Tukur ta tattaro

    A wannan makon, babban labarin da ya fi jan hankali shi ne batun sace ɗalibai 'yan makarantar sakandare ta Kagara a jihar Neja.

    Masana na ganin matsalar tsaron da yankin arewacin Najeriya ke fuskantar za ta jawo babban giɓi a fannin ilimi.

    Fauziyya Kabir Tukur ta yi mana duba kan wannan batun a cikin wannan bidiyon.

  16. Majalisar Jihar Jigawa ta amince da ɗaurin rai-da-rai kan masu fyaɗe

    Gidan yari

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dokokin Jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya ta amimnce da hukuncin kisa da kuma ɗaurin rai-da-rai ga waɗanda aka kama da aikata fyaɗe.

    Dokar ta tanadi ɗaurin rai-da-rai ga wanda ya aikata laifin fyaɗe da kuma hukuncin kisa idan mutum ya saka wa wanda ya yi wa fyaɗen cutar HIV/AIDS.

    Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa majalisar ta cimma matakin ne bayan amincewa da rahoton kwamitin shari'a ƙarƙashin jagorancin Abubakar Jallo, wanda ya ƙunshi mambobi guda bakwai a ranar Laraba.

    Bayan amincewa da rahoton ne kuma Kakakin Majalisar Idris Garba ya sanar da amincewa da ƙudirin dokar.

    Ɗaukacin 'yan majalisar 30 ne da ke wakiltar ƙananann hukumomi 27 na jihar suka amimnce da dokar.

    Nan gaba za a miƙa wa Gwamna Badaru Abubakar domin sanya mata hannu kafin ta zama doka a jihar.

    Dokar ta ƙunshi tanade-tanade guda 18 ciki har da hukuncin kisa ga mutumin da ya saka wa wanda ya yi wa fyaɗe cutar ƙanjamau wato HIV da kuma ɗaurin rai-da-rai ga wanda ya aikata fyaɗe.

  17. Mahangar malaman Musulunci kan ƙaruwar masu kashe kansu a Najeriya

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton Khalifa Shehu Dokaji daga Kano

    Mallamai a Najeriya sun fara bayyana ra’ayoyin su kan yadda ake samun ƙaruwar mutanen da ke kashe kansu a wasu daga cikin jahohin ƙasar.

    Mallaman na da ra’ayin cewar akwai bukatar mahukunta da kafafen yaɗa labarai da su malamai su tashi haiƙan wajen ilimantar da al’umma illolin da ke tattare da mutum ya kashe kansa.

    A yayin wata tattaunawa da wakilin mu a Kano, shuaban majalisar malamai na Najeriya Mallam Ibrahim Khalil ya ce duk da haramcin mutum ya kashe kansa a Musulunci, akwai babban laifi daga ɓanagren gwamanti.

  18. Za a ci gaba da aikin shata iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru

    Najeriya da Kamaru

    Za a ci gaba da ayyukan shata iyakoki tsakanin Kamaru da Najeriya nan da 'yan watanni masu zuwa bayan an dakatar da aikin na tsawon lokaci.

    An samu bayanan hakan ne bayan ganawar da Babban jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a yammaci da tsakiyar Afrika, Mohamed Ibn Chambas, wadda ya yi da Firaministan Kamaru Joseph Dion Ngute.

    Ayyukan shata iyakokin na ɗaya daga cikin abubuwan da gwamnatin ƙasashen biyu suka cimma za su yi aiki a kai ƙarƙashin yarjejeniyar “Green Tree”.

    Tun a shekarar 2002 ne kotun kasa da kasa ta warware tankiyar da take tsakanin Kamaru da Najeriya game da tsibirin Bakassi.

  19. Akwai yiwuwar ɓullar cutar Ebola a Najeriya – NCDC

    Ebola

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar yaƙi da yaɗuwar cutuka a Najeriya ta NCDC ta saka Najeriya a "mataki na tsakatsaki" na yiwuwar ɓullar annobar cutar Ebola bayan ɓullar cutar a ƙasar Guinea.

    NCDC ta bayyana haka ne a shafinta na intanet, tana mai cewa an ɗuki matakin ne saboda kusancin Guinea da Najeriya da kuma sauran ƙasashen Afirka ta Yamma.

    "Ganin irin kusancin Najeriya da Guinea da kuma sauran ƙasashen Afirka ta Yamma, an saka Najeriya a mataki na tsakatsaki na ɓullar annobar cutar Ebola," a cewar NCDC.

    Ebola ta ɓulla a Guinea ranar 14 ga watan Fabarairu, inda aka samu mutuwar mutane a yankin N’zerekore.

    Mutum bakwai ne suka kamu bayan sun halarci jana'izar wata ma'aikaciyar jinya ranar 1 ga Fabarairu, a cewar NCDC.

  20. Abin da ake nufi da ficewar Najeriya daga masassarar tattalin arziki

    Shinkafa

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu ƙwararru sun ce fitar Nijeriya daga masassarar tattalin arziƙi a ƙarshen shekarar da ta wuce wani haske ne cewa ƙasar na kan hanyar samun bunƙasar arziƙi mai ɗorewa.

    Sun ce hakan ya faru ne sakamakon ƙoƙarin gwamnati na haɓaka fannonin da ba na man fetur ba.

    A jiya Alhamis ne wani rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasar NBS ya ce Nijeriya ta samu bunƙasar kashi 0.11 cikin 100 a tsakanin watan Oktoba zuwa na Disamban 2020.

    Wannan na nuna cewa ƙasar ta fita daga karayar tattalin arziƙin da ta afka cikin Yuli zuwa Satumba.

    Bayanan sautiKu saurari rahoton Mukhtari Adamu Bawa idan kuka latsa hoton sama