Fifa ta dakatar da Ahmad shugaban Caf na tsawon shekaru biyar
Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ta dakatar da shugaban ƙwallon Afirka Caf Ahmad na tsawon shekaru biyar saboda saɓa ka'idojinta na ɗa'a.
An samu mataimakin shugaban na Fifa mai shekaru 60 da karya dokokin da suka shafi ɗa'a da bayar da kyauta da karɓa da kuma almubazzaranci da kuɗi.
Sanarwar da Fifa ta fitar ta bayyana cewa "binciken da aka gudanar kan Ahmad daga 2017 zuwa 2019 kan shagubancin Caf da ya ƙunshi har da ɗaukar nauyinsa zuwa aikin hajji da kuma hulɗar Caf da wani kamfanin kayayyakin wasanni."
An kuma ci Ahmad tarar dala 200,000. A baya ya musanta zargin da ake masa.