‘Ƴan bindiga sun yi wa manoma fiye da 40 yankan rago a Borno’

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Mutum 22 sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a Chadi

    Shugaba Idriss Deby

    Asalin hoton, @MIdrissDebyItno

    Mutum aƙalla 22 ne suka mutu sakamakon wani mummunan rikici da ya kaure tsakanin makiyaya Larabawa da manoma da ke zaune a yankin Kabbia da ke kudancin Chadi.

    Ana kyautata zaton rashin jituwar ta samo asali ne daga satar shanu da take amfanin gona da ake samu tsakanin al'ummar biyu.

    Ministan Sadarwar Chadi, Cherif Mahamat, ya fada wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa ƙauyuka da dama sun ƙone yayin rikicin na ranakun Litinin da Talata.

    An kama mutum 66 kuma dokar hana fita ta fara aiki a yankin.

    Rikici tsakanin ƙungiyoyin ya kunno kai a yankin Sahel da ke gabar Chadi tun tsawon shekaru da dama da suka gabata.

  2. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ɗan fashi a Filato

    A ci gaba da ayyukanta na yaƙi da fashi da makami, rundunar Operation Safe Heaven ta sojojin Najeriya ta ce ta kashe wani da ake zargin ɗan fashi ne a Barkin Ladi da ke Jihar Filato.

    Mutumin ya gamu da ajalinsa ne yayin da dakarun rundunar suka yi arangama da tawagarsu ranar Laraba a kan Titin Angul Maraban Jama’a da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu.

    A cewar wata sanarwa da Birgediya Janar John Enenche ya fitar a yau Asabar, abokan tafiyarsa ne suka harbe shi sakamakon musayar wutar da aka yi tsakaninsu da sojojin, inda wasu suka tsere da raunuka.

    Sanarawar ta ƙara da cewa an ƙwace ƙaramar bindiga ƙirar gida a hannunsa.

    A ranar Larabar ne kuma rundunar ta ce ta kashe 'yan fashi aƙalla 82 a jihohin Katsina da Zamfara.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Cutar korona na yaɗuwa kamar wutar daji a Amurka

    Korona a Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Adadin mutanen da suka kamu da cutar korona a Amurka ya zarce miliyan 13 yayin da har yanzu cutar ke ci gaba da yaɗuwa kamar wutar daji.

    Kimanin Amurkawa 230,000 ne suka mutu sakamakon cutar da kuma 900,000 kwance a gadajen asibiti.

    Duk da haka, ana sa ran cutar ta kara yin ƙamari, yayin da miliyoyin yan ƙasar ke balaguro domin ziyarar 'yan uwansu a bikin cikaciki ko kuma Thanksgiving.

    Yayin da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Joe Biden ke kira ga jama'a su yi bikin daga gida ba tare da gayyar 'yan uwa ba, shi kuwa shugaba mai barin gado Donald Trump na kiran jama'a su taru, a ci a sha, a kuma yi wa ƙasa addu'a.

  4. Mutum biyu sun mutu a Najeriya sakamakon cutar korona

    Jana'iza

    Asalin hoton, NG Presidency

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu karin mutum 246 da suka kamu da cutar korona a ranar Jumma'a.

    Kazalika, ƙarin mutum biyu sun rasa rayukansu sakamakon cutar, abin da ya kawo jimillar wadanda cutar ta kashe a ƙasar zuwa 1,171.

    Adadin waɗanda suka kamu da cutar a ranar Alhamis ya fi yawa a Legas mai mutum 81, Abuja mai mutum 77, sai Filato mai 19, da Kaduna inda aka samu 25, Ogun mai 13, da Bauchi mai mutum 3.

    Ragowar jihohin da aka samu sabbin kamuwa a cikinsu su ne: Rivers da mutum 4, Ekiti mai mutum 2, Kano mai 2, Taraba ma da mutum 2.

    Da wannan sabbin alƙaluman, jimillar waɗanda cutar ta kama a ƙasar sun kai 66,805, sannan kuma an sallami mutum 62,686 bayan sun warke.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Maraba

    Barkanmu da hantsin Asabar tare da fatan an fara hutun ƙarshen mako a sa'a.

    Umar Mikail ne zai kasance tare da ku daga yanzu zuwa yammaci domin kawo labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Ku biyo ni.