Mutum 22 sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a Chadi
Mutum aƙalla 22 ne suka mutu sakamakon wani mummunan rikici da ya kaure tsakanin makiyaya Larabawa da manoma da ke zaune a yankin Kabbia da ke kudancin Chadi.
Ana kyautata zaton rashin jituwar ta samo asali ne daga satar shanu da take amfanin gona da ake samu tsakanin al'ummar biyu.
Ministan Sadarwar Chadi, Cherif Mahamat, ya fada wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa ƙauyuka da dama sun ƙone yayin rikicin na ranakun Litinin da Talata.
An kama mutum 66 kuma dokar hana fita ta fara aiki a yankin.
Rikici tsakanin ƙungiyoyin ya kunno kai a yankin Sahel da ke gabar Chadi tun tsawon shekaru da dama da suka gabata.