Rufewa
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Jami'an hukumar lafiya a Birtaniya sun ce an yi wa dubban mutane rigakafin cutar korona a rana ta farko da aka fara shirin rigakafin.
Birtaniya ce ƙasa ta farko a faɗin duniya da ta fara amfani da allurar rigakafin kamfanin Pfizer da BioNTech da aka yi wa cikakken gwaji.
Wata tsohuwa yar shekra 90 ce ta farko da aka yi wa rigakafin wadda kamfanonin suka ce tana da inganci.
Gwamnatin Burtaniyar ta yi odar alluran rigakafin miliyan arba'in a kashin farko na shirin.
Birtaniya ce ƙasar da wannan annoba ta fi kisa inda sama da mutum dubu sittin da ɗaya suka mutu.

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa Najeriya ta garƙame iyakokinta, inda ya ce an yi haka ne a yunƙurin ƙasar na daƙile fasa ƙwaurin makamai da miyagun ƙwayoyin da ake yi cikin ƙasar.
A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan kafofin yaɗa labarai Garba Shehu ya fitar, ya bayyana cewa nan gaba kaɗan za a buɗe iyakokin sakamakon makwaftan ƙasar sun fahimci dalilin da ya sa ƙasar ta rufe iyakokin.
A yau ne shugaban ƙasar ya tattauna da gwamnoni 36 na ƙasar inda aka fi mayar da hankali kan muhimman abubuwan da ke damun ƙasar a halin yanzu, kamar yadda sanarwar ta nuna.
Shugaban ya kuma yi kira ga gwamnonin ƙasar da su yi aiki hannu da hannu da sarakunan gargajiya domin samun bayanan sirri.
Kan batun dai na tsaro, shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi ƙoƙari a arewa maso gabas da kudu maso kudancin ƙasar, sai dai ya ce har yanzu abin da ke faruwa a kudu maso kudancin ƙasar na damunsa.
"A kullum ina samun rahoton matatun mai da aka kafa ba bisa ƙa'ida ba da kuma fasa bututun mai, dole a hana ɓata garin nan lalata kayayyakin mai da aka saka," in ji shugaban.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu zakuna huɗu da ke Gidan Zoo na Barcelona sun kamu da cutar korona, kamar yadda jami'an lafiyar dabbobi na birnin suka bayyana.
Tun da farko dai, zakunan sun fara nuna alamomin cutar ne, wanda hakan ya ja aka yi musu gwaji aka gano suna ɗauke da cutar.
Haka kuma an tabbatar da cewa ma'aikatan gidan zoo ɗin har mutum biyu sun kamu da cutar.
A yanzu dai an ƙaddamar da bincike kan yadda dabbobin suka kamu da cutar, sai dai ana tunanin sun haɗu da wani jam'in gidan zoo ɗin mai ɗauke da cutar amma ba alamomin a tattare da shi.

Asalin hoton, Alamy
Jami'ar Amurka ta East Carolina, ta nuna takaicinta kan yaudarar da aka yi wa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wurin amfani da sunanta domin ba shi muƙamin Farfesa.
A wata sanarwa da mataimakin shugaban jami'ar kan harkokin ɗalibai ya fitar, jami'ar ta bayyana rashin jin daɗinta kan ko amsar da ta bayar a farko ta jawo wa gwamnan abin kunya, inda ta ce ba da niyyar hakan ta aika wasiƙar farkon ba.
Wannan wasiƙar dai amsa ce kan ƙorafin da Gandujen ya aika wa jami'ar inda ya buƙaci ta ba shi haƙuri da kuma hukunta malamin jami'ar da ya aika wasiƙar.
Tun da farko sakataren watsa labarai na jihar Kano, Abba Anwar ne ya fitar da wata sanarwa da ke cewa Jami'ar East Carolina a Amurka ta ba Ganduje matsayin Farfesa sakamakon abin da ta kira "ƙwarewarsa wurin gudanar da mulki na gari da kuma inganta rayuwar al'umma".
Sai dai daga baya jami'ar ta fitar da wata sanarwa da ta nisantar da kanta daga wannan lamari, abin da ya fusata Gwamna Ganduje.

Asalin hoton, ecu
Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce ƙwace jirgin ruwan kasar da mayaƙa masu biyayya ga jagoran ƴan tawayen Libya Janar Khalifa Haftar yana tafe da abin da ta kira mummunan sakamako.
An bar jirgin ruwan ya ci gaba da tafiya zuwa yammacin birnin Misrata bayan bincike da kuma biyan tara.
Mai magana da yawun sojojin da ke Benghazi ya ce jirgin ya saɓa ƙa'idojin teku kuma ya shiga yankin da aka haramta masa.
Turkiyya, wadda take goyon bayan gwamnatin Libya da ƙasashen duniya suka amince da ita ta ce za ta kalli waɗanda suke da hannu a lamarin a matsayin mahara.
Jirgin dai yana ɗauke ne da kayayyakin asibiti daga Masar.

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta karbi bakuncin Borussia Monchengladbach a wasa na karshe a cikin rukuni na biyu a Champions League ranar Laraba.
Borussia Monchengladbach ce ta daya a rukuni na biyu da maki takwas, yayin da Shakhtar Donesk ce ta biyu da maki bakwai.
Real Madrid ma makai bakwai ne da ita sai Inter Milan ta karshe da maki biyar.
Ga cikakken labarin a nan:

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty ta bayyana cewa tsofaffi ne suka fi shan wuya da tagayyara a hare-haren Boko Haram sakamakon yadda ba su iya samun damar tserewa a duk lokacin da aka kai harin.
Ƙungiyar ce ta bayyana hakan a wani rahoto da ta fitar mai shafuka 67 a ranar Talata, ta kawo misalai da dama da ke nuna yadda waɗanda suka manyanta yunwa ta kashe su, haka kuma aka yanka su, da kuma mutuwarsu a hannun sojoji ba bisa ƙa'ida ba
Ƙungiyar ta bayyana cewa hakan na faruwa ne sakamakon akasarin garuruwan da ke ƙarƙashin Boko Haram tsofaffi ne suka fi yawa waɗanda suka kasa guduwa ko kuma waɗanda suka zaɓi su tsaya su ci gaba da aiki a gonakinsu.
A kwanakin baya ne dai 'yan Boko Haram ɗin suka yanka manoma 43 a garin Zamarmari da ke jihar Borno.

Asalin hoton, AFP
Rikici ya sake ɓarkewa a Majalisar Tarayyar Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo a karo na biyu a jere.
A yau, sai da ta kai ga an kira 'yan sanda domin su raba faɗa tsakanin magoya bayan Shugaban ƙasar Felix Tshisekedi da kuma magoya bayan Tsohon Shugaban, Jospeh Kabila.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa mutum uku sun samu rauni sakamakon jifar juna da ɓangarorin suka rinƙa yi.
Har sai da aka yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa mutanen da ke wajen majalisar a Kinshasa babban birnin ƙasar.
Ko a jiya sai da aka bayar da rahoton cewa an lalata kujerun majalisar sakamakon rikicin da aka yi.

Wata matsala da ke mamaye fagen siyasar Jamhuriyyar Nijar a yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓe ita ce ta yawaitar labarun ƙarya a shafukan sada zumunta.
Wasu na amfani da kafofin na zamani don yaɗa labarin da suke so don ɓata suna ko ma aibata wani, abin da ake gani zai iya kawo cikas a ƙoƙarin da ake na shimfiɗa zaman lafiya a lokacin zaɓe.
Ga cikkaken labarin a nan:

Asalin hoton, Thinkstock
Ma'aikatar noma a Faransa ta tabbatar da ɓullar wata cutar murar tsuntsaye a wata gonar agwagwa da ke kudu maso yammacin kasar.
Wannan ne karon farko da aka samu barkewar cutar a Faransa cikin wannan shekarar. Tuni aka killace yankunan da ke kusa da gonar.
Cutar murar tsuntsaye tana yaduwa a Turai inda a aka tabbatar da cutar a Jamus da Netherlands wanda ya sa aka rage tsuntsaye da dama.
Ana cikin shirin ko ta kwana a akasarin Faransa saboda cutar abin da ke nufin ana ajiye tsuntsayen cikin gida ko sanya matakan kariya.
Wata kotu a Senegal ta yanke wa wasu iyaye maza uku hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata daya saboda biyan masu safarar mutane kudi su kai yaransu Turai.
Daya daga cikin yaran mai suna Ousmane Faye da aka fi sani da Doudou ya mutu a teku cikin watan Oktoba.
Matashin mai shekara 15 yana da burin shiga makarantar koyar da kwallon kafa a Italiya.
Kotun ta kuma yanke wa mutanen hukuncin gyara halinka na shekara biyu saboda kasada da rayukan yaransu.
Mahaifin Doudou ya biya kusan dala 450 ga masu safarar mutanen. Mutuwar matashin ta sa fargaba a zuƙatan jama'a a Senegal inda aka samu ƙarin baƙin haure da ke ƙoƙarin isa Turai.

Baturen zabe na Jihar Ashanti da ke Ghana, Benjamin Bannor Bior, ya ce sun samu wasu ƙuri'u ɗauke da hatimin boge.
Ya bayyana haka ne bayan hukumar zaɓe reshen jihar ta Ashanti ta kammala ƙirgar ƙuri'un, sai dai ba ta kai ga bayyana sakamakon ba.
Ya ce an kwaikwaye su ne don a ɓata wa hukumar zabe aiki.

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Majalisar zartarwa ta jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta rusa kwamitin shugabancinta na ƙasa da na yankuna da na jihohi.
An rusa kwamitin shugabancin riƙo na ƙasa ƙarƙashin shugabancin Gwamna Mai Mala Buni na Yobe a zaman da majalisar ta yi bisa jagorancin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Fadar Aso Rock Villa yau Talata.
Sai dai an sake naɗa Mai Mala Buni domin ci gaba da jagorancin kwamitin na tsawon wata shida.
Kazalika, majalisar ta kori Ntufam Hilliard Eta, tsohon mataimakin shugaban APC na yankin kudu maso kudu, daga jam'iyyar saboda ya ƙi janye ƙarar da ya shigar da jam'iyyar a gaban kotu yana neman ta ayyana shi a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa.
Taron ya samu halartar Gwamnan Jihar Ebonyi, David Nweze Umahi, wanda ya koma APC a watan da ya gabata daga jam'iyyar PDP.
An kafa kwamitin Mai Mala Buni ne sakamakon rikicin shugabancin da jam`iyyar ta yi fama da shi.
Zaman ya mayar da hankali ne wajen nazarin rahoton da shugaban kwamitin rikon jam`ya mika musu dangane da aikin da ya yi na daidaita tafiyar jam`iyyar da sasanta tsakanin `ya`yanta da yin bikon `ya`yan jam`iyyar da suka fice da kuma janyo sabbin magoya baya.

Asalin hoton, EPA
Hukumar zaɓen Ghana ta ce har yanzu tana ci gaba da tattara sakamako daga yanki 16 na ƙasar kuma za ta sanar da sakamakonsu da zarar ta kammala tattarawa.
Ghana Electoral Comission ta ce (EC) - ƙarƙashin shugabancin Jean Mensa - ta ce a wannan karon tana tattara sakamakon ne daga yanki 16 ba mazaɓa 275 ba kamar yadda ta saba a baya.
Hakan na nufin babu wani sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka bayyana a hukumance zuwa yanzu.
Sai dai hukumomin yankuna na ci gaba da ƙirgawa tare da bayyana nasu sakamakon.
EC ta roƙi 'yan ƙasa da su ƙara haƙuri yayin da suke jiran su ji sakamakon abin da suka zaɓa na mutumin da zai shugabance su nan da shekara huɗu masu zuwa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Reuters
Binciken da aka gudanar kan kisan gillar da wani mai tsattsauran kishin farar fata ya aikata a masallacin birnin Christchurch na New Zealand ya gano cewa akwai gazawar hukumomin tsaro.
Brenton Tarrant ya kashe Musulmi 51 a ranar 15 ga watan Maris din shekarar 2019.
Wakiliyar BBC ta ce bincike ya gano akwai gazawa wajen kare Musulmi da gano ainihin manufar ɗan bindigar ko kuma duba irin kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da yake harka da su.
Firaminista Jacinda Ardern, ta nemi afuwa kuma ta ce gwamnati ta karbi shawarwari da aka ba ta ciki har da kafa sabuwar hukumar bincike.

Asalin hoton, NASS
Ɗan Majalisar Wakilan Najeriya Honorabul Herman Hembe ya fice daga jam'iyyarsa ta All Progressive Grand Allience (APGA) kuma ya koma All Progressives Congress (APC) mai mulkin Najeriya.
An bayyana ficewar ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Vandeikya/Konshisha daga Jihar Benue a zaman majalisar na yau Talata.
Herman Hembe mai shekara 45, shi ne tsohon shugaban kwamitin Board of Michael Imodu NILS a majalisar.
An fara zaɓarsa zuwa majalisar a shekarar 2007 sannan aka sake zaɓarsa a 2011 kafin daga bisani ya sake komawa a 2019 ƙarƙashin tutar jam'iyyar APGA.
Kotun Ƙoli ta kore shi daga majalisar a 2017 bayan ta yanke hukuncin cewa ba shi ya ci zaɓe ba a jam'iyyar APC kuma ta bayar da umarnin a rantsar da Dorathy Mato ta maye gurbinsa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Rukunin H na Real Madrid da Inter Milan da Borussia Monchengladbach da Shakhtar na cikin halin fargaba, sakamakon kowannensu na da damar zuwa zagaye na gaba a wasan ƙarshe.
Monchengladbach za ta ziyarci Real Madrid a yau. Duk wanda ya ci wasa a cikinsu shi ne zai fito daga rukunin. Haka nan idan aka yi canjaras Monchengladbach ce za ta fito.
Real Madrid za ta iya fitowa idan aka yi canjaras amma dole ne sai Inter ta doke Shakhtar. Hakan zai faru ne saboda Madrid ta fi zira wa Inter ƙwallaye - ba Shakhtar ba.
Idan Shakhtar ta ci wasa za ta fito. Kuma za ta iya fitowa ma da canjaras indai Madrid ta ci nata wasan.
Wajibi ne Inter Milan ta ci wasa kafin ta fito. Ko da ta ci, indai aka tashi canjaras a ɗaya wasan to gida za ta koma.

Asalin hoton, BBC Sport
Manchester United
Rukunin H da ya ƙunshi Manchester United da PSG da RB Leipzig da Istanbul Basaksehir, shi ma a rikice yake.
Man United na buƙatar maki ɗaya kacal domin ta samu zuwa zagaye na gaba. Idan har aka doke ta a wasa tsakaninta da RB Leipzig to za ta wuce kai tsaye zuwa Europa League.
Za ta ƙare a mataki na ɗaya a rukunin (idan PSG ba ta ci Istanbul Basaksehir ba), idan PSG ta ci wasanta, ita ce za ta jagoranci rukunin ko da kuwa Man United ta ci wasa.
Leipzig za ta wuce zagaye na gaba idan ta ci wasa. Idan kuma ta yi canjaras to za ta buƙaci a cinye PSG.
Idan PSG da Man United suka yi rashin nasara PSG ce za ta fito (tare da Leipzig) saboda bambancin yawan ƙwallayen da PSG ta ɗura wa United.

Asalin hoton, BBC Sport