Tsohon mataimakin shugaban APC mai mulkin Najeriya wanda kuma ya shugabanci kwamitin riƙon jam'iyyar, Mister Hilliard Eta, ya kai jam'iyyar kotu yana neman a rusa kwamitin Mai Mala Buni.
Kazalika, Mista Eta na neman Babbar Kotun Tarayyar da ke Abuja da ta bayyana shi a matsayin muƙaddashin shugaban jam'iyyar.
Kwamitin Zartwarwar APC na Ƙasa (NEC) ya rusa kwamitin shugabancin jam'iyyar na ƙasa ranar 25 ga watan Yuni yayin wani taro da ya gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa ƙarƙshin jagorancin Adams Oshiomhole.
Yayin taron ne, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, aka naɗa kwamitin riƙo tare da Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni a matsayin shugaba.
Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da Mai Mala Buni a matsayinsa na shugaba, da John Akpan Udoedehe a matsayinsa na sakatare, da Gwamna Adegboyega Oyetola na Osun, da Gwamna Sani Bello na Neja da kuma Stella Okotete a matsayinsu na mambobin kwamitin.
Ita ma hukumar zaɓe ta INEC na cikin waɗanda ake ƙarar.
Masu ƙarar na ƙorafin cewa sashe na 183 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da Aya ta 17 (i), (iv) da kuma 20 (a), (b) na kundin tsarin APC sun haramta tsige zaɓaɓɓun shugabannin jam'iyyar.
Haka nan, suna ƙorafin cewa Kundin Tsarin Mulki na Najeriya da na APC sun haramta wa masu riƙe da zaɓaɓɓen muƙami na gwamnati su riƙe kowane irin muƙami a cikin APC.
Zuwa yanzu ba a saka lokacin fara sauraron ƙarar ba.