Ƴan bindiga sun kashe mutum 7 a jihar Edo

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Fauziyya Tukur

  1. Labarai da dumi-dumi, 'Yan wasan Wikki Tourists ta Bauchi sun yi hatsari

    Motar 'yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Wikki Tourists ta garin Bauchi ta kama da wuta a yau Alhamis yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Akwa Ibom.

    Ƙungiyar mai buga Firimiyar Najeriya na kan zuwa filin wasa na Godswill Akpabio International da ke garin Uyo domin karawa da ƙungiyar Dakkada a wasan mako na 11 ranar Lahadi.

    Wani bidiyo da ɗan wasan Wikki, Damala Ezekeil, ya wallafa a shafinsa na Twitter ya nuna yadda motar ke ci da wuta a gefen titi.

    "Lamarin ya faru ne a safiyar nan a garin Hawan Kibo a kan hanyarmu ta zuwa Akwa Ibom...tayarmu biyu ta fashe kafin motar ta kama da wuta," a cewarsa.

    Sai dai sun auna arziki domin kuwa babu wanda jikkata balle rasa rai.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. Labarai da dumi-dumi, NAFDAC ta amince da amfani da rigakafin korona na Oxford/AstraZeneca a Najeriya

    Korona

    Asalin hoton, UNIVERSITY OF OXFORD

    Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC) ta amince da fara amfani da rigakafin cutar korona ta kamafanin Oxford/AstraZeneca a ƙasar.

    Shugabar NAFDAC, Dr. Mojisola Adeyeye, ita ce ta bayyana hakan a yau Alhamis cikin wani jawabi da ta gabatar kai-tsaye ta talabijin.

    Ta ƙara da cewa za a iya ajiye allurar a cikin yanayin sanyi daga 2 zuwa 8 na ma'aunin Celsius.

    A cewarta, akwai rigakafi guda uku da ake kan tantancewa amma sakamkaon gwajin da aka yi a kan Oxford/AstraZeneca ya nuna cewa allurar na da tasiri sosai kan nau'in cutar wanda ya ɓulla a Birtaniya kuma ya shiga Najeriya.

    Sai dai ta ce nau'in cutar da aka samu a Afirka ta Kudu bai ɓulla Najeriya ba zuwa yanzu.

  3. Gwamnati ta fara tattaunawa da 'yan fashin da suka sace ɗalibai a Jihar Neja

    Gwamna Sani Bello

    Asalin hoton, @abusbello

    Bayanan hoto, Gwamna Sani Bello na Jihar Neja ya ce gwamnatinsa ba za ta biya kuɗin fansa ba

    Gwamnatin Jihar Neja da ta Tarayyar Najeriya sun fara tattaunawa da 'yan bindigar da suka sace ɗliban makarantar Kagara, a cewar rahoton Daily Trust.

    Jaridar ta ruwaito wata majiya da ke cikin tawagar na cewa gwamnatocin na tattaunawar ce ta hannun masu shiga tsakani bayan sace ɗaliban a daren Talata.

    Wasu shugabannin Fulani da kuma tubabbun 'yan fashi ne ke jagorantar ƙoƙarin ceto yaran, a cewar jaridar.

    Ta ƙara da cewa an nemi wasu manyan tubabbun 'yan fashin daji daga Zamfara da Katsina domin jagorantar tattaunawar.

    Gwamnatin Jihar Neja ta ce mutum 42 ne aka sace ciki har da ɗalibai 27 da ma'aikata uku da iyalansu guda 12. Makarantar na da ɗlibai kusan 1,000.

    'Yan bindigar sun kashe ɗalibi ɗaya yayin da yake ƙoƙarin guduwa, inda suka harbe shi sau uku.

    Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya ce gwamnatinsa ba za ta biya kuɗin fansa ba.

  4. Wani fasto a Najeriya na addu'ar kar cutar korona ta ƙare

    Apostle Johnson Suleman

    Asalin hoton, @APOSTLESULEMAN

    Wani malamin addinin Kirista a Najeriya mai suna Apostle Johnson Suleman ya ce ya yi addu'ar "kar cutar korona ta ƙare" saboda ya fi hutawa a loakcin annobar.

    Cikin wani bidiyo da yake ta waɗari a shafukan zumunta, fasto ɗin mai shekara 49 ya ce a cikin annobar ya sayi jirgin sama na uku domin amfanin kansa kawai.

    "Na yi ta addu'ar kar cutar korona ta zo ƙarshe saboda ina hutawata," in ji shi. "Matata ma sai da ta ce 'a'ah, da ma haka rayuwa take da daɗi."

    Faston wanda shi ne shugaban cocin Omega Fire Ministries International wadda ke da hedikwata a Jihar Edo da ke kudancin Najeriya, ya ce yana jin daɗin jita-jitar da ake yaɗawa a kansa cewa yana da injin buga kuɗi.

    Sai dai faston bai ji da daɗi ba a hannun 'yan Najeriya, domin kuwa wani mai suna @dunnia33 cewa ya yi "bai kamata a mayar da hankali ba a kan kuɗi kawai, ko kuwa Allah ba ya son waɗnda suka mutu ne?"

    Wannan maganganu nasa suka sa wasu ke yin kalaman ɓatanci ga addinin Kiristanci baki ɗaya - kalaman da ba za mu iya wallafa su ba a nan.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Ana zargin gwamnatin Sri Lanka da ƙin yi wa waɗanda yaƙi ya ɗaiɗaita adalci

    Kungiyar kare hakki ta Amnesty International ta zargi mahukunta a Sri Lanka da kawo cikas ga kokarin cimma adalci ga wadanda aka cutar yayin yakin basasar kasar da aka kwashe shekara 30 ana yi.

    A wani sabon rahoto da ta fitar, kungiyar ta ce gwamnati na fakon kungiyoyin kare hakkin dan Adam da ‘yan jarida da kuma masu adawa da su a siyasance.

    Rahoton ya ce ana barazana ga jami'an kungiyoyin da ke aiki da iyalan wadanda suka bace yayin rikicin.

    Gwamnatin kasar ta musanta wannan batu, inda ta zargi kasashen waje da yin makarkashiya don dagula lamura a kasar.

  6. Korona a Najeriya: Mutum takwas sun mutu, 869 sun kamu

    Korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 869 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Laraba.

    Kazalika, an samu ƙarin mutum takwas da suka rasu sakamakon cutar.

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, jihar Legas da ta fi yawan masu fama da cutar a Najeriya ce ke kan gaba da mutum 229 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

    Jihar Rivers da ke yankin kudu maso gabas, na da kimanin mutane 79 da gwajin da aka yi musu ya tabbatar da cewa sun kamu da cutar korona a wannan rana ta Laraba kaɗai.

    Kazalika an samu mutum 73 a jihar Taraba da ke tsakiyar Najeriya, da kuma mutum 66 a jihar Oyo da ke kudu maso gabas, baya ga ƙarin wasu mutane 60 da aka gano sun kamu da cutar a jihar Ogun.

    A babban birnin ƙasar Abuja, mutum 58 ne gwaji ya nuna cewa sun kamu da korona a ranar Laraba.

    Jihohi da adadin waɗanda suka kamu:

    • Plateau-56
    • Kwara-38
    • Ondo-38
    • Osun-24
    • Kano-22
    • Nasarawa-21
    • Abia-19
    • Edo-19
    • Akwa Ibom-19
    • Cross River-10
    • Delta-9
    • Benue-8
    • Ekiti-6
    • Borno-6
    • Katsina-4
    • Bauchi-3
    • Bayelsa-1
    • Zamfara-1
  7. Iran za ta fara tattaunawa da ƙasashen Yamma kan nukiliya a yau

    Iran

    Asalin hoton, EPA

    Nan gaba a yau ne jami’an difilomasiyya daga Amurka da Birtaniyya da Faransa da Jamus za su yi wata tattaunawa don duba hanyoyin farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka cimma a 2015.

    Iran ta ce za ta kara daukar matakan karya yarjejeniyar idan ba a dage takunkumin da aka sanya mata ba a mako mai zuwa.

    A ranar Laraba ta fada wa hukumar da ke sa ido kan nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya cewa ta shirya tsaf don kara inganta sinadarin Uranium - wanda ake haɗa makamin nukiliya da shi.

    Wakilin BBC ya ce shugaba Binden ya bayyana aniyarsa ta sake shiga yarjejeniyar, amma da alama ya makara, domin tuni gwamnatin Iran ta fara karya yarjejeniyaryar.

    Daga cikin ayyukan karya dokar da Iran ta yi ciki har da samarwa da kuma inganta sinadarin Uranium da aka haramta amfani da shi.

  8. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na safiyar Alhamis.

    Ku biyo ni Umar Mikail domin sanin halin da duniya ke ciki a wannan rana - musamman Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.