Ƴan bindiga sun kashe mutum 8 da ƙona buhunan masara 330 a Kaduna
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Imam Saleh and Mustapha Musa Kaita
Birtaniya ta hana jiragen da suka taso daga Afrika Ta Kudu sauka a Ingila
Asalin hoton, Getty Images
Birtaniya ta hana dukkanin jiragen saman da
suka taso daga Afrika Ta Kudu sauka a Ingila domin hana bazuwar sabon nau'in
annobar Coronavirus.
Sakataren sufurin Birtaniya Grant Shapps ya
ce matakan za su fara aiki ne da safiyar nan ta Alhamis.
An dai fara gano mutane biyu da suka harbu
da sabon nau'in cutar a Ingila ranar Talata.
Masana Kimiyya sun ce ya riga ya bazu cikin
sauri a sassa daban-daban na Africa Ta kudu.
Birtaniya dai na fadi tashin ganin ta hana
barkewar sabon nau'in annobar, abin da ya sa kasashen duniya suka hana matafiya
daga Birtaniya shiga cikinsu.
Ku saurari Labaran Duniya cikin Minti Ɗaya da BBC Hausa
Bayanan sautiLabarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Safe 24/12/2020
Shugaba Trump ya sake yi wa "mutanensa" afuwa
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Donald Trump ya sake yin afuwa ga
wasu mutanen da yi musu afuwar zai iya sake jawo ka-ce-na-ce yayin da wa'adin
mulkinsa ke zuwa karshe.
Tsohon manajan Kamfe na Mr. Trump Paul
Manafort da wani dadadden mai ba shi shawara Roger stone na daga cikin mutane
26 da ya sake yi wa afuwa.
Dukansu an daure su ne bayan samunsu da
laifi da kwamitin Mueller ya yi a binciken katsalandan din ake zargin Rasha ta
yi a zaben shugaban kasar Amurka na 2016.
Mr. Trump haka ma ya saka Charles Kushner,
mahaifin surukinsa Jared Kushner cikin wadanda ya yi wa afuwa.
Mr. Kushner dai ya yi zaman sarƙa na shekaru
biyu kan kaucewa biyan haraji, da ɓoye shaida da kuma bayar da kudi don yin
yakin neman zabe ba bisa ka'ida ba.
Wannan mataki ya nuna irin
yadda shugaban ya tsaya kai da fata wajen ganin ya cire duk wadanda aka samu da
laifi a wannan binciken na Mueller kan zargin kutsen Rasha a zaben 2016 daga
sarƙa. Kuma a da ya sha nuna adawa a binciken yana kiransa na bogi.
Dan majalisa a Indiya ya saki matarsa don ta sauya jam'iyya
Asalin hoton, BAPI BANERJEE
Auren wani ɗan majalisar dokoki a Indiya da matarsa da ya fi shekara 10 yana rawa bayan da ya aika mata saƙon sakinta sakamakon sauya jam'iyya da ta yi.
A ranar Talata ne Saumitra Khan na jihar Bengal da ke yammacin ƙasar na jam'iyyar Fira Minista Narendra Modi wato BJP, ya aika wa matarsa Sujata Mondal Khan saƙon saki, kwana guda bayan da ta sauya sheƙa zuwa jam'iyyar TMC.
Jihar West Bengal na shirye-shiryen yin zaɓukan majalisar dokoki nan da watanni kaɗan kuma za a fi fafatawa ne tsakanin jam'iyyun BJP da kuma TMC.
A wajen wani taron manema labarai a babban birnin jihar, Kolkata a ranar Litinin, Ms Mondal Khan ta sanar da matakinta na barin jam'iyyar BJP tare da bayyana dalilanta na yin hakan.
Ta ce jam'iyyar ba ta nuna mata girmamawa ko kaɗan, inda ta fi karɓar "baragurbin ƴan siyasa" daga jam'iyyun adawa tana fifita su fiye da ƴan jam'iyya na ainihi masu kishinta.
Sa'o'i kaɗan bayan nan sai ɗan majalisar ya kira wani taron gaggawa na manema labarai, inda Mista Khan mai shekara 40 cikin hawaye da takaici ya sanar da matakin da ya ɗauka na rabuwa da matarsa bayan shafe shekara 10 suna tare.
Ya umarce ta da ta daina amfani da sunansa Khan a gaban sunanta, inda ya ce ya sakar mata mara ta je ta cika dukkan muradunta na siyasa, kamar yadda kafar yada labran Press Trust ta ruwaito shi yana faɗa.
Daga nan sai ya zargi jam'iyyar TMC da rusa masa gida.
"TMC ta sace min mata, ta ƙwace min farin cikina da soyayyata," a cewarsa..
Yau ake sa ran cimma yarjejeniya kan ficewar Burtaniya daga EU
Asalin hoton, Reuters
Tattaunawa tsakanin Burtaniya da EU kan yarjejeniyar cinikayya bayan Brexit na ci gaba, yayin da ake sa ran cimma yarjejeniya nan gaba a yau Alhamis.
Masu shiga tsakani a Brussels na ta kokarin kammala cika sharudddan kamun kifii, abin da ya jima yana yiwa yarjejeniyar tarnaki.
Ana sa ran Firai ministan Burtaniya Boris Johnson zai yi magana da shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta wayar tarho,
Editar siyasa ta BBC Laura Kuenssberg ta ce.
Bayan haka ana sa ran taron manema labarai zai biyo baya.
Kuenssberg ta ce ta fahimci an yi tattaunawar waya sau hudu tsakanin mutanen biyu don cimma yarjejeniyar Brexit, wandda a na karshen ne ake sa ran za a kammala komi a kuma rattabawa yarjejeniyar hannu.
Buɗewa
Bayani kan maƙala
Marubuci, Imam Saleh
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
Masu bibiyarmu a wannan shafi barka da warhaka da fatan kun wayi gari lafiya.
Imam Saleh ke fatan kasancewa da ku don kawo muku labarai kai tsaye, dangane da irin wainar da ake toyawa a sassan duniya daban-daban musamman Najeriya da Nijar, Kamaru da Chadi.