Zaben Ghana 2020: An fara kai sakamako hukumar zaɓe

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

    Masu bibyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. Bidiyon yadda ake kirga kuri'un zaɓe Ghana

    Bayanan bidiyo, Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  3. Bama-bamai sun hallaka mutum shida a Kudancin Kaduna

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren rahoton

    A Najeriya, ƙungiyar mutanen yankin Kudancin Kaduna, wato SOKAPU, ta bayyana damuwa game da jefa wasu abubuwa da ake zargin bama-bamai ne kan wasu gidaje da wasu jiragen sama suka yi a jiya Lahadi, a garin Kasayi na yankin karamar hukumar Chikun a jihar ta Kaduna.

    Al'amarin dai ya yi sanadin mutuwar mutane aƙalla shida, wasu kimanin huɗu kuma suka samu munanan raunuka.

  4. Buhari zai hallara gaban majalisun tarayya ranar Alhamis

    ..

    Asalin hoton, Nigerian Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai hallara gaban zaman haɗaka na majalisun tarayyar ƙasar a ranar Alhamis domin yi musu jawabi.

    Mai taimaka wa shugaban ƙasar kan kafofin sada zumunta, Lauretta Onochie ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter.

    Duk da cewa babu tabbacin abubuwan da shugaban zai yi magana a kansu, amma ana sa ran cewa zai taɓo batun matsalar tsaro.

    A makon da ya gabata ne dai majalisar ƙasar ta gayyaci shugaban ya hallara a gabanta inda kuma ya amsa goron gayyatar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Zaben Ghana 2020: An fara kai sakamako hukumar zaɓe

    ..
    .
  6. MINTI ƊAYA DA BBC - LABARAN YAMMA 07/12/2020

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren labaran
  7. Ƙungiyar al-Qaeda ta tabbatar da kashe mutum shida

    Reshen ƙungiyar al-Qaeda da ke Yemen ya bayyana cewa ƙungiyar ce ta kashe mambobin wata ƙungiyar 'yan aware shida a kudancin lardin Abyan.

    Mutum shidan da aka kashe, na daga cikin masu kayan sarki na ƙungiyar 'yan aware ta Southern Transitional Council wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen korar 'yan ƙungiyar al-Qaeda da kuma IS daga kudancin ƙasar.

    Kungiyar, wadda ke da goyon bayan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na so a raba Yemen, ƙasar da aka haɗa kanta sama da shekara 30 da suka gabata.

  8. Shugaban Ghana ya ce a kasa a tsare yayin ƙirga ƙuri'u

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban ƙasar Ghana, Nana Akuffo-Addo ya buƙaci a kasa a tsare yayin da ake ƙirga ƙuri'un Ghana.

    Shugaban ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter jim kaɗan bayan an soma ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa a wasu daga cikin rumfunan zaɓen ƙasar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. An soma ƙirga ƙuri'un da aka jefa a zaɓen Ghana

    ..

    An soma ƙirga ƙuri'un zaɓen Ghana a wasu rumfunan zaɓen ƙasar.

    An dai fara jefa ƙuri'un ne tun da safiyar yau Litinin.

    Manyan 'yan takarar da ke fafatawa su ne Shugaban ƙasar Nana Akuffo-Addo da kuma Tsohon Shugaban ƙasar, John Dramani Mahama.

    Ƴan takara 11 ke ƙalubalantar shugaba mai-ci Nana Akufo-Addo, wanda ke neman wa'adi na biyu.

    ..
  10. 'Yan majalisa sun lalata kujeru yayin hatsaniya a DR Congo

    An samu hatsaniya a Majalisar Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo, inda 'yan majalisar da ke goyon bayan Shugaba Felix Tshisekedi suka lalata kujerun majalisar.

    Wannan ce rigima ta baya-bayan nan tsakanin magoya bayan Tsohon Shugaban ƙasar, Joseph Kabila da na Felix Tshisekedi, inda har yanzu magoya bayan Kabila ke da rinjaye a majalisar.

    A ranar Lahadi ne Shugaba Tshisekedi ya bayyana cewa ana ƙoƙarin daƙile tsare-tsarensa, inda ya ce yana so ko dai ya kafa gwamnatin haɗin gwiwa ko kuma ya sanar da gudanar da sabon zaɓe.

    Wakiliyar Majalisar Ɗinkin Duniya a Congo, Leila Zerrougui, ta yi gargaɗin cewa rikicin siyasa na da illa matuƙa ga ƙasar.

  11. Hotunan harbin da wasu 'yan bindiga suka yi a wata rumfar zaɓe a Ghana

    ..
    ..
    ..
  12. Sojojin Ethiopia sun 'dakatar' da jami'an MDD daga shiga sansanin 'yan gudun hijira

    Rahotanni daga arewacin Tigray na cewa sojoji daga Ethiopia sun dakatar da jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya daga shiga wani sansanin 'yan gudun hijira.

    Wasu rahotanni da ba a tabatar ba na cewa an harbi ɗaya daga cikin jami'an MDD a ranar Lahadi a daidai lokacin da tawagar ta majalisar ke ƙoƙarin shiga sansanin da ke a Shimelba, wanda mazauni ne ga dubban 'yan Eritrea.

    Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan MDD ta bayyana cewa ta cimma matsaya da hukumomi a Ethiopian domin kai kayan agaji a yankin Tigray wanda a halin yanzu ke ƙarƙashin gwamnatin tarayyar ƙasar bayan shafe sama da wata guda a ana rikici.

  13. Malaman jami'a sun ce ba za su koma aiki ba sai an biya su albashinsu

    ..

    Asalin hoton, FESTUS KEYAMO/TWITTER

    Kungiyar malaman jami'a ta Najeriya ASUU, za ta kammala tattaunawar da take yi a wannan makon sannan ta sanar da gwamanti domin su sake zama.

    ASUU na tattaunawa da sauran mambobinta kan sabon tayin da gwamnati ta yi musu bayan kammala tattaunwarsu a ranar 27 ga watan Nuwamba.

    A tattaunawar da aka yi, gwamnati ta yarda ta biya malaman albashinsu amma sai sun fara komawa bakin aikinsu - abin da malaman suka ce sun ƙi wayon, babu kudi babu aiki.

    Ga cikakken labarin a nan:

  14. 'Yan sanda sun kama wasu ma'aikatan hukumar zaɓen Ghana

    'Yan sandan Ghana sun kama wasu daga cikin jami'an hukumar zaɓen ƙasar, sakamakon zargin yin taɓe-taɓe a jikin takardar zaɓen ƙasar, wanda hakan ya dagula sahihancin takardar.

    A wata sanarwa da hukumar zaɓen ta fitar a shafinta na Twitter, hukumar ta ce a halin yanzu waɗanda aka kama ɗin na hannun 'yan sanda.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Ana ci gaba da kaɗa ƙuri'a a zaɓen Ghana

    ..

    Babban Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye Mubarak Muntaka yayin da ya kada kuri'a a zaɓen Ghana da taimakon karamar 'yarsa.

    ..
  16. Ƙungiyar likitocin Kenya ta janye yajin aikin da ta shirya shiga

    Likitoci a Kenya sun janye yajin aikin da suka shirya somawa a ranar Litinin sakamakon rashin kayayyakin kare kai da kuma inshorar lafiya da kuma ƙarancin ma'aikata a yaƙi da annobar korona.

    An dakatar da yajin aikin da kwanaki 14 domin bayar da dama a sake tattaunawa, kamar yadda ƙungiyar likitoci ta ƙasar ta bayyana.

    Ana sa ran cewa manyan 'yan ƙungiyar likitocin za su tattauna da sanatocin ƙasar da 'yan majalisa a ranakun Laraba da Alhamis.

    Ƙasar da ke gabashin Afrika ta sake samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar ta korona.

    A yanzu dai an tabbatar da mutum 88,380 sun kamu da cutar a ƙasar tun bayan ɓullarta, inda kuma mutum 1,526 cutar ta kashe, kamar yadda ƙididdigar Jami'ar John Hopkins ta nuna.

  17. Yadda aka fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen Ghana

    A wannan bidiyon na sama, babu maganar bayar da tazara domin kauce wa yaɗa cutar korona.

    Sai dai wasu na sanye da takunkumi yayin da suke ƙokarin kafa layin jefa ƙuri'a a wata rumfar zaɓe da ke birnin Kumasi.

  18. An harbi mutum biyu a kusa da rumfar zaɓe

    'Yan sandan Ghana

    Asalin hoton, @GhPoliceService

    Mutum biyu sun jikkata sakamakon harbin bindiga a kusa da rumfar zaɓen Steps to Christ da ke mazaɓar Awutu Senya East.

    'Yan sanda sun ce wasu mutane ne da suka je wurin a baƙar mota suka buɗe wa wasu mutanen wuta a ƙaramar mota ƙirar KIA.

    Rundunar 'yan sandan Ghana ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa an kai waɗanda aka raunata asibiti.

    "An kai waɗanda ke cikin motar asibiti bayan sun ji rauni kuma ana ba su kulawa," in ji 'yan sandan, a cikin wata sanarwa.

    "Ya zuwa yanzu 'yan sanda na binciken duk wani zargin maguɗi da suka samu."

    Babu wani ƙarin bayani game da abin da ya jawo harbin. Rahotanni sun bayyana cewa an samu hatsaniya tun yayin aikin rajistar zaɓe a mazaɓar ta Awutu Senya East.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Hukumar zaɓen Ghana ta dakatar da ma'aikatanta bisa shirin yin maguɗi

    'Yan sanda

    Hukumar zaɓen Ghana EC ta kori wasu ma'aikatanta daga rumfunan zaɓen da suke aiki bayan an kama su da shirin yin maguɗi.

    EC ta ce matakin ya biyo bayan rahotannin da ta samu ne na wasu jami'an zaɓe da aikata ba daidai ba ta hanyar mallakar ƙuri'un da zaɓen shugaban ƙasa waɗanda ba sahihai ba.

    Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce ta haɗa kai da rundunar 'yan sanda, inda ta gano ma'aikatan tare da dakatar da su daga rumfar zaɓe a Awutu Senya West da kuma Bawku.

    "Kafin a ƙirga kowacce ƙuri'a a matsayin sahihiya, sai ta kasance ɗauke da sunayen duka 'yan takara 12 a jikinta," hukumar ta jaddada.

    Kazalika, hukumar ta yi kira ga wakilan jam'iyyu da su ƙara sa ido da kuma wayar da kan masu zaɓe.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. An kashe jami'in gwamnati a zaɓen Kamaru

    Kamaru

    Asalin hoton, Reuters

    An kashe wani jami'in gwamnati a kusa da garin Bamenda na arewacin Kamaru jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen ranar Lahadi na yankuna, irinsa na farko a ƙasar.

    Ana zargin 'yan tawayen yankin rainon Ingila ne suka kashe shi, waɗanda suka tsaurara hare-hare a baya-bayan nan.

    Gwamnati na fatan zaɓen na wakilai 900 a yanki 10 na ƙasar zai share fagen ƙara wa yankuna ƙarfin iko a yankin rainon Ingila kamar yadda aka bayar da shawara a tattaunawar da aka yi bara a wurin taron ƙasa kan yankin.

    Sai dai wasu daga cikin 'yan jam'iyyun adawa na SDF da MRC ba su shiga zaɓen ba, sannan wasu na ganin cewa zaɓen ba zai kawo ƙarshen tawayen da aka shafe shekara huɗu ana yi ba a yankin na rainon Ingila.

    "Don mun samu wakilai daga yankuna ba ya nufin shikenan sai harbe-harbe su tsagaita komai ya dawo lafiya ƙalau," a cewar wani mai sharhin siyasa Stephane Akoa a hirarsa da Reuters.