Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ƴan bindiga sun kashe mutum 8 da ƙona buhunan masara 330 a Kaduna

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Imam Saleh and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Imam Saleh
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu ta wannan shafi a nan muka zo ga ƙarshen kawo muku labaran duniya kai tsaye.

    Da fatan za ku kasance da mu gobe idan Allah ya kaimu domin ci gaba.

    Imam Saleh ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Paparoma ya roƙi ƙasashe su taimaki juna da rigakafin korona

    A sakonsa na barka da arzikin zagayowar ranar kirsimeti, shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya bukaci kasashen duniya da su taimaka wa juna a yaki da kwayar cutar korona ta hanyar samar da allurar rigakafin ta ga kowa.

    "Yau, a wannan lokacin na duhu da rashin tabbas yayin annobar, fitilu daban-daban na fata na gari sun bayyana, kamar gano alluran rigakafin da dole ne kowa ya samu," inji Paparoman yayin da yake gabatar da jawabinsa na shekara shekara ga jama'ar duniya.

    "Ina roƙon duk shugabanni kamfanonin samar da wadannan magunguna da sauran masu fada a ji su inganta haɗin kai, ba wai maganar gasa ba, su nemi mafita ga kowa, a bayar da allurar rigakafi ga kowa, musamman ga marasa ƙarfi da mabukata a duk yankunan duniya." inji Paparoma.

  3. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye, sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau:

    • Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda uku a Benue
    • Iran ta gargaɗi Donald Trump
    • Asibitoci a Afrika Ta Kudu na cikin matsin lamba
    • Sojojin Ethiopia sun kashe sama da mutum 40 da ke zargi da kisan kiyashi
    • APC ta ji kunya kan rashin tsaro - Gwamnan Rivers

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  4. 'Yan ci-rani 20 sun mutu a hatsarin kwale-kwale kusa da Tunisia

    Jami'an da ke gadin teku sun gano gawarwakin ƴan-cirani 20 waɗanda suka mutu bayan kwalekwalensu ya jirkice a kusa da ruwan Tunisia.

    A yanzu dai ana ci gaba da neman aƙalla mutum 15 da har yanzu ba a gano su ba, ciki har da ƙananan yara.

    Sai dai jami'an sun samu nasarar ceto mutum biyar.

    Ana kyautata zaton waɗanda ke cikin jirgin ruwan sun fito ne daga yankin Afrika.

    'Yan ci-ranin sun taso ne daga tashar ruwa ta Sfax ta Tunisia inda suka kama hanyar zuwa tsibirin Lampedusa da ke Italiya.

  5. Ra'ayin Sheik Gumi dangane da riga-kafin korona a mahangar Musulunci

  6. Ƴan bindiga sun kashe mutum 7 da ƙona buhunan masara 330 a Kaduna

    Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa ƴan bindiga sun kai hari a kasuwar Galadimawa da ke Ƙaramar Hukumar Giwa, lamarin da ya ja aka tafka mummunar asara.

    A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar, ya bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe 'yan banga biyu da wasu mutum biyar.

    A harin dai, 'yan bindigar waɗanda suka je kasuwar kan babura 15 sun yi sanadiyar ƙonewar wata ƙaramar mota da kuma buhunan masara 330 da ke cikin wata tirela mallakar wani direba mai suna Alhaji Yusuf Tumburku.

    Rahotanni dai sun ce ɓarayin tun farko sun shiga kasuwar ne da misalin ƙarfe huɗu na yamma inda suka buɗe wa ƴan bangar wuta.

    Amma daga baya jami'an tsaro da suka haɗa da sojojin sama sun bi ɓarayin inda suka samu nasarar kashe wasu daga cikinsu, kamar yadda sanarwar da kwamishinan ya fitar ta bayyana.

  7. Sojojin Ethiopia sun kashe sama da mutum 40 da ke zargi da kisan kiyashi

    Sojojin Ethiopia sun kashe sama da mutum 40 da ake zargi da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa aƙalla mutum 100, cikin har da yara a wani ƙauye da ke yankin jihar Benishangul-Gumuz, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta ƙasar ta ruwaito.

    Rahotanni sun ce akwai jami'a biyar waɗanda suka yi murabus da masu ci a yanzu da aka kama sakamakon zarginsu da hannu a rikicin.

    Waɗanda suka yi kisan kiyashin sun ƙona gidaje yayin da 'yan ƙauyen ke bacci a ciki, tare da harbin mutane da caka musu wuƙa a safiyar Laraba.

    Wannan harin na zuwa ne kwana guda bayan Firaiministan ƙasar, Abiy Ahmed ya kai ziyara yankin.

  8. Asibitoci a Afrika Ta Kudu na cikin matsin lamba

    Hukumomi a Afrika Ta Kudu sun ce asibitoci a yammacin yankin Cape na cikin matsin lamba sakamakon ƙara yaɗuwar korona, inda ake tunanin sabon nau'in cutar ne ke janyo hakan.

    Ƙasar na fama da tsananin yaɗuwar cutar inda ko a jiya Laraba sai da aka tabbatar da cewa mutum dubu 14 sun kamu.

    Gwamnatin yankin ta bayyana cewa asibitoci na cika maƙil da mutane.

    Masana kimiyya na cewa sabon nau'in cutar ya fi saurin yaɗuwa fiye da na baya.

    Tuni dai Birtaniya ta dakatar da jiragenta daga zwa Afrika Ta Kudu haka kuma ta dakatar da na ƙasar daga zuwa Birtaniyar.

    A wani ɓangaren kuma jami'an lafiya na zargin cewa akwai yiwuwar an samu sabon nau'in wannan cuta a Najeriya

  9. Iran ta gargaɗi Donald Trump

    Ƙasar Iran ta yi watsi da zargin da Shugaban Amurka mai barin gado, Donald Trump ya yi cewa ita ta kai harin makamanin roka a wani ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza a makon nan.

    Ministan harkokin wajen Iran, Javad Zarif, ya gargaɗi Mista Trump ɗin kan yin wata kasada a kwanakinsa na ƙarshe a matsayin shugaban ƙasa.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Trump ɗin ya bayyana cewa idan aka kuskura aka kashe ɗan Amurka guda, zai ɗora alhakin kisan kan Iran.

    Babu wanda ya mutu a harin da aka kai wa ofishin jakadancin a ranar Lahadi, sai dai wani farar hula guda ,dan asalin Iraƙi ya samu rauni.

  10. Indiya: Ɗan majalisar da ya saki matarsa saboda ta sauya jam'iyya

    Auren wani ɗan majalisar dokoki a Indiya da matarsa da ya fi shekara 10 yana rawa bayan da ya aika mata saƙon sakinta sakamakon sauya jam'iyya da ta yi.

    A ranar Talata ne Saumitra Khan na jihar Bengal da ke yammacin ƙasar na jam'iyyar Fira Minista Narendra Modi wato BJP, ya aika wa matarsa Sujata Mondal Khan saƙon saki, kwana guda bayan da ta sauya sheƙa zuwa jam'iyyar TMC.

    Jihar West Bengal na shirye-shiryen yin zaɓukan majalisar dokoki nan da watanni kaɗan kuma za a fi fafatawa ne tsakanin jam'iyyun BJP da kuma TMC.

    Karanta cikakken labarin a nan:

  11. Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda uku a Benue

    Rahotanni na cewa yan bindiga sun hallaka wasu mutane biyar, ciki harda ƴan sanda uku a gidan Alfred Avalumun Atera, shugaban Karamar Hukumar Katsina-Ala da ke Jihar Benuwai.

    Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa an kuma jikkata mutane da dama a yayin harin da aka kai da misalin karfe 11:30 na safe.

    Majiyoyin sun ce lamarin ya janyo tashin hankali a yankin, kafin daga bisani yan sanda suka shawo kansa.

    Jami'in watsa labarai na ƙaramar hukumar Tertesa Benga ya tabbatarwa Daily Sun aukuwar lamarin.

  12. Dakarun Habasha sun kashe mutane 40 da ake zargi da kisan kiyashi

    Sojojin Habasha sun kashe wasu mutane 40 da ake zargi da alaka da kisan kiyashin da aka yiwa akalla mutane 100, ciki har da yara, a yankin Benishangul-Gumuz, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta ruwaito.

    Rahotannin sun kara da cewa an kuma kama wasu jami'an gwamnati dake kan mukami a yanzu, da kuma wasu tsaffi da ake zargi da hannu a lamarin.

    Maharan sun kone gidajen mazauna kauyukan yayin da suke bacci, sannan suka yi ta harbe-harbe da daba wa mutane wuka a harin na ranar Laraba.

    Harin ya zo ne kwana daya bayan Firai minista Abiy Ahmed ya ziyarci yankin.

  13. APC ta ji kunya kan rashin tsaro - Gwamnan Rivers

    Gwamnan jihar Rivers a Najeriya Nyesom Wike, ya shawarci ƴan uwansa gwamnoni na jam'iyyar APC da kada su ji kunyar amincewa da cewa jam'iyyarsu ta APC ta gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'ar Najeriya.

    Ya ce ba zai isa ba, idan gwamnonin suka amince da cewa akwai matsalar tsaro ba tare da sun ɗaura alhakin hakan a kan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba.

    Yana magana ne yayin ƙaddamar da aikin wata hanya da gwamnan jihar Oyo ya samar a garin Obagi.

    ''Komai ya rushe a ƙasar nan, tsaro ya taɓarɓare, tattalin arziƙin ƙasa ya ruguje, ba wani abu dake tafiya a wannan ƙasar, yau matsalar tsaro ta shiga ko ina a Najeriya. APC ta ji kunya'' inji gwamnan, kamar yadda jaridar The Punch ta rawaito.

  14. Za a rantsar da shugaban Ghana a majalisar dokoki

    Gwamnatin Ghana ta ce shugaban ƙasar nana Akufo-Addo zai sha rantsuwar kama aiki ne a majalisar dokokin ƙasar maimakon dandalin yancin kai na Independence Square.

    Mataimakin ministan watsa labaran ƙasar Piu Enam Hdzide, ya ce an ɗauki matakin ne sakamakon buƙatar da majalisar dokokin ƙasar ta miƙa.

    Sannan ya ce za a bi dokokin da aka shimfida na kaucewa kamuwa da cutar korona.

    A ranar 9 ga watan Disamban nan ne hukumar zaɓen Ghana ta sanar da cewa shugaban ƙasar mai ci ne ya lashe zaɓen da aka gudanar, inda ya yi nasara a kan babban abokin hamayyarsa tsohon Shugaba John Dramani Mahama.

    Shugaba Nana Akufo Addo ya yi nasara da kashi 50.8 cikin 100 a cewar shugabar hukumar zaɓen Jean Mensa. Alƙaluman sun nuna cewa Nana Akufo-Addo na jam'iyyar NPP ya samu ƙuri'a 6,730,413.

  15. Buhari ya amince da sakin sama da Biliyan 44 don samar da tituna a Abuja

    Majalisar zartarwar Najeriya ƙarƙshin jagorancin shugaba Muhamamdu Buhari ta amince da sakin sama da Naira Biliyan 44 domin bada kwangilar samar da tituna a Abuja.

    Aikin wanda zai gudana ƙarƙshin ma'aikatar kula da babban birnin da kuma ma'aikatar ayyuka da gidaje ya ƙunshi inganta samar da ruwan sha, da kuma samar da tituna a sassan ƙwaryar birnin.

    Jaridar The Nations ta ambato ministan watsa labaran Najeriya Lai Muhammad na cewa an amince da sakin Naira Biliyan 31,630,221,349 a kan waɗannan ayyuka.

    Shima ministan ayyukada gidaje Babatunda Fashola, ya ce ma'aikatarsa ta haɗa hannu da hukumar kula da ingancin tituna ta FERMA, domin tabbatar da anyi aikin yadda ya kamata.

    Ya ce aikin zai laƙume naira Biliyan 8,180,948,137.50.

  16. An fara yi wa mutane allurar riga-kafin Covid-19 a Kuwait

    An yi wa Fira ministan Kuwait Sheikh Sabah Al-Khalid Al-Hamad Al-Sabah allurar riga-kafin cutar korona ta kamfanin Pfizer.

    Fira ministan ya ce "A yau 24 ga watan Disamba mun fara yin allurar riga-kafin cutar korona. Don haka ina son godewa kwamitocin Ma'aikatar Lafiya da suka yi ƙoƙarin ganin yiwuwar hakan."

    Ya ce a jiya ne ƙasar ta karɓi allurar riga-kafin Pfizer ɗin kuma an fara bayar da ita a yau ga mutanen ƙasar.

    Ya ƙara da cewa za a shafe tsawon watanni ana yin ta ta yadda dukkan al'ummar ƙasar za su samu yi.

  17. Bidiyon Matan Afirkan da shekarar 2020 ta yi musu rana duk da annobar korona

  18. Faransa ta zargi tsohon shugaban kasar Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka François Bozizé da son hana yin zabukan kasar

    Faransa ta zargi tsohon shugaban kasar Jamhuriyyar Tsakiyar Africa Faransuwa Bozize da kokorin hana a yi zabukan shugaban kasar da 'yan majalisar da aka tsara yi ranar Lahadi.

    Jiragen saman yakin Faransa sun yi shawagi a sararin samaniyar kasar domin nuna rashin amincewar Faransa ga abin da ofishin Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana da kokari hargitsa kasar.

    Faransa dai na da daruruwan sojoji a kasar tare da na MDD wadda adadin nata sojojin ya zarta haka nesa.

    Yiwuwar barkewar rikici ta karu a kasar bayan dakarun gwamnati sun sake karbe garin Bambari da mayakan 'yan tawaye suka mamaye ranar Talata.

    Mr. Bozize dai ya musanta zargin da gwamnati ta yi masa cewa ya hada kai da 'yan tawayen domin kokarin yin juyin mulki.

    Sai dai Jean-Pierre Lacroix jami'i a rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD da ke kasar cewa yake yi:

    Ya ce "mun ga tsohon Shugaba Bozize ya tafi wasu wurare daban-daban a Jamhuriyar Tsakiyyar Afrika inda yake ganawa da shugabannin wasu kungiyoyi kuma a kwananna ma, mun ga alamu karara cewa Bozize na da hannu wajen tsara wa ko kuma ingiza wutar wannan rikicin"

  19. Shin talaucin da Jamhuriyyar Nijar ke fama da shi ana kambama shi ne?

    Jamhuriyyar Nijar ta dade da shiga bakin duniya a matsayin kasar da al'ummarta ke gaba-gaba wajen fama da talauci a duniya.

    Kuma wannan na cikin dalilan da ke sa matasa da dama ke tafiya ci-rani.

    Sai dai wasu masu kare hakkin bil adama na cewa ana kambama talaucin, kamar yadda za ku ji a wannan rahoton da Ibrahim Isa ya aiko mana daga Damagaram.

  20. An gano ma'aikatan bogi fiye da 25,000 a jihar Borno

    Gwamnatin jihar borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce an gano ma'aikatan bogi 25,056 a jihar a matsayin malaman makaranta da ma'aikatan ƙananan hukumomi.

    A wata sanarwa da ta aike wa manema labarai, gwamnatin ta ce an gano hakan ne bayan umarnin da Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayar na yin binciken tantancewa har sau biyu.

    Kwamitoci biyu na tantance ma'aikatan ƙananan hukumomi da na malaman makaranta ne suka gabatar da rahoton binciken nasu ga gwamnan.

    Daga cikin jumullar ma'aikatan bogin, 14,762 suna karɓar albashi ne a matsayin ma'aikatan ƙananan hukumomi, yayin da 7,794 kuma malaman makaranta ne na bogi.

    A sakamakon hakan sanarwar ta ce gwamnati ta yi nasarar samun rarar naira miliyan 420 kamar yadda bayanan da gwamna ya gabatar suka nuna.

    Naira miliyan 183.6 an same su ne bayan dakatar da biyan ma'aikatan bogi na ƙananan hukkmomi yayin da aka samu naira miliyan 237 da ake biyan malaman makaranta.

    Ga wani labari da za ku so karantawa: Wane ne gwamnan Borno Babagana Umara Zulum?