Zaben Ghana 2020: An fara kai sakamako hukumar zaɓe

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Labarai cikin minti ɗaya

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari Miniti Daya Da BBC Na Rana 07/12/2020
    • Majalisar Wakilan Najeriya ta yi watsi da kiran da wani ɗan majalisar ya yi na a tsige Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daga mulki. Honorabul Kingsley Chinda mai wakiltar mazaɓar Obio/Akpor ta Jihar Rivers da ke kudancin Najeriya ya nemi 'yan Najeriya da su matsa wa wakilansu a majalisa da su fara shirin tsige Buhari daga mulki ranar Lahadi.
    • Ƙungiyar haɓaka tattalin arzikin Afirka ta Yamma wato ECOWAS ta tura wakilanta 125 domin sa ido a zaɓen Ghana. An tura wakilan ne zuwa dukkanin sassa 16 na ƙasar domin ganin yadda mutum miliyan 17 za su kaɗa ƙuri'unsu a yau Litinin a zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisa.
    • Aƙalla mutum ɗaya ya mutu sannan an kwantar da mutum 227 a asibiti sakamakon kamuwa da wata baƙuwar cuta a jihar Andhra Pradesh da ke kudancin India. Mutanen da suka kamu da cutar suna nuna alamomi kamar su jiri da kuma suma, a cewar likitoci.
  2. Shugaban Ƙasa Nana Akufo-Addo ya kaɗa ƙuri'arsa

    Ghana

    Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo ya kaɗa ƙuri'arsa a mazaɓar Rock Ages da ke Kibi.

    Shugaban ya ce ya gamsu da kuma farin ciki da yadda zaɓen ke tafiya a faɗin ƙasar.

    "Ina cike da fata da kuma farin cikin yadda zaɓen ke tafiya a ƙasa baki ɗaya. Lafiya ƙalau yake tafiya," in ji shi.

    "Hakan na nuna irin yadda al'ummnar Ghana ke mutunta harkokin dimokuraɗiyya."

    Ghana
  3. Ba a tabbatar da zargin da ake yi wa wani mutum ba da aka kama da ƙuri'u

    'Yan sandan Ghana sun ce babu tabbas game da zargin da ake yi cewa an ga wasu takardun kaɗa ƙuri'a da aka dangwala wa wata jam'iyya.

    Rundunar ta nemi 'yan ƙasar su kwantar da hankalinsu yayin da suke bincike a kan lamarin kuma za su bayar da rahoton binciken nasu.

    A jiya Lahadi ne mazauna yankin Sunyani suka kama wani mai suna Daniel Tibiri Boahen a cikin wata motar 'yan sanda tare da zargin yana ɗauke da wasu takardun kaɗa ƙuri'a.

    Ciikin wani saƙon Twitter, 'yan sandan Ghana sun ce bincike ya nuna tun a farkon wannan shekarar aka yi gwanjon motar ga wani mutum.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Majalisar Wakilan Najeriya ta yi watsi da neman a tsige Buhari

    Buhari da shugabannin majalisa

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Majalisar Wakilan Najeriya ta yi watsi da kiran da wani ɗan majalisar ya yi na a tsige Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daga mulki.

    Honorabul Kingsley Chinda mai wakiltar mazaɓar Obio/Akpor ta Jihar Rivers da ke kudancin Najeriya ya nemi 'yan Najeriya da su matsa wa wakilansu a majalisa da su fara shirin tsige Buhari daga mulki ranar Lahadi.

    Sai dai mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya bayyana kiran ɗan majalisar da cewa "ra'ayin mutum ɗaya ne kawai daga cikin jam'iyyar adawa".

    "Da a ce wannan kiran bayan zuwan Buhari majalisa ne kuma ya gaza yin cikakken bayani ko kuma ya ƙi ɗaukar shawararmu, sai a ce kiran ya yi ma'ana," in ji Benjamin Kalu cikin wata sanarwa.

    A makon da ya gabata ne majalisar ta daddale sannan ta yi kira ga Shugaba Buhari da ya bayyana a gabanta domin yin bayani kan halin rashin tsaro da ƙasar ke ciki.

    Matsalar tsaron da ake ciki ta ƙara ta'azzara a kwana nan sakamakon hare-haren 'yan fashin daji a arewacin ƙasar da kuma yankan rago da Boko Haram ta yi wa manoma 43 a Zabarmari ta Jihar Borno, abin da ya sa majalisar ta gayyace shi.

    Duk da cewa majalisar ba ta faɗi sanda take so shugaban ya je ba, ana sa ran ya bayyana a wannan makon bayan Kakakin Majalisa Femi Gbajabeamila ya ce Buharin ya yarda zai amsa gayyatar - kodayake shi ma bai faɗi rana ba.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Wakilan ECOWAS sun isa Ghana domin sa ido a zaɓe

    Wakilan ECOWAS

    Asalin hoton, ECOWAS

    Ƙungiyar haɓaka tattalin arzikin Afirka ta Yamma wato ECOWAS ta tura wakilanta 125 domin sa ido a zaɓen Ghana.

    An tura wakilan ne zuwa dukkanin sassa 16 na ƙasar domin ganin yadda mutum miliyan 17 za su kaɗa ƙuri'unsu a yau Litinin a zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisa.

    Tawagar wadda ke ƙarƙashin jagorancin tsohuwar Shugabar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf, ta ƙunshi wakilai daga ɓangarorin ƙungiyar daban-daban kamar majalisa da kotu da ƙungiyoyin farar hula da ƙwararru da sauransu.

    Wakilan ECOWAS

    Asalin hoton, ECOWAS

    Wata sanarwa da ECOWAS ta fitar ta ce tuni tawagar ta gana da shugabar hukumar zaɓen Ghana da jami'an gwamnati da jami'an tsaro da shugabannin masu sa ido daga ƙasashen waje domin ƙara wa juna sani game da zaɓen.

    Bisa kundin dokokinta game da zaɓe da tafiyar da kyakkyawan shugabanci na Supplementary Protocol on Democracy and Good Governance, ECOWAS na da damar tura masu sa ido zuwa ƙasashe mambobinta da ke gudanar da zaɓe.

  6. Channels TV na bincike kan ɗan jaridarta da ake zargi da lakaɗa wa matarsa duka

    Channels TV

    Asalin hoton, Channels TV

    Kafar talabijin ta Channels TV ta ce ta fara bincike kan wani ma'aikacinta da ake zargi da lakaɗa wa matarsa dukan kawo wuƙa.

    Rahotanni sun ruwaito cewa ana zargin Pius Angbo, wanda shi ne wakilin Channels a Jihar Benue, ya yi wa matarsa likita Ifeanyinwa Angbo duka har ma ya ji mata raunuka.

    Cikin wani bidiyo da Sahara Repoters ta samu a daren Lahadi, matar ta ce mijin nata ya dake ta bayan ta ba shi shawara kan ya daina kashe wa 'yan mata kuɗi, ya ajiye su domin kula da 'ya'yansa.

    Gidan talabijin na Channels ya mayar da martani kan lamarin, yana mai cewa ba zai lamunci cin zarafi ba.

    "Channels Talevision ba za ta taɓa yarda da cin zarafin mata ba ko kuma sauran mutane baki ɗaya. Ana bincikar lamarin kuma za a ɗauki matakin da ya dace."

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Wasu masu kaɗa ƙuri'ar sun bayar da tazara...

    Ghana
    Bayanan hoto, Wasu masu zaɓe kenan a kan layin kaɗa ƙuri'a, inda suka bai wa juna tazara saboda korona, amma kuma mafi yawansu ba su da takunkumi
    Ghana
    Bayanan hoto, Tun farko hukumar zaɓen Ghana ta EC ta ce duk wanda ba shi da takunkumi ba zai shiga wurin kaɗa ƙuri'a ba
    Ghana
    Bayanan hoto, Sai dai kuma waɗannan ba su san mece ce tazara ba kamar yadda ake gani
  8. Kashi 51 cikin 100 na masu katin zaɓe a Ghana mata ne

    Bayanan bidiyo, Yadda wata hajiya ta kaɗa ƙuri'arta

    Alƙaluman da hukumar zaɓen Ghana EC ta fitar sun nuna cewa kashi 51 cikin 100 na masu katin zaɓe a ƙasar mata ne.

    Wakilin BBC Haruna Shehu ya shaida mata da yawansu a rumfunan zaɓen da ya halarta.

    Ana sa ran mutum fiye da miliyan 17 za su kaɗa ƙuri'a a rumfar zaɓe fiye 38,000.

  9. Labarai cikin minti ɗaya

    Bayanan sautiMINTI DAYA DA BBC NA SAFE 07/12/2020
  10. Mutum fiye da miliyan 17 ne ake sa ran za su kaɗa ƙuri'a a yau

    Ghana

    Mutum fiye da miliyan 17 ne ake sa ran za su kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasar Ghana da kuma na 'yan majalisa a yau Litinin.

    Za a gudanar da zaɓen a rumfar zaɓe fiye da 38,000 a yanki 16 na Ghana.

    Shugabar hukumar zaɓe ta Ghana, Jean Mensa, ta gargaɗi masu zaɓe da kafafen yaɗa labarai da su guji tayar da fitina game da sakamakon zaɓen.

    Jean Mensa ta ce hukumar Ghana Electoral Commission (EC), ita kaɗai ce ke da alhakin sanar da sakamakon, kamar yadda doka ta tanada.

    Wakilin BBC ya ce mutane sun fara fitowa tun misalin ƙarfe 2:00 na dare domin jefa ƙuri'ar.

    A yammacin jiya Lahadi ne Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar jam'iyyar NPP, Nana Akufo-Addo ya yi wa 'yan ƙasar jawabi game da zaɓen.

    Shugaban ya ƙarfafa wa mutane gwiwar cewa kar su bari cutar korona ta hana su fita rumfar zaɓe kuma ya gargaɗe su cewa jami'an tsaro za su hukunta duk wanda ya karya doka.

  11. Nana Akufo-Addo da John Mahama sun sha fafatawa kafin yanzu

    Nana Akufo-Addo da John Mahama

    Asalin hoton, Others

    Duniya ta shiga wani yanayi da hali na rashin tabbas da mamaki a wannan shekarar sai dai zaɓen Ghana bai zo da wani mamaki ba.

    Dan takarar jam'iyya mai mulki ta NPP, Mr Akufo-Addo mai shekara 76, da babban abokin hamayyarsa, Mr Mahama, mai shekara 62, na jam'iyyar NDC na fafatawa a karo na uku.

    A shekara ta 2012 mutanen biyu suka yi takarar farko.

    A takararsu ta farko, kwatsam Mr Mahama ya kasance mutumin da jam'iyyarsa ta zaɓa bayan mutuwar shugaba John Evans Atta Mills wata biyar kafin zaɓe.

    Mr Mahama mai shekara 62, ya doke abokin hamayyarsa Mr Akufo-Addo ɗan shekara 76 da samun nasara.

    An ƙalubalanci sakamakon zaɓen a kotu kan zargin maguɗi sai dai bayan wata 8 kotun ƙoli ta tabbatar wa Mr Mahaman da nasara.

    Amma a 2016, Mr Akufo-Addo ya rama.

    Mr Mahama ya shaida wa BBC cewa matsalolin tattalin arziki, rikicin mulki da ya shawo kansa a makare, da labaran boge da akai ta yaɗa wa a kafofin sada zumunta su suka haifar da rashin nasararsa shekaru hudu da suka wuce.

    Amma ko ma dai me ya faru, ba za a sake tataɓurza ba tsakanin mazajen biyu - domin duk wanda ya yi nasara a wannan lokaci to ya gama wa'adinsa na shugabanci sau biyu.

  12. Zaɓen Ghana

    Ghana
    Bayanan hoto, Haulah Ishaq - wata mai lalurar nakasa - ta kaɗa ƙuri'arta a birnin Kumasi
    Ghana
    Bayanan hoto, Wakiliyar yaƙi da cutar korona a wata rumfar zaɓe a Kumasi na auna zafin jikin masu zaɓe kafin su jefa ƙuri’a
  13. An fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasar Ghana

    Ghana

    A yau al'ummar Ghana ke kaɗa kuri'a a babban Zaɓe na shugaban ƙasa da ƴan majalisa.

    Shugaba Nana Akufo-Addo na fatan sake nasara a wa'adi na biyu, yayin da abokin hamayyarsa John Mahama ya kasance tsohon shugaba, wanda a baya sau biyu suna fafatawa.

    Rahotanni na nuna yiwuwar su yi kai da kai.

    Dukkanin mutum biyun sun alkawarta bunƙasa tattalin arzikin Ghanar da ke cikin garari da tabbatar da cewa an yi zaɓen cikin kwanciyar hankali.

    Sai dai ana fargabar yiwuwar samun rikicin bayan zaɓe.

    Ghana
  14. Maraba

    Barkanku da hantsin Litinin tare da fatan kun tashi lafiya.

    Ku biyo ni Umar Mikail domin sanin yadda take kasancewa a zaɓen shugaban ƙasar Ghana da sauran sassan duniya.