Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona za ta ɓarje gumi da Paris Saint-Germain a zagayen 'yan 16 na gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Hakan na nufin Neymar zai fuskanci tsohon kulob ɗinsa karon farko tun bayan da ya bar su kuma ya sake tabbatar da dalilin da ya sa ya bar ƙungiyar.
Kazalika, babu mamaki ya zama wasan zagayen 'yan 16 na Champions League na ƙarshe ga Messi a cikin jesin Barcelona, ganin yadda abubuwa ke rikicewa tsakanin gwarzon ɗan ƙwallon da mahukuntan ƙungiyar ta Catalonia.
A wasa na ƙarshe da ƙungiyoyin biyu suka buga ranar 8 ga watan Maris na 2017, Barca ce ta lallasa PSG da 6-1 bayan PSG ɗin ta ci wasan farko 4-0.
Wani wasan da zai ja hankali shi ne wanda Chelsea za ta kara da Atletico Madrid.
Kazalika, wadda ta fi kowa goshi a gasar wato Real Madrid za ta yi nata wasan da Atalanta ta Italiya.
Sai kuma masu riƙe da kofin Bayern Munich, wadda za ta gwabza da Lazio ta Italiya.
Ƙungiyar Cristiano Ronaldo ta Juventus za ta buga da FC Porto ta Portugal da kuma karawa tsakanin Sevilla da Borussia Dortmund.
Za a buga wasannin farko ranakun 16,17, 23, 24 na watan Fabarairun 2021, kafin daga bisani a buga na biyun a ranakun 9,10,16,17 na watan Maris.