Yariman Saudiyya ya musanta zargin tura makasa zuwa Canada

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. An dakatar da kamfanonin waya sayar da sabbin layuka a Najeriya

    Kamfanin MTN

    Asalin hoton, MTN

    Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya Nigerian Communications Commission (NCC), ta bai wa kamfanonin sadarwa umarnin dakatar da sayar da sabbin layukan wayar salula a ƙasar.

    Cikin wata wasiƙa da ta aike wa kamfanonin ranar Litinin wadda kuma jaridar TheCable ta gani, hukumar ta ce ta duƙufa ne kan duba rumbun bayanan rajistar masu layukan, kuma umarnin zai ci gaba da aiki har sai an kammala.

    "Bisa umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na tabbatar da an bi tsarin yi wa layuka rajista, hukumar ta duƙufa kan tantance rajistar masu layuka domin ta tabbatar da an bi umarnin sannan ta daidaita ayyuka," a cewar wasiƙar da daraktan ayyuka na NCC, A.I. Sholanke, ya sanya wa hannu.

    "Saboda haka, an umarce ku da ku dakatar da sayarwa da kuma ƙaddamar da sabbin layukan kamfaninku har zuwa sanda za a kammala binciken.

    "Sai dai kuma idan ya zama dole, za a iya bayar da umarni na musamman idan an samu amincewar gwamnatin tarayya ta hannun hukumar NCC."

    Wasiƙar ta kuma gargaɗi kamfanonin cewa idan suka ƙi bin umarnin "za a iya ƙwace lasisin gudanar da ayyukansu".

    Daraktan hulɗa da jama'a na NCC, Ikechukwu Adinde, ya faɗa a yau Laraba cewa matakin ya zama dole saboda "yadda layuka marasa rajista suka karaɗe gari, waɗanda ake amfani da su wurin aikata mugayen laifuka".

  2. El-Rufai ya saka hannu kan kasafin kuɗin 2021

    Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya saka hannu kan kasafin kuɗi na shekarar 2021.

    El-Rufai ya saka hannun ne a yau Laraba yayin wani taƙaitaccen biki a fadar gwamnatin jihar.

    Gwamnan ya ce an ware kashi 66 cikin 100 na jumillar biliyan 257 domin manyan ayyuka, waɗanda za su tallafa wa harkokin lafiya da ilimi da ayyukan raya ƙasa da kuma noma.

    Yayin da yake jawabi a majalisa lokacin da ya gabatar da kasafin, El-Rufai ya ce gwamnatinsa za ta ƙara ƙoƙari wurin tattara kuɗin haraji a jihar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Hatsarin jirgin sama ya kashe mutum biyar a Faransa

    Jirgin helikwafta

    Asalin hoton, EPA

    Wani jirgin helikwafta ya yi hatsari a Faransa, inda ya kashe fasinja biyar cikin shida da ke cikinsa, a cewar hukumomi.

    Jirgin mallakar wani kamfani, yana kan aikin ceto ne a lokacin da ya faɗo a kusa da garin Bonvillard da ke yankin Savoie.

    Ba a san musabbabin hatsarin ba zuwa yanzu, amma hukumomi sun ce akwai yiwuwar rashin kyawun yanayi ne ya haddasa.

    Matuƙin jirgin ne ya fara sanar da halin da suke ciki, wanda ya tsallake rijiya da baya da mugayen raunuka.

    Kamfanin Service Aérien Français ne ya mallaki jirgin, wanda ke gudanar da aikin ceto da kuma sauran ayyuka a Faransa.

    Cikin wani saƙon Twitter, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nuna "alhininsa da na al'ummar ƙasar ga iyalan mamatan da abokansu a matsayinsu na gwarazan Faransa".

  4. An sace ɗan majalisar Jihar Taraba

    Ɗan sanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da Barista Bashir Mohammed, ɗan majalisa mai wakiltar Nguroje a Majalisar Dokokin Jihar Taraba.

    A cewar wani ɗan uwan ɗan majalisar, wanda shi ne shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisa, an ɗauke shi ne a gidansa da ke kusa da Filin Idi na Dr Jalo a garin Jalingo da misalin ƙarfe 1:45 na dare, a cewar rahoton Channels TV.

    Mutumin ya bayyana cewa babu alamun jami'an tsaro a lokacin da 'yan bindigar suka je tafiya da shi, wanda aka yi kusan awa uku ana artabu.

    Ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoton, rundunar 'yan sandan jihar ba ta ce komai ba game da lamarin.

  5. Zaɓen Ghana: An bayyana sakamakon yanki 7 cikin 16 na zaɓen shugaban ƙasa

    Ghana

    Asalin hoton, Getty Images

    Ya zuwa yanzu hukumar zaɓen ƙasar Ghana ta bayyana sakamkaon zaɓen shugaban ƙasa na yanki bakwai daga cikin 16.

    Daga cikin waɗanda aka bayyana, tsohon Shugaba John Mahama na jam'iyyar NDC ke kan gaba da ƙuri'a 1,997,450.

    Shi kuma Shugaba Nana Akufo-Addo na jam'iyya mai mulki ta NPP na da ƙuri'a 1,500,310.

    Yankunan da aka bayyana:

    • Upper West: NPP: 121,230 - NDC: 238,972
    • North East: NPP: 122,742 - NDC:112,306
    • Bono East: NPP: 292, 604 - NDC: 203,329
    • Oti: NPP: 103,865 - NDC: 181,021
    • Volta: NPP: 100,481 - NDC: 606,508
    • Ahafo: NPP: 145,584 - NDC: 116,485
    • Central: NPP: 613,804 - NDC: 538,829
  6. An dakatar da wasan PSG saboda kalaman wariyar launin fata

    PSG da Istanbul Basaksehir

    Asalin hoton, Getty Images

    An dakatar da wasan PSG da Istanbul Basaksehir ana tsaka da wasa sakamakon kalaman wariyar launin da ake zargin mataimakin alƙalin wasa da yi.

    Ƴan wasan ƙungiyoyin biyu sun tsayar da wasan da suke bugawa na a gasar Zakarun Turai ta Champions League a daren jiya Talata a Faransa daƙiƙa 14 kacal da take wasan.

    Jim kaɗan bayan tsayar da wasan ne kuma ƴan wasan suka fice daga fili.

    Basaksehir ta zargi ɗaya daga cikin alƙalan wasan ɗan ƙasar Romania da ambatar kalmar nuna ƙyama a lokacin da suke sa'in'sa da mataimakin kocinsu, Pierre Webo, tsohon ɗan wasan Kamaru.

    Yanzu za a buga wasan da sabbin alkalai domin wajen ƙarasa shi, wanda ake sa ran a soma buga shi daidai lokacin da aka tsayar.

    Hukumomin ƙwallon kafa kuma na binciken wannan zargi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Najeriya: Mutum 550 sun kamu da korona, ɗaya ya mutu

    Korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 550 da suka kamu da cutar korona a ranar Talata.

    Kazalika, ƙarin mutum ɗaya ya mutu, abin da ya kawo adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar zuwa 1.182 a kasar.

    A saƙon da ta wallafa a shafinta na intanet, NCDC ta ce an samu sabbin kamuwar ne a jiha 17 da suka haɗa da Legas (219) da Abuja(168) Kaduna (52) da Kwara (19) sai Kano da Rivers masu mutum (15) da suka kamu a kowacce jiha.

    Jihar Sokoto na mutum (10) da Enugu (9) da Gombe (8), sai Plateau da Osun masu mutum 7-7, Anambra da Oyo mutum 5-5.

    Jigawa da Ogun na da mutum 4-4 da suka kamu a kowacce jiha, sai Bauchi mutum 2 da kuma Edo mai mutum guda.

  8. Kun shigo shafin labarai kai-tsaye

    Barkanmu da sake haɗuwa a hantsin Laraba - ta bawa ranar samu - da fatan kun tashi lafiya.

    Umar Mikail ne zai kawo muku labaran a wannan safiya daga Ghana da Najeriya da Nijar da maƙwabtansu, har ma da sauran sassan duniya.