Gwamnatin jihar borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce an gano ma'aikatan bogi 25,056 a jihar a matsayin malaman makaranta da ma'aikatan ƙananan hukumomi.
A wata sanarwa da ta aike wa manema labarai, gwamnatin ta ce an gano hakan ne bayan umarnin da Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayar na yin binciken tantancewa har sau biyu.
Kwamitoci biyu na tantance ma'aikatan ƙananan hukumomi da na malaman makaranta ne suka gabatar da rahoton binciken nasu ga gwamnan.
Daga cikin jumullar ma'aikatan bogin, 14,762 suna karɓar albashi ne a matsayin ma'aikatan ƙananan hukumomi, yayin da 7,794 kuma malaman makaranta ne na bogi.
A sakamakon hakan sanarwar ta ce gwamnati ta yi nasarar samun rarar naira miliyan 420 kamar yadda bayanan da gwamna ya gabatar suka nuna.
Naira miliyan 183.6 an same su ne bayan dakatar da biyan ma'aikatan bogi na ƙananan hukkmomi yayin da aka samu naira miliyan 237 da ake biyan malaman makaranta.