Boko Haram ta kai hari garin Askira na jihar Borno

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Ƙarin mutum 796 sun kamu da cutar korona a Najeriya

    Korona

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 796 da suka kamu da cutar korona a ranar Juma'a.

    A saƙon da ta wallafa a shafinta na intanet, NCDC ta ce an samu sabbin kamuwar ne a jiha 16 da suka haɗa da Abuja (258) da Legas (248), Kaduna (117), Katsina (52), Ogun (27) sai Kwara (23).

    Jahar Gombe (22), sai Adamawa (17) Plateau na binta (15) sai Kano (6).

    Jihohin Rivers da Ondo da Ekiti da Nasarawa da Sokoto kowannensu na da 2-2, sai Taraba mai mutun 1 tal.

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 72,140 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya. Daga cikinsu, 1,190 sun mutu sannan an sallami 65,712 bayan sun warke daga cutar.

    A ranar 28 ga watan Fabrairu ne aka samu mutum na farko mai ɗauke da cutar a Najeriya, wani dan Italiya da ya shiga birnin Legas ranar 25 ga watan.

    Sannan a ranar 23 ga watan Maris mutum na farko ya mutu sakamakon cutar a Najeriya.

  2. Assalamu Alaikum

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye. Barkanmu da hantsin Asabar.

    Ku biyo ni Umar Mikail domin karanta labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.