An nuna wani bidiyo mai 'cike da hujjoji' a zaman sauraren tsige Trump

Asalin hoton, EPA
An nuna wa sanatoci a zaman sauraren ƙarar tsige Donald Trump wani bidiyo mai 'cike da hujjoji' na ranar da waɗanda ake tunanin magiya bayansa ne suka afakawa majalisar dokokin Amurkar.
Hoton bidiyon ya nuna ƴan sanda suna karawa da masu zanga-zangar kuma suna roƙon a kawo masu ɗauki.
Ƴan sanda sun kange ƴan majalisar, a wanu lokaci ma babu tazara sosai tsakaninsu da masu zanga-zangar daf da za su auka zauren majalisar.
Lauyoyin ƙasar sun ce Mista Trump ne ya ingiza magoya bayan nasa ta hanyar wallafa wani saƙo a shafinsa na Twitter.
Ana buƙatar kashi biyu cikin uku na ƴan majalisar su amince da tsige Trump, amma haka zai yi wuya saboda mafi yawan ƴan Republican na nan tare da tsoho shugaban.
Amma idan aka tsige shi, ba zai iya sake tsayawa takarar shugaba a ƙasar ba har abada.




