Sakataren Gwamnati Boss Mustapha ya killace kansa saboda korona
Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya, Boss Mustapha, ya killace kansa bayan wasu daga cikin iyalan gidansa sun kamu da cutar korona.
Boss Mustapha wanda shi ne shugaban kwamitin yaƙi da korona na shugaban ƙasa, ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi cikin wata sanarwa.
"Ina mai shaida wa al'umma cewa wasu daga cikin iyalan gidana sun kamu da korona a yammacin jiya (Asabar)," in ji sakataren.
"Duk da cewa ba su fara nuna alamar cutar ba, an killace su kuma suna samun kulawa a ɗaya daga cikin cibiyoyin killace mutane na gwamnati.
"Gwaji ya nuna ni da matata ba ma ɗauke da cutar amma za mu ci gaba da killace kanmu sannan mu yi aiki daga gida kamar yadda dokokin yaƙi da cutar suka tanada.
"Ina so na tunatar da 'yan Najeriya cewa cutar korona gaskiya ce. Kamar yadda hukumar NCDC ta sanar a makon da ya gabata, ana samun ƙarin masu kamuwa da cutar a jihohi da dama."
Kwana huɗu kenan a jere ana samun mutum fiye da 400 da ke kamuwa a kullum a Najeriya da kuma mutum bakwai da suka mutu a ranakun Asabar da Lahadi.