Yariman Saudiyya ya musanta zargin tura makasa zuwa Canada

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan labaran da muka wallafa ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. Yadda ake murnar nasarar Shugaba Nana Akufo-Addo a Ghana

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  3. Kotun ICC na zargin sojojin Birtaniya da aikata laifukan yaƙi a Iraƙi

    Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke Hague ta ce tana da dalilan da za su sa ta yadda cewa sojojin Birtaniya sun aikata laifukan yaki a Iraƙi.

    Amma kotun ta ICC ta ce a yanzu, ba ta da burin ɗaukar mataki kan Birtaniyar saboda ba ta samu isassun hujjojin cewa gwmanatin Birtaniyar ta ɗauki matakin don kare sojojinta daga gurfana ba.

    Rahoton ICC na tsawon shekara tara ya kare a 2011 lokacin da kotun ta yi imanin cewa an aikata laifuka kan fursunonin Iraƙi da ke tsare a hannun Birtaniya.

    Laifukan da ake zargi sun haɗa da kisa ba bisa ƙa'ida ba da azabtarwa da kuma fyaɗe.

  4. Rasha na shirin kafa sansanin sojin ruwa a Khartoum

    ..

    Asalin hoton, AFP

    An fara samun bayanai da ke nuna cewa akwai wata yarjejeniya tsakanin Sudan da Rasha domin Rashar ta kafa sansanin sojin ruwa a gabar tekun maliya a Khartoum.

    Yarjejeniyar, wadda aka saka wa hannu a makon da ya gabata, za ta ba Rasha damar ajiye manyan jiragen ruwa huɗu a tashar jirgin Sudan, ciki har da jirgi mai amfani da makamashin nukilya na tsawon shekara 25.

    Masu sharhi na ganin cewa wannan wani yunƙuri ne na Rasha domin ta ƙara ƙarfin ƙasarta.

    A 2017, a ziyararsa ta farko zuwa Rasha, Tsohon Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya buƙaci Vladimir Putin ya kare ƙasarsa daga matsin lambar Amurka.

    Tuni dai aka hamɓarar da gwamnatin Mista Bashir inda yanzu haka ake tsare da shi a gidan yarin Khartoum.

  5. Majalisar Dokokin Faransa ta amince da wata doka kan masu tsatsauran ra'ayin addini

    Majalisar ministocin Faransa ta amince da wani kudirin doka da ya shafi masu tsatsauran ra'ayin Islama bayan wasu hare-hare da ake zargin masu kaifin kishin addini ne suka kai.

    Dokar da aka yi wa laƙabi da dokar yanci ta tsaurara dokoki kan koyarwa a gida da kuma yaɗa kalaman ƙiyayya ta intanet, martani ne ga kisan malamin nan Samuel Party, da ya nuna wa ɗalibansa zanen barkwanci na Annabi Muhammad SAW.

    Shugaba Macron ya daɗe da shirya samar da waɗannan sauye-sauyen kuma ana ta matsa lamba kan ya ɗauki mataki.

    Firaminista Jean Castex, ya shaida wa manema labarai cewa dokar na neman 'yantar da Musulmi daga mummunan halin da ake fuskanta na masu tsatsauran ra'ayin Islama.

    Sai dai za a miƙa kudirin dokar ga majalisar dokokin ƙasar domin amincewa.

  6. Labarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Yamma - 09/12/2020

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren labaran
  7. Iran ta kama wasu da take zargin da hannunsu a kisan ƙwararre kan makamin nukiliyarta

    Mohsen Fakhrizadeh

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, An kashe Mohsen Fakhrizadeh ne a ranar 27 ga watan jiya a birnin Tehran

    Hukumomi a Iran sun sanar da cafke wasu daga cikin waɗanda ke da hannu a kisan ƙwararre kan makamin nukiliyar kasar.

    Mai bai wa majalisa shawara Hossein Amir Abdollahian ya shaida wa gidan talabijin ɗin kasar Al-Alam ba zai bayyana sunayen mutanen ba saboda dalilai na tsaro, sai dai za a hukunta waɗanda aka samu da laifi.

    Abdollahian ya kara da cewa akwai shaidun da ke nuna akwai hannun Isra’ila a kan lamarin, sai dai kawo yanzu Isra’ilar ba ta uffan ba kan zargin.

    An kashe Mohsen Fakhrizadeh ne a ranar 27 ga watan jiya a birnin Tehran.

  8. Nana Akufo ya doke John Dramani a zaɓen Ghana

    ..

    Hukumar zaɓen Ghana ta sake tabbatar da shugaban ƙasar, Nana Akufo-Addo a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.

    Shugaba Addo ya kayar da babban abokin hamayyarsa John Dramani Mahama, wanda shi ne tsohon shugaban ƙasar.

  9. Yariman Saudiyya ya musanta zargin tura makasa zuwa Canada

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya yi watsi da duka zarge-zargen da ake yi masa na tura tawagar masu kashe mutane zuwa Canada domin kashe tsohon jami'in ƙasar na tattara bayanan sirri da aka tilasta wa gudun hijira.

    A wata ƙara da aka kai a wata kotun Amurka, Saad al-Jabri ya yi iƙirarin cewa an yi ƙoƙarin kashe shi a Canada, inda ya gudu shekara uku da suka gabata.

    Ya bayyana cewa Mohammed bin Salman na so ya kashe shi sakamakon ya san abubuwa da dama.

    Yarima mai jiran gadon ya bayyana cewa Mista Jabri na ƙoƙarin lulluɓe laifukansa ne kawai.

  10. Nana Akufo-Addo na daf da lashe zaɓen Ghana

    ..
  11. Manoma a Indiya sun yi fatali da shawarwarin gwamnati kan sauye-sauyen aikin gona

    Shugabannin manoma a Indiya, sun yi fatali da shawarwarin gwamnati na kawo ƙarshen taƙaddama kan sauye-sauyen aikin gona.

    Gwamnati ta aike wa ƙungiyoyin manoma wasu shawarwari ƙunshe cikin shafuka 20 a ƙoƙarin kawo ƙarshen zanga-zangar da suke gudanarwa, amma manoman sun yi watsi da shawarwarin.

    Manoman sun ce ba sa buƙatar komai sai neman janye dokokin baki ɗaya.

    Dubban jama'a ne a sassan India suka shiga zanga-zangar domin nuna goyon bayansu ga manoman amma gwamnatin ta ce dokar za ta amfani manoman.

    Manoman dai za su ci gaba da gudanar da zanga-zangar a sassan ƙasar tare da rufe titunan da suka kai ga Delhi babban birnin ƙasar.

  12. Shugaba Nana Akufo-Addo na ci gaba da ba John Dramani tazara

    ..
  13. Magoya bayan John Mahama sun fara zanga-zanga

    Bayanan bidiyo, Yadda magoya bayan John Mahama ke zanga-zanga

    Magoya bayan John Dramani Mahama na NDC na zanga-zanga a gaban ofishin hukumar zabe inda suke neman a tabbatar masa da nasarar da ya samu a zaben.

    Suna wannan zanga-zanga tun kafin hukumar zaɓe ta gama tattara bayanai ko sanar da sakamakon zaɓen.

  14. Nijar: Hukumar yaƙi da rashawa ta sha alwashin tsaftace zaɓen ƙasar

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton Tchima Illa Issoufou daga Yamai

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Jamhuriyar Nijar, HALCIA ta ce za ta shiga cikin harkokin babban zaɓen ƙasar da za a gudanar ranar 27 ga watan Disambar nan.

    Maƙasudin yin hakan shi ne kawo ƙarshen cin hanci a al'amuran zaɓe, a cewarta.

    Ta bayyana aniyarta ne yayin biikin ranar yaƙi da cin hanci da rashawa ta duniya, wadda ake gudanarwa duk ranar 9 ga watan Disamban kowace shekara.

    Ta ƙara da cewa ta samu ƙwarin gwiwar ɗaukar wannan mataki ne biyo bayan binciken da ƙungiyar Transparency Interantional ta yi, wanda ya gano yadda ake tafka cin hanci da rashawa yayin yaƙin neman zaɓe a ƙasar.

  15. Zaɓen Ghana: Shugaba Nana Akuffo-Ado ne kan gaba

    Ya zuwa yanzu an sanar da sakamako na yanki 11 cikin 16.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Buhari ya rantsar da Mahmood Yakubu shugaban INEC a karo na biyu

    Farfesa Mahmood Yakubu

    Asalin hoton, NG Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban hukumar zaɓe ta INEC a karo na biyu.

    An yi rantsuwar ce a gurguje kafin fara zaman Majalisar Zaratarwa na 27 ƙarƙashin jagorancin Shugaba Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock Villa a yau Laraba.

    Farfesa Yakubu ya zama shugaban hukumar na farko da aka sake naɗa shi kuma zai jagorance ta tsawon shekara biyar masu zuwa.

    "Mun nuna ƙarara a zaɓukan baya-bayan nan cewa zaɓukan na ƙara kyautatuwa kuma za su ci gaba da kyautatuwa," in ji Farfesa Yakubu jim kaɗan bayan rantsar da shi.

    Ana sa ran wa'adinsa na biyu zai fara aiki ne daga yammacin Laraba, 9 ga watan Disamban 2020. Tun a ranar 9 ga Nuwamba ya sauka daga muƙamin bayan wa'adinsa na farko ya ƙare, inda wani kwamishinan hukumar ya karɓi jagoranci.

    Buhari ya fara naɗa Mahmood Yakubu a Oktoban 2015 kuma shi ne ya jagoranci gudanar da babban zaɓe na 2019.

    Bisa al'ada, taron Majalisar Zartarwa wanda ake gudanarwa duk Laraba, yana samun halartar dukkanin ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati.

    A gobe Alhamis ne ake sa ran Buhari zai bayyana a gaban 'yan Majalisar Wakilan Najeriya domin yi musu bayani game da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar, musamman a Arewa.

    Sai dai a jiya Talata shugaban ya ce suna bakin ƙoƙarinsu wurin samar wa sojoji makaman da suke buƙata na yaƙi da 'yan fashin daji da kuma ƙungiyar 'yan bindiga ta Boko Haram.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Labarai cikin minti ɗaya

    Bayanan sautiMinti Ɗaya Da BBC Na Rana 09/12/2020
    • Ƙasashe masu arziki na ɓoye riga-kafin cutar korona, yayin da mutanen da ke ƙasashe matalauta za su iya rasawa, kamar yadda gamayyar masu fafutuka suka yi gargaɗi. Gamayyar ƙungiyoyi ta The People's Vaccine Alliance ta ce a kusan ƙasashe 70 marasa ƙarfi mutum ɗaya cikin 10 ne kawai za su iya yi wa riga-kafi.
    • Sakamakon da hukumar zaɓen Ghana da ta fitar ya zuwa yanzu ya nuna cewa tsohon shugaban ƙasar John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC ne yake kan gaba inda ya samu ƙuri'a 1,997,450. Kawo yanzu hukumar ta fitar da sakamakon zaɓen larduna bakwai daga cikin 16 da ake da su a faɗin ƙasar Ghana, wanda ya nua cewa shugaba mai-ci Nana Akufo-Addo na jam'iyyar NPP ya samu ƙuri'a 1,500,310.
    • Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya Nigerian Communications Commission (NCC), ta bai wa kamfanonin sadarwa umarnin dakatar da sayar da sabbin layukan wayar salula a ƙasar. Cikin wata wasiƙa da ta aike wa kamfanonin, hukumar ta ce ta duƙufa ne kan duba rumbun bayanan rajistar masu layukan, kuma umarnin zai ci gaba da aiki har sai an kammala.
    • An dakatar da wasan PSG da Istanbul Basaksehir ana tsaka da wasa sakamakon kalaman wariyar launin fata da ake zargin mataimakin alƙalin wasa da yi. Ƴan wasan ƙungiyoyin biyu sun tsayar da wasan da suke bugawa a gasar Zakarun Turai ta Champions League a daren jiya Talata a Faransa daƙiƙa 14 kacal da take wasan.
  18. Kotu ta kori ƙarar Trump kan sakamakon Jihar Pennsylvania

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da ƙarar da tawagar kamfe ɗin Donald Trump ta shigar gabanta ta neman rushe sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na Jihar Pennsylvania.

    Kotun ta yi watsi da buƙatar neman rushe kuri'u fiye da miliyan biyu da rabi da aka kada ta gidan waya, ba tare da bayyana hujoji ba.

    Wakilin BBC ya ce shari'ar ta kasance ta baya-bayanan cikin jerin gwamman ƙararraki da ofishin kamfe ɗin na Trump ke rashin nasara a kotu.

    Kafin wannan lokaci, Jihar Texas ta buƙaci Kotun Ƙolin ta soke sakamakon zaɓukan wasu jiha huɗu, a shari'ar da masu sharhi ke ganin da wuya a kai labari.

  19. An kashe sojojin Najeriya 10 a Jihar Borno

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Aƙalla sojojin Najeriya 10 ne suka mutu yayin wani artabu da mayaƙan ƙungiyar da ke da alaƙa da IS a Alagarno da ke Jihar Borno, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kai hare-hare guda uku a kan dakarun na Najeriya cikin wata sanarwa a jiya Talata, inda ta ce ta kashe sojoji bakwai ranar Litinin tare da kama wani guda ɗaya.

    Wasu majiyoyin tsaro sun faɗa wa AFP cewa sojoji 10 ne suka mutu bayan dakarun Najeriyar sun kai wa sansanin ƙungiyar ISWAP hari ranar Litinin a Alagarno.

    "Mun rasa soja 10 a faɗan kuma 'yan ta'adda sun ɗauke ɗaya," in ji majiyar. An kama sojan ne yayin da yake neman tsira sakamakon ruwan wutar da 'yan bindigar suka yi musu, a cewarsa.

    "An fafata sosai kuma an kashe 'yan bindigar su ma, amma duk da haka sun rinjayi sojojin," a cewar majiya ta biyu.

    Mayaƙan ƙungiyar sun ƙwace mota huɗu da suka haɗa da motar silke da kuma na zirga-zirga.

    Ƙungiyar ta wallafa wasu hotuna tana iƙirarin cewa sojan da ta kama ne da gawarwakin waɗanda ta kashe da kuma motocin da ta ƙwata daga hannunsu.

    A cewar ƙungiyar, cikin ɗaya daga hare-haren da ta kai, ta yi wa sojoji kwanton-ɓauna a kan titin Gamboru zuwa Dikwa, inda ta kashe soja huɗu.

    Garin Alagarno mai nisan kilomita 150 daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, ya kasance matattarar ƙungiyar ISWAP, wadda ta ɓalle daga Boko Haram a 2016 kuma take cin gashin kanta.

    Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 36,000 a yankin arewa maso gashin Najeriya, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

  20. Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa

    Buhari

    Asalin hoton, NG Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa a Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock Villa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

    Yayin taron, Buhari ya rantsar da Farfesa Mahmud Yakubu a matsayin shugaban hukumar zaɓe ta INEC a karo na biyu.

    Bisa al'ada, taron wanda ake gudanarwa duk Laraba, yana samun halartar dukkanin ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati.

    A gobe Alhamis ne ake sa ran Buhari zai bayyana a gaban 'yan Majalisar Wakilan Najeriya domin yi musu bayani game da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar, musamman a Arewa.

    Sai dai a jiya Talata shugaban ya ce suna bakin ƙoƙarinsu wurin samar wa sojoji makaman da suke buƙata na yaƙi da 'yan fashin daji da kuma ƙungiyar 'yan bindiga ta Boko Haram.

    Bayan kammala taron ne majalisar za ta yi wa 'yan jarida bayanin mahimman abubuwan da suka tattauna game da ayyukan cigaban ƙasa da kuma sauran matakai.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X