Allah ƙara wa Ganduje lafiya da tsawon kwana ‒ Buhari

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da duniya.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh and Mustapha Musa Kaita

  1. 'Sai an bunƙasa rayuwar matasa kafin a magance matsalar tsaro'

    Kungiyar dawo da martabar arewacin Najeriya ta ce zai yi wuya a shawo kan matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin, sai gwamantin kasar ta samarwa da matasa aikin yi da hanyoyin da za su bunkasa tattalin arzikinsu.

    Kakakin kungiyar Malam Faruk Umar ya shaida wa BBC cewar akwai bukatar gwamnatin kasar ta shigar da tsoffin ma'aikatan tsaron kasar cikin rudunar mayakan sa kai, domin ƙara musu ƙarfi wajen tunkarar yƴan Boko Haram da ƴan bindiga.

    Ga dai yadda hirarsa ta kasance da Khalifa shehu Dokaji inda ya faraa da tambayarsa ko mene ne bambancin kungiyarsu da sauran kungiyoyin arewacin Najeriya?

    Ku latsa lasifikar da ke ƙasa don sauraron hirar:

    Bayanan sautiHirar Dokaji da Malam Umar Faruk
  2. Shugabannin EU sun yi murna da yarjejeniyar cinikayya tsakaninsu da Birtaniya

    Macron

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabannin ƙasashen Tarayyar Turai EU 27 sun yi maraba da cimma yarjejeniyar cinikayyar da aka yi tsakaninsu da Birtaniya.

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce irin haɗin kai da kuma dagewar da Turai ta nuna yayin tattaunawar da aka yi kan yarjejeniyar, kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

    Ya saka a shafinsa na Tuwita cewar yanzu Tarayyar Turai za ta iya tsara yadda gobenta za ta kasance tana mai cikakken ƴanci da kuma ƙarfi.

    Takwararsa ta Jamus Angeka Merkel ta bayyana yarjejeniyar a zaman wani kyakkyawan sakamako.

    Yayin da shi kuwa Ministan Harkokin Wajen Denmark ya ce babu wani abu da Birtaniya da kuma EU za su iya bai wa junansu a matsayin goron Kirsimeti da ya kai cimma wannan yarjejeniyar.

    Masu fashin baƙi suna cewa da a ce Birtaniya ta fice ba tare da cimma wannan yarjejeniya ba da tabbas za ta afka cikin ruɗani ta fuskar tattalin arziki da siyasa da kuma zamantakewa.

    Sai dai ga alama tana ƙasa tana dabo don sai dukkan ɓangarorin biyun sun jefa ƙuri'ar amincewa da yarjejeniyar a Majalisar Dokoki kafin ta fara aiki a watan Janairu.

    A Birtaniya ana sa ran ƴan majalisar su kaɗa ƙuri'ar amincewar cikin sauƙi a makon gobe.

    Babbar jam'iyyar adawa ta Labour ta ce za ta goyi bayan yarjejeniyar duk da cewa tana da ƙorafe-ƙorafe game da ita.

    A ɓangaren Tarayyar Turai kuwa Minsitan Harkokin Wajen Jamus ya ce ƙasarsa za ta taimaka wajen amincewa da yarjejeniyar cikin sauri.

    A halin yanzu Jamus ce ke riƙe da shugabancin EU.

    Ya zama dole majalisar dokokin EU ta amince, amma ana iya fara aiki da dokar na wucin gadi gabanin ƴan majalisa su jefa ƙuri'a a kanta.

  3. An fara yi wa ƴan ƙasashen Mexico da Chile da Costa Rica allurar riga-kafin cutar korona

    An yi wa malamar jinya ƴar Mexico allurar riga-kafin cutar korona

    Asalin hoton, Reuters

    Wata malamar jinya ƴar Mexico ce ta farko a yankin Latin Amurka da aka yi wa allurar riga-kafin cutar korona, a lokacin da ƙasarta ta fara yi wa al'umma a wani gangamin yin riga-kafin a ranar Alhamis.

    Tun da fari Mexico ta karɓi alluran 3,000 na samfurin Pfizer-BioNTech.

    Ƙasar na daga cikin waɗanda aka samu yawan mace-macen mutane sakamakon annobar a duniya, baya ga Amurka da Brazil da Indiya.

    Jim kaɗan bayan hakan a ranar Alhamis ɗin sai Chile da Costa Rica ma suka fara yin allurar riga-kafin cutar koronan ta kamfanin Pfizer-BioNTech.

  4. Buhari ya soke ziyarar gaisuwar Kirsimeti zuwa fadarsa

    Buhari da takunkumi

    Asalin hoton, MBuhari

    Bayanan hoto, An dauki matakin ne don bin dokokin hana yaduwar cutar korona

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soke duk wata ziyara zuwa fadar shugaban kasa domin karbar bakin da zasuyi gaisuwar Kirsimeti ga shugaban kasar a fadarsa ta Abuja.

    Ya bayyana hakane ne a wata sanarwa da fadar tasa ta aike wa manema labarai a ranar Alhamis inda ya ce ya ɗauki wannan matakin ne don bin ƙa’idojin da Kwamitin Shugaban Ƙasa da ke yaƙi da Cutar Korona ya shimfiɗa.

    “A sakamakon haka shugaban ba zai samu ganawa da shugabannin addinai da masu sarautun gargajiya ba kamar yadda aka saba a duk ranar Kirsimeti,” in ji sanarwar.

    Ita ma rundunar tsaro ta ‘yan sanda a kasar ta ce za ta tsananta daukar matakan tsaro sakamakon wasu rahotanni daga cibiyoyin tsaro su ka nuna akwai yiwuwa akai hare hare a wasu wurare ma su muhinmanci ga al’umma da kasar kanta.

    Ga rahoton Umar Shehu Elleman kan batun:

    Bayanan sautiRahoton Umar Elleman kan tsaro a ranar Kirsimetin 2020
  5. Buɗewa

    Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa assalamu alaikum, barkanmu da wayar gari lafiya kuma barkanmu da Juma'a.

    Sannan muna yi wa dukkan Kiristoci barka da ranar Kirsimeti.

    Ku kasance da mu a wannan shafi daga yanzu har dare domin samun labarai da rahotanni kai tsaye daga Najeriya da Afirka da saurahn sassan duniya.

    Za kuma ku dinga samun labarai da hotuna kan yadda ake gudanar da bikin Kirsimeti a sassa daban-daban, da labaran annobar cutar korona da kuma duk wani abu da ya shafe ku.

    Sunana Halima Umar Saleh zan ja ragamar shafin a wannan safiya kafin daga bisani abokin aikina Mustapha Musa Kaita ya karɓa.

    Halima Umar Saleh

    Asalin hoton, Halima