Auren wani ɗan majalisar dokoki a Indiya da matarsa da ya fi shekara 10 yana rawa bayan da ya aika mata saƙon sakinta sakamakon sauya jam'iyya da ta yi.
A ranar Talata ne Saumitra Khan na jihar Bengal da ke yammacin ƙasar na jam'iyyar Fira Minista Narendra Modi wato BJP, ya aika wa matarsa Sujata Mondal Khan saƙon saki, kwana guda bayan da ta sauya sheƙa zuwa jam'iyyar TMC.
Jihar West Bengal na shirye-shiryen yin zaɓukan majalisar dokoki nan da watanni kaɗan kuma za a fi fafatawa ne tsakanin jam'iyyun BJP da kuma TMC.
A wajen wani taron manema labarai a babban birnin jihar, Kolkata a ranar Litinin, Ms Mondal Khan ta sanar da matakinta na barin jam'iyyar BJP tare da bayyana dalilanta na yin hakan.
Ta ce jam'iyyar ba ta nuna mata girmamawa ko kaɗan, inda ta fi karɓar "baragurbin ƴan siyasa" daga jam'iyyun adawa tana fifita su fiye da ƴan jam'iyya na ainihi masu kishinta.
Sa'o'i kaɗan bayan nan sai ɗan majalisar ya kira wani taron gaggawa na manema labarai, inda Mista Khan mai shekara 40 cikin hawaye da takaici ya sanar da matakin da ya ɗauka na rabuwa da matarsa bayan shafe shekara 10 suna tare.
Ya umarce ta da ta daina amfani da sunansa Khan a gaban sunanta, inda ya ce ya sakar mata mara ta je ta cika dukkan muradunta na siyasa, kamar yadda kafar yada labran Press Trust ta ruwaito shi yana faɗa.
Daga nan sai ya zargi jam'iyyar TMC da rusa masa gida.
"TMC ta sace min mata, ta ƙwace min farin cikina da soyayyata," a cewarsa..