Mu kwana lafiya
Nan muka zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.
Muna fatan sake haɗuwa da ku gobe domin kawo wasu rahotannin.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran ƙasashen duniya.
Fauziyya Tukur and Umar Mikail
Nan muka zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.
Muna fatan sake haɗuwa da ku gobe domin kawo wasu rahotannin.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.
Ɗaliban kwalejin United Comprehensive High School da ke Jihar Ogun sun tare babbar hanyar Legas zuwa Abeokuta a safiyar Alhamis yayin da suke zanga-zangar mutuwar wani abokin karatunsu.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa ɗaliban sun yi wa titin tsinke ne bayan da suka samu labarin cewa abin hawa ya bige ɗalibin lokacin da yake tsallaka titin.
Zanga-zangar ta haddasa cunkoson ababen hawa tun daga cikin Legas har zuwa garin Abeokuta na Jihar Ogun, inda masu ababen hawa suka shafe awanni a wurin.
Kwamandan hukumar kiyaye haɗura a yankin, Ahmed Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin ga NAN.
Ya ce: "Ana zanga-zangar ne kan wani hatsari da ya faru a ƙauyen Wasimi da ke kusa da garin Itori a kan hanyar Legas zuwa Abeokuta da misalin ƙarfe 9:35 na safe."
Ya ƙara da cewa sakamakon haka ne wasu fusatattun ɗlibai suka cinna wa motar wuta sannan aka jikkata 'yan sanda biyu bayan sun yi ƙoƙarin daƙile faruwar lamarin.

China ta haramta wa babbar tashar Ingilishi ta talabijin ta BBC watsa labarai cikin ƙasar, sakamakon abin da Chinar ta kira rashin adalci da kuma rashin faɗin gaskiya a aikin jarida.
Wannan na zuwa ne mako ɗaya bayan Birtaniya ta dakatar da tashar talabijin ta Chinar daga watsa labarai a cikin Birtaniyar.
China ta caccaki BBC kan wani rahotonta na ɓarkewar cutar korona da kuma wani rahoton BBC kan xin zarafin da ƙasar ke yi wa Muslmai ƴan ƙabilar Uighur.
Wannan dakatarwa ba za ta yi wani tasiri ba sosai sakamakon tashar talabijin ɗin da harshen Ingilishi take watsa labarai.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Joe Biden ya soke dokar gaggawa da tsohon Shugaba Donald Trump ya yi amfani da ita wurin tattara kudin gina katanga tsakanin kasar da makwabciyarta Mexico.
Cikin wata wasika zuwa ga Majalisar Wakilai a yau Alhamis, Mista Biden ya ce babu wata hujjar yin hakan kuma ba za a sake kashe ko kwandala ba wurin ginin katangar.
Mista Trump ya saka dokar ta-ɓaci a kan iyakar ƙasar ta kudu a 2019, abin da ya ba shi damar kauce wa neman amincewar majalisa tare da yin amfani da kasafin kuɗin rundunar sojan ƙasar wurin gina katangar.
Ya zuwa lokacin da Trump ya bar ofis, an kashe kusan dala biliyan 25 a kan aikin.
Matakin na Biden na cikin na baya-bayan nan da yake ɗauka a kan umarnin shugaban ƙasa da Trump ya riƙa bayarwa a lokacin mulkinsa.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta kare matsayar da ta cimma da shugaban yankunan ƙasar na tsawaita dokar korona har zuwa 17 ga watan Maris.
Da ba a tsawaita wannan doka ba, da wannan Lahadin mai zuwa dokar kullen za ta zo ƙarshe.
Ta shaida wa ƴan majalisar ƙasar cewa sabon nau'in korona da aka samu zai iya jawo ɓarkewar cutar karo na uku
Ms Merkel kenan ke cewa an samu sabon nau'in a Jamus, kuma wanda ya fi saurin bazuwa shi ne na Birtaniya, ƙwararru sun tabbatar mana da cewa nan da wani lokaci saon nau'in zai iya mamaye ko ina har ya wuce asalin koronar da ta fara ɓulla.

Asalin hoton, AFP
Rundunar sojin Turkiyya ta ce an kashe sojojinta uku a wani hari da suka kai wa mayaƙan Kurdawa a kusa da Iraƙi.
An kai harin ne ga mayaƙan da ke goyon bayan ƙungiyar PKK ta Kurdawan, waɗanda suka jima suna yaƙin sunkuru da Turkiyya.
Mayaƙan Kurdawan sun shafe shekaru suna amfani da tsaunuka a arewacin Iraƙi a matsayin sansani, inda kuma mayaƙan Turkiyyan ke yawan kai musu hari a can.
Turkiyya da wasu ƙasashen duniya na kallon PKK a matsayin ƙungiyar ta'addanci, waɗanda suka daɗe suna amfani da tsaunukan Iraƙi a matsayin gidan ɓuya a yaƙin da take yi da dakarun Turkiyya.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban ƙasar Belarus, Alexander Lukashenko, ya faɗa wa wata tawagar wakilai a Minsk babban birnin ƙasar cewa yana da ƙarfin iko matuƙa.
Ya ƙara jaddada alƙawarin da ya yi na cewa za a yi sauyi ga kundin tsarin mulkin ƙasar a bana da zai sa a yi ƙuri'ar raba gardama a baɗi.
Shiru da ya yi kwana biyu kan wannan lamarin ya sa aka fara ce-ceku-ce kan cewa akwai yiwuwar ya fasa cika alƙawarinsa.
Ƴan adawa a ƙasar, waɗanda wasunsu na gidan yari wasu kuma na gudun hijira sun yi kira da kafa gwamnatin riƙon ƙwarya cikin gaggawa wadda za ta shirya zaɓen gaskiya da adalci.

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa tsofaffin masu hidimar ƙasa guda 110 aikin yi tare da tallafin karatu.
Buhari wanda ya bayyana hakan a yau Alhamis yayin wani taron karrama 'yan hidimar ƙasar a fadarsa mai laƙabin 2018/2019 President’s National Youth Service Corps, ya kuma ba su kyautar kuɗi.
Matasan na cikin waɗanda suka yi wa ƙasa hidima wato NYSC a shekarar 2018 zuwa 2019 kuma shugaban ya halarci taron ne ta intanet.

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Haka nan ya umarci ma'aikatun gwamnati da su tabbatar an bai wa waɗanda suka samu kyautar kyautukansu sannan ya yi kira ga matasan da su mayar da hankali wurin ci gaba da halayen da suka sa aka zaɓe su.
"Ya kamata a sani cewa matasan maza da mata da aka zaɓa sun yi zarra a ɓangare huɗu na shirin yi wa ƙasa hidima (NYSC); wayar da kai, zuwa wurin aiki, ayyukan raya al'umma da kuma kammala aikin, waɗanda su ne sharuɗan samun kyautar," in ji shugaban.
"A madadin gwamnati da kuma 'yan Najeriya, ina taya waɗanda aka karrama murna bisa kere wa tsaransu domin samun wannan kyauta."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Joe Biden ya amince da wani umarnin shugaban ƙasa da ya ƙaƙaba wa sojojin da suka yi juyin mulki a Myanmar takunkumi.
Matakin zai karkata kacokam kan jagororin sojojin da iyalansu da kuma harkokin kasuwancinsu.
Kazalika ana ɗaukar matakin hana su taɓa kuɗi mallakin ƙasar kusan dala biliyan ɗaya da ke ajiye a Amurkar.
Hukuncin ya zo ne biyo bayan harbin wata mai zanga-zanga da aka yi a kanta, inda take rai-kwakwai-mutu-kwakwai a gadon asibiti.
An ji wa Mya Thwe Thwe Khaing rauni ne ranar Talata lokacin da 'yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zanga da ruwa mai ƙarfi da harsasan roba har ma da harsasai masu kisa.
Dubban masu zanga-zanga ne suka taru domin yin Allah-wadai da juyin mulkin na makon da ya wuce, wanda ya tumɓuke gwamnatin Aung San Suu Kyi a ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya Mal Alfarma Sa'ad Abubakar III ta buƙaci al'ummar Musulmi da su fara duba sabon watan Rajab na kalandar Hijira daga daren gobe Juma'a.
Cikin wata sanarwa da Farfesa Sambo Wali Junaidu ya sanya wa hannu, fadar ta ce Juma'ar ce za ta zama 29 ga watan Jumadal Akhirah wadda ta yi daidai da 12 ga watan Fabarairun 2021.
Sanarwar ta buƙaci mutane da su kai rahoton ganin watan ga dagaci ko mai unguwa mafi kusa da su domin isar da saƙon ganin ga Sarkin Musulmi.
Rajab ne na bakwai a jerin watannin kalandar Musulunci, wadda ke da kwana 29 a kowane wata - amma yana kaiwa 30 idan ba a ga sabon watan ba a daren 29 ɗin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta kama wani mutum kan zarginsa da yaɗa labarin karya cewa mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji a Borno.
Kafar yaɗa labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewamutumin mai shekara 29 ya yi zargin cewa mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji biyar tare da sace wasu da dama, a yayin da ma’aikata ke gyaran wuta a kan titin Maiduguri-Damaturu ranar Litinin ɗin da ta gabata.
Mutumin ya yaɗa labarin ƙaryar ne ranar 8 ga watan Fabrairu. PRNigeria ta ruwaito wata majiyar soji ta ce an kama mutumin ne wanda ɗan bijilante ne a yankin Shehuri ta arewa a cikin birnin Maiduguri, a yayin da yake bakin aikinsa.
Majiyar ta ƙara da cewa mutumin ya yaɗa labarin ƙaryar duk da ya san cewa hakan na iya sanya fargaba a zuƙatan ƴan ƙasa.
Sai dai kafar ta PRNigeria ta gano cewa wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa an ƙwace iko da shafinsa ne aka aika saƙon ƙaryar.
Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin Ado Isa a wata sanarwa ya bayyana rahoton da cewa na ƙarya.

Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta fara riga-kafin korona ga adadi ƙanƙani na Falasɗinawa da ke shiga ƙasar domin su yi aiki.
Ana ganin wannan ne karo na farko da ƙasar ta yi riga-kafi ga Falasɗinawa daga Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, idan ba wai ma'aikatan lafiya da ke can ba.
Wakililin BBC ya ce jami'an lafiyan Isra'ila sun fara yi wa Falasɗinawa riga-kafin ne a wani shingen bincike na kan hanya a kusa da birnin Qudus.
Dubban Falasdinawa ne ke aiki a cikin Isra'ila inda wasu ke aiki a gonaki wasu kuma a wuraren gine-gine.
Shirin yin allurar riga-kafi na Isra'ila shi ne wanda ya fi sauri a duk duniya.
Sai dai ƙin yi wa Falasɗinawa da ke zaune a yankin na Isra'ila ya jawo wa ƙsar caccaka daga ƙasashen duniya.

Asalin hoton, EPA
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya tattauna da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan kan kokarin kawo karshen yakin Yemen da karfafa tsarin tsaron Saudiyya.
Majiyoyi daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya sun ce, ministocin biyu sun tattauna kan bukatar samo hanyar siyasa ta magance yaƙin Yemen.
Tun shekarar 2015, Saudiyya ta jagoranci ƙawance a Yemen don tallafa wa sojojin gwamnati da ke fada da Houthis mai ƙawance da Iran.
Jami'an Majalisar Dinkin Duniya na kokarin farfado da tattaunawar zaman lafiyar.
Kungiyar Houthi ta Yeman ta fada a ranar Laraba cewa ta kai wani harin jirgi mara matuki a filin jirgin saman Abha na Saudiyya.
Shugaban Amurka Joe Biden, a makon da ya gabata, ya nada jami’in diflomasiyya Tim Lenderking a matsayin jakadan Amurka na musamman a Yemen, a wani yunkuri na karfafa kokarin diflomasiyyar Amurka na kawo karshen yaƙin.
Sabuwar gwamnatin a Washington ma ta sanar da kawo karshen goyon bayanta ga ayyukan sojin da Saudiyya ke jagoranta a Yemen.
Amma jami'an sun tattauna a wayar tarho kan hadin gwiwa don tallafa wa tsarin tsaron Saudiyya don magance hare-hare kan masarautar.
A ƴan kwanakin ana ci gaba da yin muhawara a arewacin Najeriya kan batun ko a soke lefe ko a ci gaba da yinsa.
Wasu mazauna yankunan jihar Maradi a Jamhuriyyar Nijar ne ke kokawa da yadda matsalar tsaro ke daɗa taɓarɓarewa.
Mazaunan sun ce a ƴan kwanakin nan suna fuskantar yawaita hare-hare daga ƴan bindiga.
Daga Yamai ga rahoton Tchima Illa Issoufou:
Gwamnan farar hula na farko na jihar Legas Alhaji Lateef Kayode Jakande ya rasu, kamar yadda gwamnan jihar Babajide San-Olu ya sanar a shafinsa na Tuwita.
Gwamna San-Olu ya ce jihar Legas ba za ta taɓa mantawa da irin gudunmowar da marigayin ya bai wa jihar da al'umma.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ta ta fara bincike kan wani bidiyo da ya yaɗu a intanet kamar wutar daji, da ke nuna yadda wasu matasa suka dinga zane wasu ƴan mata da dorina.
A sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce an ja hankalinta ne kan wannan bidiyo, inda ta jajantawa waɗanda lamarin ya faru da su, tare da shan alwashin gano waɗanda suka aikata wannan abu da gurfanar da su gaban shari'a.
Sanarwar me ɗauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, SP Ahmed Mohammad Wakil ta ce tuni rundunar ƴan sandan ta gayyaci ƴan matan da abin ya shafa da su bayar da bayanan da za su kai ga kama tare da gurfanar da samarin a gaban shari'a.
Bidiyon yana nuna yadda wasu zaratan matasa ɗauke da dorina da adduna a hannayensu suka rutsa wasu ƴan mata wani kango.
Bidiyon yana nuna yadda wasu zaratan matasa ɗauke da dorina da adduna a hannayensu suka rutsa wasu ƴan mata wani kango.
Ku karanta cikakken labarin a nan.

Asalin hoton, Getty Images
Masu fafutukar kare haƙƙin mata da ƙananan yara sun alaƙanta ƙaruwar cin zarafin mata da ake samu a jihar Gombe da jan ƙafar da ake yi a shari'o'in masu aikata lalata.
Wani bincike na baya-bayan nan ya ce Gombe na cikin jihohin da ke sahun gaba a Najeriya a yawan cin zarafin yara.
Haka kuma, an danganta ƙaruwar lamarin da rashin ƙwararan dokokin hukunta masu aikata laifin a jihar.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Maikuɗi Shehu ya ce kusan kullum suna samun rahoton fyaɗe musamman na ƙananan yara.
Ya ce "sai ka ga dattijo ya lalata ƙaramar yarinya. Wannan ba ya rasa nasaba da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi. Shi ya sa muke duba yadda za mu shawo kan wannan matsala"
Wata mai fafutukar kare haƙƙin,Hajiiya Fati Usman Kulani ta ce idan ba a yi wa tufkar hanci tun yanzu ba, nan gaba abun zai gagari kowa.
Ta kuma ce ana aikata waɗannan laifukan ne kan talakawa marasa galihu da ba za su iya ɗaukar nauyin shari'a ba.
"Sau da yawa waɗanda suka aika laifin sun fi iyayen yaran da aka lalata. Don haka sai a bar iyayen yara da zirag-zirga, ai da dage shari'ar har abin ya bi ruwa," a cewarta.
Ta kuma ce iyayen yara su daina kunyar kai ƙara.
Sai dai a kwanan nan ne aka gabatar da wani ƙudiri a gaban majalisa wadda za ta sa a tsaurara hukunci ga masu cin zarafin ƙananan yara.

Kakakin ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta a Yemen da ke yaƙi da ƴan tawayen Houthi a Yemen ya ce ƙawancen ya daƙile wani harin jirgi marar matuƙi da ƴan Houthin suka aika garin Khamis Mushait a kusa da iyakar Saudiyya a Kudu maso yammaci.
Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya ce jirgin na ɗauke ne da abubuwan fashewa kuma an yi ƙoƙarin kai wa fararen hula hari ne.
Haka kuma, ƙawancen ya ce ƴan Houthi si yi ƙoƙarin kai hari filin jirgin sama na Abha wanda ke kusa da Khamis Mushait inda har wani jirgin fararen hula ya kama da wuta.
Ƴan Houthin sun dau alhakin hari na filin jirgin kuma sun ce sun so kai hari ne a ma'ajiyar jiragen saman yaƙi da ke wurin.