Wani mutum ya sassara uba da ɗansa a Kano

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Fifa ta dakatar da Ahmad shugaban Caf na tsawon shekaru biyar

    Shugaban Caf Ahmad

    Asalin hoton, Fadel Senna

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ta dakatar da shugaban ƙwallon Afirka Caf Ahmad na tsawon shekaru biyar saboda saɓa ka'idojinta na ɗa'a.

    An samu mataimakin shugaban na Fifa mai shekaru 60 da karya dokokin da suka shafi ɗa'a da bayar da kyauta da karɓa da kuma almubazzaranci da kuɗi.

    Sanarwar da Fifa ta fitar ta bayyana cewa "binciken da aka gudanar kan Ahmad daga 2017 zuwa 2019 kan shagubancin Caf da ya ƙunshi har da ɗaukar nauyinsa zuwa aikin hajji da kuma hulɗar Caf da wani kamfanin kayayyakin wasanni."

    An kuma ci Ahmad tarar dala 200,000. A baya ya musanta zargin da ake masa.

  2. Save the Children: Najeriya na cikin ƙasashe mafi hatsari ga yara ƙanana

    Save the Children

    Asalin hoton, @save_children

    Ƙungiyar agaji ta Save the Children ta bayyana Najeriya cikin jerin ƙasashe 12 mafi hatsari ga rayuwar yara ƙanana.

    A cikin rahotonda ta fitar ƙungiyar ta bayyana ƙasashe mafi hatsari ga yara ƙanana da suka haɗa da Syria da Somalia da Afghanistan da Yemen da Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Congo da Mali da Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Iraqi da Sudan da Sudan da Kudu da kuma Najeriya

    A cikin rahoton mai taken 'Zamani na take haƙƙin yara a yaƙi,”ƙungiyar Save the Children ta ce yara 25, kwatankwacin adadin yaran da ke cikin aji, ake kashewa ko raunata a kowace rana.

    Rahoton ya ce jimillar yara 93,236 aka kashe a yaƙi a shekaru 10, inda kuma sama da yara miliyan uku ke rayuwa a wuraren da ake rikici.

    Rahoton ya ce a Afghanistan aka fi kashe yara ƙanana a 2019. Najeriya kuma na cikin manyan ƙasashen da aka fi yi wa yara illa, ko da yake rahoton ya ce an samu raguwar adadin idan aka kwatanta daga 2018 zuwa 2019.

  3. Ƴan bindiga sun tarwatsa wani ƙauyen Zamfara

    Hare-haren Najeriya

    Asalin hoton, TWITTER/NIGERIAN ARMY

    Mazauna wani ƙauyen ƙaramar hukumar Maradun a Jihar Zamfara sun ce ƴan bindiga sun tarwatsa su bayan sun kai masu hari a ranar Lahadi.

    Wani mazauni ƙauyen na Aljumma ya shaida wa BBC cewa ƴan bindigar sama da 50 ne suka shigo ƙauyensu saman babura suka buɗe wuta.

    Sai dai ya ce jami’an tsaro da ƴan banga sun kore su amma daga baya suka dawo lamarin da ya ɗimauta mazauna ƙauyen suka shiga daji suka tsere.

    “Mutanen gari na watsewa mata da ƙananan yara,” in ji shi.

    Wannan na zuwa bayan ƴan bindigar sun shiga Dutsin Gari na yankin Kanoma a ƙaramar hukumar Maru inda suka saci mutane suna cikin sallah tare da kashe mutum biyar bayan sun saci shanu sama da 200.

    A ƴan kawanakin nan matsalar tsaro musamman ƴan bindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa ta yi ƙamari a arewacin Najeriya inda a ƙarshen mako an tsinci gawar shugaban Jam’iyyar APC na jihar Nasarawa bayan ƴan bindiga sun sace shi.

    AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya duba irin hare-haren ƴan bindiga da suka faru a ƙarshen mako a rahotonsa

    Bayanan sautiƳan bindiga sun tarwatsa wani ƙauye a Zamfara
  4. Ƴan tawayen Houthi sun ce sun kai hari wata cibiyar man Saudiyya

    ‘Yan tawayen Houthi a Yemen sun ce sun harba makamin roka da ya fada kan wata cibiyarmai a birnin Jeddah na Saudiyya.

    Babu wani tabbaci daga hukumomin Saudiyya, amma bidiyon da aka yaɗa a intanet ya nuna yadda hayaƙi ke tashi daga cibiyar man mallakar kamfanin man Saudiyya na Aramco.

    Wannan na zuwa kwanaki bayan Gwamnatin Trump ta ce tana tunanin sanya kungiyar Houthi a matsayin ta ƴan ta’adda.

    A ranar Juma'a, MajalisarƊinkin Duniya ta yi gargadin cewa duk wani yunƙuri irin wannan, barazana ne ga ƙoƙarin samar da zaman lafiya a Yemen a dai dai lokacin da ƙasar ke fuskantar yunwa mafi muni a duniya cikin shekaru da dama.

    'Yan tawayen Houthi sun sha kai wa Saudiyya hari da makamai masu linzami da jirage marasa matuka, yayin da sojojin Saudiyya suka kakkabo wasunsu da dama.

    Wani harin Houthi

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Gwamnan Rivers ya sanya dokar hana fita kan ƙungiyoyin asiri

    Gwamnan Rivers

    Asalin hoton, Rivers State

    Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a wasu sassan jihar kan ƙaruwar ayyukan ƙungiyoyin asiri.

    Gwamnan unguwar da ke babbar gadar Okoro-Nu-Odu za ta kasance cikin dokar na tsawon mako biyu.

    Amma dokar ba ta shafi ma’aikatan da ke aiki a babbar gadar ba.

    Gwamnan ya yi gargadin cewa za a hukunta duk wanda ya saɓa dokar da kuma ƙoƙarin kawo hargitsi ga zaman lafiya a jihar.

  6. Biden ya zaɓi sakataren harakokin wajensa

    Anthony Blinken

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanai sun ce zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden zai zabi Anthony Blinken a matsayin sakataren harkokin wajensa.

    Mista Blinken na da ƙyaƙyawan alaƙa kuma makusanci ne ga Mista Biden a tsawon kusan shekaru 20.

    Ya kasance wanda ke karfafa gwiwar ƙawance ko ƙula da harkoki da ƙasashe da dama, inda a farkon wannan shekarar yake cewa matsalolin irinsu sauyin yanayi, annobar korona da yaɗuwar makamai masu haɗari ba wanda Amurka ita kadai zata iya shawo kansu ba ne.

    Ya taba riƙe muƙamin mataimakin sakataren harkokin ketare a karkashin mulkin tsohon shugaba Barack Obama inda ya taimaka wajen inganta tsare-tsare da harkoki a gabas ta tsakiya.

    Mr Bilken mai shekara 58 ya yi karatu a Faransa, sannan ya yi Jami'ar Havard da makarantar shari'a ta Colombia.

  7. Ana matsin lamba ga Trump ya amince da sakamakon zaɓe

    Trump

    Asalin hoton, AFP/GETTY IMAGES

    Donald Trump na fuskantar matsi daga wasu manyan jam'iyyarsa ta Republican kan ya jingine ƙokarin da yake na ƙalubalantar nasarar da Joe Biden ya samu a zaɓen shugaban Amurka.

    Tsohon gwamnan New Jersey kuma makusanci ga Shugaban, Chris Christie, ya bayyana abin da tawagar lauyoyin Trump ke yi a matsayin wani abin zubar da mutunci kasa.

    Tsohon mai bai wa Mista Trump shawara kan lamuran tsaron ƙasa, John Bolton ya ce abin da shugaban ke yi tamkar buɗe kofa ko miƙa kasar a hannun makiyanta ne.

    Haka kuma tsohon wanda ke ba shi shawarar kan tsaron, McMaster ya ce halayen da Trump ke nuna wa tamkar da sa shakku ne tsakanin masu zaɓe.

    Sama da mako biyu da shan kaye a zaɓe, har yanzu Mr Trump na kan bakarsa cewa an murɗe masa nasararsa, sai dai ya gagara gabatar da shaida.

  8. Buɗewa

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin inda za mu shafe yinin Litinin muna kawo labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu domin sanin halin da duniya ta ke ciki da kuma samun labaran da suka shafe ku.