Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Firaministan Habasha ya yi iƙirarin karɓe yankin Tigray
Asalin hoton, Getty Images
Firaiministan Ethiopia, Abiy Ahmed ya yi iƙirarin cewa, sojojin gwamnati
sun karɓe iko da Mekkele, babban birnin yankin Tigray, bayan kwashe fiye da
makwanni uku ana gwabza rikici.
Ya ce, dakarunsa sun kwace manyan gine-ginen gudanarwa da
kuma filin jirgin saman yankin, kuma suna ci gaba da neman shugabannin yankin
da ke da alhakin wannan tawaye.
Daruruwan mutane ne aka kashe a yaƙin wanda ya mayar da
dubbai ƴan gudun hijira.
Wani wakilin tarayyar
Turai na musamman a gabashin Afrika, Alex Rondos ya shaida wa BBC cewa, babban
abin da suka sa a gaba shi ne kare fararen hula, da kuma ganin an kawo ƙarshen
wannan rikici.
Alex ya ce, dole ne kare fararen hula.
“Muna son a ba mu damar shigar da kayan agaji yankin, inda dubban mutane
suka tsere, kuma da yawa suka bace ba a san inda suke ba.”
Zanga-zanga ta ƙazance a Faransa kan sabuwar dokar tsaro
Asalin hoton, Reuters
Rikici ya ɓarke a Paris yayin da dubban mutane suka fito zanga-zanga domin
nuna adawa da wata sabuwar doka.
An yi arangama tsakanin masu zanga-zangar da ƴan sanda, yayin da rikicin ya
ƙara ƙamari bayan dukan da ƴan sanda suka yi wa wani baƙar fata da ya girgiza
Faransawa.
Asalin hoton, Reuters
Masu zanga-zangar na son gwamnati ta soke dokar da ta haramta wallafa hotunan ƴan sanda.
Wasu masu zanga-zangar sun cinna wuta a ginin jaridar kiosque tare da jifar ƴan sanda yayin da kuma ƴan sanda suka harba hayaƙi mai sa ƙwalla.
Masu zanga-zangar sun ce dokar barazana ce ga ƴancin faɗin albarkacin baki, kuma zai hana fallasa wuce gona da irin ƴan sanda.
Yadda Zanga-zangar ta ƙazance
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Roma ta ce an cire bama-baman yaƙin duniya a filinta
Ƙungiyar ƙwallon kafa ta AS Roma da ke Italiya ta mika godiyarta ga sojin ƙasar, kan cire wasu bama-bamai da aka dasa a filin atisayenta tun lokacin yaƙin
duniya na biyu.
Aƙalla bama-bamai 20 aka tono a filin atisayen na Trigoria.
An tayar da bama-bamai masu yawa daga bangaren ƙawance da kuma dakarun Jamus
a yayin yakin, duk da gargaɗin cewa kai harin birnin mai cike da tarihi zai
zama laifi ga bil'adama.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Ana lallashin Iran kan kisan masanin nukiliyarta
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wasu ƴan Iran sun yi zanga-zangar adawa da kisan masanin kimiyar nukiliyar ƙasar
Ana ta kiraye-kirayen kai zuciya nesa bayan Iran ta ce za ta yi ramuwar
gayya kan kisan da aka yi wa babban masanin kimiyyar nukiliyarta da ta ke
zargin Isra'ila da yi.
An kashe Fakhrizadeh ne a wani harin kwanton-ɓauna da
'yan bindiga suka yi a kan motarsa a garin Absard da ke gabashin birnin Tehran.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta nemi akai zuciya nesa.
Gwamnatin Jamus ta nemi a kaucewa duk wani matakin da zai kai ga tashin
hankali a yankin.
Hukumomin Iran sun ce kisan da aka yi ba zai tafi a banza ba. Ko da yake
Shugaba Hassan Rouhani ya ce babu bukatar gaggawa a ramuwar gayyar inda ya ce
Iran za ta roma a lokacin da ya dace.
“Duk wani abu da makiyan Iran ke ji da shi ƙasar a shirye take, kuma ba za
ta bar wannan jinin ya tafi a banza ba, za a dauki fansar wannan mugun aikin a
lokacin da ya da ce.” In ji shugaban.
Carlo Ancelotti ya zubar da hawaye don jimamin Maradona
Asalin hoton, Getty Images
Carlo Ancelotti idonsa ya cika da ƙwalla lokacin da aka ware minti ɗaya domin karrama Maradona kafon soma wasa tsakanin Everton da Leeds United.
Ancelotti wanda ake ganin ɗaya daga cikin fitattun ƴan ƙwallo da kuma mai horar da ƴan wasa ya yi zamani da Maradona, a gasar Seria A, lokacin da yana AC Milan, Maradona kuma a Napoli.
A zamaninsa, Ancelotti ɗan wasan tsakiya ne kuma ya yi hamayya da Maradona.
An nuna idon kocin na Everton cike da ƙwalla a minti ɗaya na jimamin Maradona.
Ancelotti wanda ya horar da Napoli ya san martabar Maradona ga magoya bayan ƙungiyar.
An dakatar da wasa a Seria A, wasan Juventus bayan minti 10 domin karrama Maradona.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Mahrez ya ci wa Man City ƙwallo uku rigis
Riyad Mahrez ya taimaka wa Manchester City lallasa Burnley ci 5-0 a gasar Firimiya da suka fafata.
Ƙwallaye uku Mahrez ya zira a ragar Burnley, yayin da Mendy da Torres suka ci sauran ƙwallayen.
Yanzu ya zama ɗan wasan Afirka na shida da ya ci ƙwallaye 100 da waɗanda ya taimaka aka ci a gasar Firimiya, a cewar Fifa.
Manchester City tanzu ta dawo matsayi na takwas a tebur, daga matsayi na 14 kafin wasan.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
‘Ƴan bindiga sun yi wa manoma fiye da 40 yankan rago a Borno’
Asalin hoton, @HQNigerianArmy
Rahotanni daga jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya sun ce wasu da ake
tunanin mayaƙan Boko Haram ne sun shiga gonaki inda suka kashe fiye da mutum 40.
Lamarin ya faru ne da safiyar Asabar a yankin Kwashebe Zamarmari da ke
cikin ƙaramar hukumar Jere, kamar yadda wasu mazauna yankin suka tabbatar wa BBC.
Sun ce maharan
sun abka wa manoman ne yayin da suke girbin shinkafa. Kuma bayanai sun ce an ɗaure manoman ne suka yi masu yankan rago
Sai dai babu wata sanarwa daga sojoji ko rundunar ƴan sanda game da harin.
Mayaƙan Boko Haram da mayakan ISWAP
na ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya duk da
iƙirarin hukumomi da jami’an tsaro na karya lagonsu.
Ƙasashen musulmi na taro kan yaƙi da ta’addanci a Nijar
Asalin hoton, OIC
Nijar na karɓar bakuncin taron ministocin harakokin wajen mambobin ƙungiyar
ƙasashen musulmi ta OIC karo na 47 a birnin Yamai.
Taron ministocin na ƙasashen musulmi na kwanaki biyu na tattaunawa ne kan taken
“hadin guiwa kan yaƙi da ta’addanci, don zaman lafiya da ci gaba.
Tun a ranar Juma’a aka buɗe taron a babban ɗakin taro na Mahatma Gandhi da
ke Yamai.
A labarin da ta wallafa game da taron jaridar ActuNiger ta ce, Shugaban ƙasa Mohamadou Issoufou ne ke jagorantar taron tare da sakatare janar na
ƙungiyar OIC Dr Yousef A. Al-Othaimeen da kuma wakilan ƙasashe mambobin
ƙungiyar 57.
An ƙashe mutum 22 a rikicin makiyaya da manoma a Chadi
Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni sun ce aƙalla mutum 22 kashe a kudancin Chadi sakamakon rikicin
makiyaya da manoma a yanzkin.
Kamfanin dillacin labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa an kafa dokar hana
fita a yankin Kabbia da rikicin ya faru inda aka kama mutum 66.
Bayanai sun ce rikicin ya samo asali ne bayan dabbobin makiyaya sun shiga
gonakin manoma.
Hukumomi sun ce mutum 11 da suka mutu a ɓangarorin ƙabilun biyu, bayan
harbinsu da mashi, yayin da kuma mutum 34 suka jikkata.
Ƙauyuka da dama ne kuma aka ƙone.
Iran ta buƙaci Birtaniya ta yi Allah wadai da kisan Fakhrizadeh
Jekadan Birtaniya ya buƙaci Birtaniya ta yi Allah wadai da kisan Fakhrizadeh masanin nukiliyarta.
Hamid Ba'idinejad, ambasadan Iran a London, ya buƙaci Birtaniya ta yi bayani kan kisan Mohsen Fakhrizadeh kuma ta yi Allah wadai da kisan.
"Kisan Dr Fakhrizadeh ƙwararren masanin kimiya ya saɓa dokokin duniya da keta haƙƙin ɗan Adam. Mun yi tunanin gwamnatin Birtaniya za ta fito da yi Allah Wadai da wannan babban laifin da kuma ɗaukar mataki ba tare da ɓata lokaci ba, kamar yadda Ba'idinejad ya bayyana.
A cewarsa Ba'idi Nejad, "Iran na da ƴancin ramuwar gayya."
Tattalin arzikin Najeriya zai ƙaru da kashi 2 a 2021 - CBN
Asalin hoton, Getty Images
Tattalin arzikin Najeriya zai farfaɗo da kashi 2 cikin 100 a shekarar 2021, a cewar gwamnan Babban Bankin Ƙasar ranar Juma'a.
Najeriya ta faɗa cikin matsalar tattalin arziki a watan Nuwamba sakamakon lahanin da annobar korona ta yi wa tattalin arzikinta da kuma faɗuwar farashin man fetur.
Sai dai Godwin Emefiele ya ce yana tsammanin matsalar ta zama ta ɗan lokaci.
Kazalika, ya ce yana sa ran hauhawar farashin kayayyaki ma za ta sauka a wata shidan farko na 2021.
Sannan ya kare tsare-tsaren harkokin sauyin kuɗin ƙasashen waje, yana mai cewa "ya yi daidai da na sauran ƙasashen duniya" domin an ƙyale naira ta yi wa kanta farashi a kasuwa.
Ya ƙara da cewa babu buƙatar a damu game da asusun ajiyar Najeriya na ƙasashen waje.
Dubban manoma na zanga-zanga a Indiya
Asalin hoton, Getty Images
Manoma a sassa daban-daban na Indiya na bayyana goyon baya ga takwarorinsu na jihohin Punjab da Haryana.
Manoman na ƙoƙarin yin tattaki zuwa Delhi don nuna adawa da sabuwar dokar mallakar gonaki da gwamnatin kasar ta samar.
A rana ta uku a jere, dubban fusatattun manoma na ci gaba da yin karo da 'yan sandan da suka hana su tsallakawa zuwa babban birnin tafe da tarakatocinsu.
Shugabannin kungiyar manoma na jihohin Uttar Pradesh da Uttarakhand sun lashi takobin shiga zanga-zagar.
Manoman na ganin cewa sabbin dokoki guda uku na mallakar gona da majalisar dokoki ta zartar za su yi matuƙar kawo musu cikas.
Borno: Gwamna Zulum ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen ƙananan hukumomi
Asalin hoton, @GovBorno
Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da ake gudanarwa a jihar yau Asabar.
Gwamnan tare da rakiyar jami'an tsaro ya jefa ƙuri'arsa ne a garin Mafa hedikwatar Ƙaramar Hukumar Mafa.
Asalin hoton, @GovBorno
A zaɓen na yau, ana sa ran za a zaɓi shugabannin ƙaramar hukuma 27 na jihar.
Jihohi da dama na ƙoƙarin gudanar da irin wannan zaɓe, ciki har da Kano wanda za a yi ranar 16 ga watan Janairu.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ware fiye da naira biliyan biyu domin gudanar da zaɓen a ƙaramar hukuma 44 na jihar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Tsohon mataimakin shugaban APC ya kai jam'iyyar kotu
Asalin hoton, APC
Tsohon mataimakin shugaban APC mai mulkin Najeriya wanda kuma ya shugabanci kwamitin riƙon jam'iyyar, Mister Hilliard Eta, ya kai jam'iyyar kotu yana neman a rusa kwamitin Mai Mala Buni.
Kazalika, Mista Eta na neman Babbar Kotun Tarayyar da ke Abuja da ta bayyana shi a matsayin muƙaddashin shugaban jam'iyyar.
Kwamitin Zartwarwar APC na Ƙasa (NEC) ya rusa kwamitin shugabancin jam'iyyar na ƙasa ranar 25 ga watan Yuni yayin wani taro da ya gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa ƙarƙshin jagorancin Adams Oshiomhole.
Yayin taron ne, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, aka naɗa kwamitin riƙo tare da Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni a matsayin shugaba.
Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da Mai Mala Buni a matsayinsa na shugaba, da John Akpan Udoedehe a matsayinsa na sakatare, da Gwamna Adegboyega Oyetola na Osun, da Gwamna Sani Bello na Neja da kuma Stella Okotete a matsayinsu na mambobin kwamitin.
Ita ma hukumar zaɓe ta INEC na cikin waɗanda ake ƙarar.
Masu ƙarar na ƙorafin cewa sashe na 183 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da Aya ta 17 (i), (iv) da kuma 20 (a), (b) na kundin tsarin APC sun haramta tsige zaɓaɓɓun shugabannin jam'iyyar.
Haka nan, suna ƙorafin cewa Kundin Tsarin Mulki na Najeriya da na APC sun haramta wa masu riƙe da zaɓaɓɓen muƙami na gwamnati su riƙe kowane irin muƙami a cikin APC.
Zuwa yanzu ba a saka lokacin fara sauraron ƙarar ba.
Iran na zargin Isra'ila da kashe mata masanin nukiliya
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Iran ya zargi Isra'ila da kisan babban ƙwararre kan shirin nukiliyarta ranar Juma'a, tana mai cewa ba za ta taɓa ja da baya ba game da shirin.
Hassan Rouhani ya kuma ce ƙasarsa za ta yi ramuwar gayya game da kisan Mohsen Fakhrizadeh a lokacin da ta zaɓa.
An kashe Fakhrizadeh ne a wani harin kwanton-ɓauna da 'yan bindiga suka yi a kan motarsa a garin Absard da ke gabashin birnin Tehran.
Isra'ila ba ta ce komai ba game da batun zuwa yanzu, amma ta taɓa zarginsa da jagorantar wani shirin ƙera makamin nukiliya a baya.
Fakhrizadeh ne mafi shahara a cikin masana kimiyyar nukiliya na Iran, wanda ya jagoranci shirin a ƙarƙashin ma'aikatar tsaro.
Kisan nasa ka iya ƙara rura wutar rikici kan shirin ƙera nukiliya da Iran ke yi tsakaninta da Amurka da sauran ƙawayenta da suka ƙulla yarjejeniya.
Zaɓen Nijar: Bazoum Mohammed na fatan lashe zaɓe a zagayen farko
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku ji tattaunawar Aliyu Abdullahi Tanko ya yi da ɗan takarar
Kusan wata guda ya rage a yi zaɓen shugaban ƙasa a Jamhuriyyar Nijar kuma hankali ya karkata ne kan batun wanda zai gaji shugaba Muhammadou Issoufou bayan ya ja ragamar kasar na tsawon shekara 10.
Daga cikin manyan ’yan takarar har da tsohon ministan cikin gidan Nijar, Bazoum Mohammed, wanda zai shiga zaɓe a tutar jam’iyyar PNDS mai mulkin kasar.
A filinmu na Gane Mani Hanya na wannan makon, Editan Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko wanda ke ziyarar aiki a Nijar, ya tattauna da Bazoum Mohammed dangane da shirinsa na tunkarar zaben.
'Yan jarida, 'yan sanda, sojoji ba za su kaɗa ƙuri'a ba a ranar zaɓe a Ghana
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zaɓen Ghana ta ce 'yan sanda da sojoji da 'yan jarida da direbobin motar ɗaukar marsa lafiya ba za su jefa ƙuri'a ba a zaɓen ranar 7 ga watan Disamba mai zuwa.
Hukumar Ghana Electoral Commission (GEC) ta ce waɗannan rukunin mutanen da ta lissafa na cikin masu kaɗa ƙuri'a na musamman da za su yi zaɓen tun 1 ga Disamba.
Tuni GEC ta wallafa sunayen waɗanda za su jefa ƙuri'ar a rana ta musamman ga mutanen da ke aiki na musamman, waɗanda kaɗa ƙuri'ar ka iya shafar aikinsu a ranar zaɓe.
Mutanen sun haɗa da 'yan sanda da sojoji da masu tuƙa motocin ɗaukar marasa lafiya da 'yan jarida da sauransu.
Sai dai hukumar ta gargaɗi waɗanda suka yi rajistar zaɓe na musamman cewa idan suka gaza kaɗa ƙuri'a ranar 1 ga wata to ba za su yi zaɓen ba ranar 7.
"Wajibi ne masu zaɓen su tabbatar cewa sun bi matakan da suka dace domin tantance bayanansu saboda gudun kar a haramta musu kaɗa ƙuri'a tun da GEC ba za ta bari su yi zaɓe ba ranar 7 ga wata," in ji hukumar.
Kotu ta sake watsi da ƙarar Trump kan sakamakon Pennsylvania
Wata babbar kotun ɗaukaka ƙara a Amurka ta yi watsi da ƙarar da tawagar kamfe ɗin Donald Trump ta shigar don neman a hana bayyana Joe Biden a matsayin wanda ya lashe Jihar Pennsylvania.
Tawagar alƙalai guda uku ta ce ƙarar ba ta cancanci a saurare ta ba, suna masu cewa ba a gabatar da wani takamaiman zargi ba ko kuma hujja.
Hukuncin wani babban koma-baya ne ga Trump wanda ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen na watan Nuwamba da Mista Biden ya lashe.
A ranar Alhamis Trump ya ce zai sauka daga mulki idan aka bayyana Biden a matsayin wanda ya yi nasara a hukumance.
Sai dai a ranar Juma'a kuma ya sake yin zarginsa maras hujja na "gagarumin maguɗi" a shafinsa na Twitter.
"Biden zai shiga Fadar White House ne kaɗai idan ya kawo hujjar cewa ƙuri'unsa '80,000,000 votes' ba ta hanyra maguɗi ya samu ba," in ji shi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Jami'an tsaro sun daƙile harin 'yan bindiga a kan hanyar Kaduna-Abuja
Asalin hoton, @samuelaruwan
Dakarun rundunar Operation Thunder Strike sun daƙile wani harin masu garkuwa da mutane a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a daren jiya Juma'a, a cewar gwamnatin Jihar.
Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ya fitar a Juma'a ta ce 'yan bindigar sun fito kan titin ne ta ɓangaren Kasarami da ke Ƙaramar Hukumar Chikun da misalin ƙarfe 7:38 na yamma.
Sanawar ta ce sojojin sun yi nasarar fatattakar 'yan fashin, inda wasu da yawa suka gudu da raunuka.
Sai dai lamarin ya jawo tsaiko ga matafiyan da ke kan hanyar a lokacin da abin ya faru, abin da ya sa gwamnatin jihar ta Kaduna ta nemi afuwar masu ababen hawa.
Babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja mai nisan kilomita 165, ta shahara wurin ayyukan masu garkuwa da mutane da kuma rasa rayuka sakamakon rashin kyanta.
Mako biyu da suka wuce an yi garkuwa da ɗaliban Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) guda tara a kan hanyarsu ta zuwa Legas sannan aka shiga cikin Kwalejin Nuhu Bamalli a Zariya, inda aka ɗauke malami.
Kazalika, an shiga har cikin gidan wani malamin jami'ar ta ABU tare da yin garkuwa da shi da matarsa da 'yarsa kafin daga bisani su saki iyalan nasa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.