Boko Haram ta kai hari garin Askira na jihar Borno
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau
Rufewa
Nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Da fatan za ku kasance da mu gobe inda za mu shafe yinin Lahadi muna kawo labarai da rahotanni kai tsaye.
Za ku iya zuwa har ƙasan wannan shafin domin karanta abubuwan da suka faru a yinin Asabar.
Bayanan hoto, Har yanzu ba a san yawan ɗaliban da aka sace ba a makarantar Kankara a jihar Katsina
Boko Haram ta kai hari garin Askira na jihar Borno
Rahotanni daga Jihar Borno sun ce mahara da ake kyautata zaton ƴan boko Haram ne sun shiga garin Askira inda suka shafe sa'o'i suna musayar wuta da jami'an tsaro.
Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa sun shiga garin ne da Magariba kuma har sun shiga asibitin garin da kuma ƙoƙarin kwace sansanin soji.
Haka kuma wasu rahotanni sun ce ƴan boko Haram sun kai hari garin Ngom na karamar hukumar Bama.
Asalin hoton, AFP
Gwamnan Legas ya kamu da korona
Gwamnantin Legas ta ce gwaji ya tabbatar da gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya kamu da cutar korona.
Gwamnatin jihar ta ce sakamakon gwajin da aka yi wa gwamnan ranar Juma'a ya tabbatar da yana ɗauke da cutar.
Tun da farko gwamnan ya killace kansa bayan ɗaya daga cikin jami'an ofishinsa gwaji ya tabbatar da yana ɗauke da cutar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce ta tura ƙarin jami’ai Kankara
Rundunar
ƴan sandan Najeriya ta ce babban Sufeton ƴan sandan ƙasar M.A Adamu ya bayar da umurnin tura ƙarin jami’ai
domin bincike da kuma kuɓutar da ɗaliban da aka sace a Kankara a jihar Katsina.
Sanarwar
da rundunar ta aika wa BBC ta ce jami’an sun haɗa da na rundunoni na musamman
masu leƙen asiri.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
A ranar Juma’a ne ƴan bindiga masu garkuwa da mutane suka shiga makarantar sakandare a Kankaka suka yi awon gaba da ɗalibai da dama.
Har yanzu ba a san adadin yawan ɗaliban da suka sace ba, amma rahotanni sun ce sun haura 600.
Rundunar ƴan sandan ta ce jami’an za su yi aiki da sojoji da ke farautar maharan da suka sace ɗaliban.
Sanarwar rundunar kuma ta ce an kashe ɗaya daga cikin maharan a artabun da jami’an tsaro yayin da kuma jami’inta ɗaya ya samu rauni.
Matasa 10 sun mutu a Najeriya a hanyar zuwa jarabawar shiga sojan sama
Rahotanni a Najeriya sun ce aƙalla matasa 10 ne suka mutu a kan hanyarsu ta
zuwa rubuta jarabawar shiga aikin sojan sama a Kano.
Bayanai sun ce sun mutu ne sakamakon taho mu gama da motar da suke ciki ta
yi da wata babbar mota a kusa da garin Ringim na jihar Jigawa.
Dukkanin matasan ƴan asalin jihar Jigawa ne daga ƙaramar hukumar Gagarawa
kuma sun gamu da ajalinsu ne a kan hanyar zuwa Kano.
Rundunar sojin Najeriya ta ce binciken ICC zai karya wa sojoji ƙwarin guiwa
Rundunar sojin Najeriya ta mayar
da martani kan binciken da Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC ta
ce za ta yi kan laifukan yaƙi da aka aikata a Najeriya.
A ranar Juma’a ne mai babbar mai
shigar da ƙara ta ICC Fatou Bensouda ta ce za ta yi bincike kan Boko Haram da
sojojin Najeriya kan cin zarafi da laifukan yaƙi da aka aikata a shekarun da
aka kwashe na rikicin Boko Haram.
Sai dai a sanarwar da wallafa a
shafinta na Facebook, rundunar sojin Najeriya ta ce wannan zai yi tasiri ga karya
ƙwarin guiwar sojoji.
“Babu shakka irin wannan bayani
na tunzurawa na iya janye hankalin sojojin Najeriya saboda tasirinsa na karye
masu ƙwarin guiwa. Zai haifar da mummunan tasiri ga ƙwarin guiwar da sojojin
suke da shi da kuma aikin soja ga ƴan Najeriya da haifar da koma-baya ga
dukkanin ayyukan tsaro a ƙasar.”
Sai dai sanarwa ta ce babban
hafsan sojin ƙasa na Najeriya Janar Tukur Buratai ya yi kira ga sojojin su yi
watsi da abin da ya kira abin da zai ɗauke hankalinsu tare da yin kira ga
sojojin kada su damu ko karaya da matakin.
Rundunar ta ce matakin ICC na
zuwa ne bayan rahoton da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International
ta fitar tana neman a gudanar da bincike kan “ta’asar da sojojin Najeriya suka
aikata.”
Fatou Bensouda ta ce ofishinta ya kammala nazari sannan ya gano wasu bayanai cewa ƙungiyar ta Boko Haram da sauran ɓangarorinta da suka ɓalle masu kaifin kishin Islama sun ci zarafin bil’adama.
Laifukan sun hada da kisa da fyaɗe da auren dole da kuma azabtarwa.
Bensouda ta kuma ce binciken da za ICC za ta gudanar ya shafi har da sojojin Najeriya da ƴan sanda.
EU Ta yi Allah wadai da zartarwa ɗan jarida hukuncin kisa a Iran
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Ruhollah Zam
Kungiyar Tarayyar Turai ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan
aiwatar da hukuncin kisa kan wani fitaccen dan jaridar adawa a Iran.
An rataye Ruhollah Zam a ranar Asabar bayan an same ta da laifin
tayar da rikici yayin zanga-zanga shekaru uku da suka gabata, da kuma hada kai
da kasashen waje don haifar da fitina a Iran - zargin da ya musanta.
A cewar wani dan
gwagwarmaya dan kasar Iran, ya yaudaru ne zuwa Iraki sannan kuma Sojojin Juyin
Juya Halin na Iran suka yi garkuwa da shi.
Amnesty International ta ce shari’ar an tursasa masa amince da laifin da ake tuhumar shi da aikatawa.
Nijar za ta rufe iyakokinta saboda zaɓen ƙananan hukumomi
Gwamnatin Nijar ta ce za ta rufe kan iyakokinta saboda zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a ranar Lahadi.
Ma'aikatar cikin gidan Nijar ta ce za a rufe iyakokin ne daga 12 dare na ranar Asabar zuwa 12 na ranar Lahadi bayan kammala kaɗa kuri'a.
A ranar 27 ga Disamba ne za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Nijar, karon farko da gwamnatin farar hula za ta gudanar da zaɓe tare da mika mulki ga wata gwamnatin farar hula.
An rufe makarantun kwana a Katsina
Asalin hoton, AMINUBELLOMASARIONTWITTER
Bayanan hoto, Aminu Bello Masari
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bada umarnin rufe makarantun kwana a jihar nan take.
Gwamnan ya bada umarnin ne cikin wata sanarwar daraktan watsa labaransa Abdu Labaran a ranar Asabar.
Matakin na zuwa ne bayan da ƴan bindiga suka sace wasu ɗalibai a makarantar sakandiren kwana ta Kankara da tsakar daren ranar Jumma'a.
Da yake magana yayin da yakai ziyara makarantar, gwamna Aminu Bello Masari ya ce ya ɗauki matakin ne domin kwantar da hankalin iyayen yara a jihar.
Ya ce tuni jami'an sojin Najeriya da ƴan sanda da kuma na tsaron farin kaya suka duƙufa don gano inda yaran suke.
PDP ta ce Buhari ya gaza bayan sace ɗalibai yana Katsina
Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta yi Allah wadai da harin da aka kai
wata makarantar Sakanfare ta Kankara a jihar Katsina inda aka sace ɗaliban
makarantar da dama.
A sanarwar da Jam’iyyar ta aika wa BBC ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu
Buhari ya yi bayani kan sace ɗaliban a matsayinsa na shugaban ƙasa kuma babban
kwamandan askarawan Najeriya, tana mai cewa harin ya faru sa’o’i bayan isa jiharsa ta Katsina.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Sai dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin ƴan bindigar a makarantar sakandaren Kankara.
Sanarwar da fadarsa ta fitar ta ce sojoji sun gano maɓuyar maharan a dajin Zango Paula a Kankara kuma sun yi musayar wuta da ɓarayin.
“Wannan ya ƙara nuna gazawar shugaba Buhari na aiki da bayanan tsaro wanda ya kamata yayin ziyarar bayan ƙin amsa gayyatar da majalisar ta yi masa ya tafi hutu, ƙasa kuma ta koma hannun ƴan ta’adda da ƴan fashi,” a cewar sanarwar PDP.
Har zuwa yanzu babu tabbacin adadin ɗaliban da suka ɓata bayan harin amma wasu rahotanni na cewa kusan 400 ne ba a gani ba bayan an lissafa waɗanda suke nan.
Wasu rahotanni sun ce adadin ya haura 600. Kuma sanarwar da fadar shugaban ta fitar ba ta bayyana adadin daliban ba.
Buhari ya yi Allah wadai da sace ɗalibai a Katsina
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da ƴan
bindiga suka kai a makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina inda rahotanni
suka ce sun yi awon gaba da dalibai da dama.
Sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce, shugaban ya buƙaci
rundunar soji da ƴan sanda su shiga farautar maharan tare da tabbatar da babu
abin da ya samu ɗaliban da aka sace.
Har zuwa yanzu babu
tabbacin adadin ɗaliban da suka ɓata bayan harin amma wasu rahotanni na cewa
kusan 400 ne ba a gani ba bayan an lissafa waɗanda suke nan.
Wasu rahotanni sun ce
adadin ya haura 600. Kuma sanarwar da fadar shugaban ta fitar ba ta bayyana
adadin daliban ba
Shugaban kuma ya buƙaci hukumar makarantar da iyaye ta gudanar da bincike
kan yawan ɗaliban makarantar, bayan harbin bindiga da ya sa ɗaruruwansu suka
shiga daji.
Ya kuma jajantawa iyayen ɗaliban da shugabannin makarantar tare da yi masu addu’a.
Sanarwar ta kuma ce sojoji sun gano maɓuyar maharan a dajin Zango Paula a
Kankara kuma sun yi musayar wuta da ɓararin.
Shugaban kuma ya bayar da umurnin tsaurara tsaro a dukkanin makarantu na
Najeriya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Ma'aikatan agaji da ISWAP ta sace ango ne da abokinsa
Asalin hoton, Red Cross
Wasu masu iƙirarin jihadi sun sace wani ango da babban abokinsa a Jihar Borno yayin da suke komawa birnin Maiduguri daga wurin ɗaurin aure, a cewar rahoton AFP.
An kama angon wanda ke aiki da hukumar samar da abinci ta MDD World Food Programme (WFP) da kuma abokin nasa mai aiki da ƙungiyar agaji ta Red Cross, a Jakana ranar Laraba, 28 ga Nuwamba.
"'Yan ta'addan ISWAP sun kama masu aikin agaji biyu a wani wurin duba ababen hawa da suka saka a kusa da Jakana," kamar yadda wata majiya ta shaida wa AFP.
Angwayen na komawa Maiduguri ne daga Jihar Adamawa bayan ɗura auren a loƙacin da aka tare su a wani wurin duba ababen hawa na bogi da misalin ƙarfe 1:30 na rana, a cewar majiyar.
Ƙungiyar ISWAP wadda ta ɓalle daga Boko Haram a 2016 ta ce ita ta sace mutanen cikin wata sanarwa da fitar ranar Juma'a.
Sirrin nasarar Jelani Aliyu a harkar zanen motoci
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari cikakakkiyar hira da Jelani Aliyu
Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya karɓi baƙuncin Jelani Aliyu, shugaban ma'aikatar zana motoci ta Najeriya.
Jelani ya shafe da dama a Amurka kafin ya koma Najeriya domin karɓar shugabancin ma'aikatar.
Cikin tattaunawar da Jabir Mustafa Sambo ya jagoranta, Jelani Aliyu ɗan asalin Jihar Sokoto ya bayyana abubuwan da ya saka a gaba bayan komawarsa gida da kuma irin abin da ma'aikatar tasa take yi a yanzu.
Yadda za a kawo ƙarshen tsadar albasa a Najeriya
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari bayanin shugaban ƙungiyar manoman albasa a Najeriya
Manoama da `yan kasuwar albasar sun bayyana cewa `yan kungiyarsu sun yi asara mai yawa, a lokacin rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar EndSARS, lamarin da ya shafi noman ta.
Ana amfani da albasa a matsayin kayan hadin abinci daban-daban a kowane lungu da saƙo na Najeriya.
Sai dai wani ƙalubale da ake fuskanta shi ne yadda albasar ke tsada
sosai a kasuwa sakamakon ƙarancin da ta yi.
Alhaji Aliyu
Maitasamu Isa, shi ne shugaban ƙungiyar manoma da `yan kasuwar albasa ta
Najeriya, kuma ya shaida wa BBC cewa za a daɗe ana fsukantar ƙarancin albasar idan ba su samu taimako ta fuskar jari da hanyoyin adana ta
ba.
Matasa 10 sun mutu a Jigawa sakamakon hatsarin mota
Asalin hoton, @FRSCNigeria
Matasa 10 sun rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da su a garin Ringim na Jihar Jigawa.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na asubahin yau Asabar yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Kano domin halartar jarrabawar shiga aikin soja.
Wani wanda yake cikikin tawagar matafiyan ya shaida wa BBC cewa an yi jana'izar mutum 10 a garin Gagarawa na Jihar Jigawa sannan wasu biyu na kwance a asibiti sakamakon raunukan da suka ji.
Nafi'u Gagarawa ya ce dukkaninsu matasa ne, inda mutum ɗaya ne a cikinsu ke da aure.
Wannan labari maras daɗi na zuwa ne kwana kaɗan bayan wasu 16 'yan Ƙaramar Hukumar Ɗambatta ta Kano sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kano.
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram guda tara
Asalin hoton, @DefenceInfoNG
Hedikwatar tsaro ta sojojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan ƙungiyar Boko Haram guda tara cikin kwana biyu tare da jikkata wasu da dama.
Wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na zumunta, cibiyar tsaron ta ce dakarunta na rundunar Operation Lafiya Dole sun yi nasarar kashe mayaƙa huɗu a kan titin Banki da ke Jihar Borno ranar Talata, 8 ga Disamba.
Sanawar ta ƙara da cewa dakarun sun kuma kashe wasu 'yan ƙungiyar guda uku ranar Talatar a kan titin Firgi-Pulka, inda aka jikkata wasu da dama.
Kazalika, an kashe ɗan Boko Haram ɗaya ranar Litinin a garin Mogoniri bayan rahotannin sirri da sojojin suka samu.
Haka nan an kashe wani mayaƙin a Gonori da ke kusa da Dajin Sambisa a Litinin ɗin.
Sai dai rundunar ba ta ce komai ba game da kisan dakarunta 10 da rahotanni suka ambato an yi ranar Litinin da ta gabata.
Ƙungiyar ISWAP da ta ɓalle daga Boko Haram a 2016 ta ce ita ta kashe sojojin guda bakwai bayan sun kai wa wani sansaninta hari tare da ƙwace motocin yaƙi. Sai dai kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito majiyar soja na cewa sojoji 10 ne suka mutu yayin fafatawar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Ana ci gaba da jimamin mutuwar mai jaridar Leadership
Ana ci gaba da jimamin rasuwar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jami'yyar APC kuma mawallafin jaridar Leadership a Najeriya, Sam Nda-Isaiah.
Shuagaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya bayyana mutuwar marigayin a matsayin "abin tsoratarwa", yana mai miƙa ta'aziyyarsa ga ƙungiyar masu gidajen jarida ta Najeriya.
Shi ma Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna ya ce mutuwar Sam "abar ɓacin rai ce kuma Kaduna ta yi rashin mutum na musamman".
Tun farko Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Nda-Isaiah a matsayin aboki kuma na hannun damansa na siyasa.
Sam Nda-Isaiah ya rasu a daren Juma'a yana da shekara 58 bayan gajeriyar rashin lafiya.
Shi ne ya kafa kamfanin Leadership Group wanda ke buga jaridar Leadership cikin Ingilishi da kuma Hausa a shekarar 2001.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
An yanke wa ɗan jarida hukuncin kisa a Iran
Asalin hoton, Reuters
Rahotanni daga Iran na cewa an yanke wa ɗan jaridan nan Ruhollah Zam hukuncin kisa.
Ruholla Zam shahararren ɗan jarida ne da ke gabatar da shirye-shirye a kafar sada zumunta ta Telegram.
A shekarar 2017 ne aka zarge shi da haddasa husuma a lokacin zanga zangar kin jinin gwamnati.
Mista Zam ya gudu zuwa Faransa kafin daga baya jami'an tsaron Iran su cafke shi a Iraƙi suka kuma tasa keyarsa zuwa gida.
Nasir El-Rufai ya sake killace kansa saboda korona
Asalin hoton, @GovKaduna
Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya killace kansa a karo na biyu sakamakon annobar cutar korona.
Matakin ya biyo bayan gwajin da ya nuna cewa wani daga cikin iyalan gidansa da kuma manyan muƙarraban gwamnatinsa sun kamu da cutar a jiya Juma'a.
Cikin wani bidiyo da gwamnatin jihar ta wallafa a shafukan zumunta, Gwamna El-Rufai ya ce ya yi hakan ne a matsayin riga-kafi kafin a yi masa gwaji gobe Lahadi.
Shi ma Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya killace kansa bayan wasu hadimansa sun kamu da cutar a jiyan.
"Na killace kaina ne bisa tsarin yaƙi da cutar korona kuma ina fatan a yi mani gwaji ranar Lahadi," in ji Gwamna El-Rufai cikin sanyayyar murya.
"Ya ku jama'ar Kaduna, na samu rahoton cewa ƙarin mutane sun kamu da cutar korona a yau [Juma'a] ciki har da iyalan gidana da kuma manyan jami'an gwamnati, saboda haka na killace kaina."
Gwamna El-Rufai ya fara killace kansa ne ranar 28 ga watan Maris bayan ya sanar da cewa ya kamu da cutar korona.
Sauran manyan mutane da suka harbu da cutar a Najeriya sun haɗa da:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Za a fara yi wa Amurkawa riga-kafin cutar korona
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka ta amince da amfani da riga-kafin kamfanin samar da magani na Pfizer domin amfanin gaggawa wurin yaƙar annobar korona.
Wakilin BBC ya ce matakin na nufin za a fara yi wa masu shekaru 60 zuwa sama.
Shugaba Donald Trump ya ce za a raba riga-kafin ga Amurkawa kyauta kuma ba tare da ɓata lokaci ba.
Ya ce abin jinjina ne a ce an samar da irin wannan riga-kafi mai muhimmanci a cikin wata tara.
Ssai dai babban ƙalubalen a yanzu shi ne yadda za a raba shi ga jihohin kasar 50 lura da kiyaye ka'idojin ajiyewa tare da raba rigakafin.
Cutar ta korona ta kashe fiye da mutum 290,000 a Amurka.