Ƙarshen rahotannin kenan
Mun zo ƙarshen rahotanni kai-tsaye a wannan shafi. Da fatan za mu haɗu da ku gobe da safe domin ɗorawa daga inda aka tsaya.
Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Mun zo ƙarshen rahotanni kai-tsaye a wannan shafi. Da fatan za mu haɗu da ku gobe da safe domin ɗorawa daga inda aka tsaya.
Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.
Gwamnatin Tsibirin Solomon ta kare shirinta na haramta amfani da Facebook, matakin da ta ce zai kare hadin kan ƙasa mai mutum kusan 700,000.
Firaminista Manasseh Sogavare ya faɗa wa majalisa cewa kamata ya yi a kare matasa daga munanan kalamai a intanet.
Ya kuma yi watsi da zarge-zargen da ke cewa an ɗauki matakin ne domin rufe bakin masu suka.
Jagoran 'yan hamayya ya fada wa kafafen yaɗa labaran Australiya cewa shawarwarin hana amfani da Facebook abin takaici ne.
Kungiyar kare hakkin ɗan Adam ta Amnesty International ta ce ɗaukar irin wannan matakin "mummunan hari ne kan 'yancin dan Adam".
Sai dai matakin bai fara aiki ba sannan babu wasu bayanai kan yadda za a aiwatar da shi.
'Yar Ministan Sadarwa na Najeriya Isa Ali Pantami ta rasu a yau Litinin.
Aishah Isa Ali (Amal) ta rasu tana da shekara 13 da haihuwa, kamar yadda ministan ya sanar a shafinsa na sada zumunta.
"Saboda wasu uzururruka, jana'iza sai gobe (Talata) a Masallacin Annur bayan Sallar Azahar da karfe 1:15 na rana," in ji Pantami.
Ministan ya yi addu'ar "Allah Ya ji ƙan ta da iyayenmu".
Wani mutum ya sare kan wani magidanci tare da sassara ɗansa a ƙauyen Tumfafi na Ƙaramar Hukumar Garko da ke Jihar Kanon Najeriya.
Mutumin wanda har yanzu ba a kai ga gano ko wane ne ba, ya kutsa gidan Malam Nuhu Muhammad a daren jiya Lahadi sannan ya fille masa kai da adda.
Bayanan da wakilin BBC a Kano Zahraddeen Lawan ya tattaro sun nuna cewa lamarin ya faru ne kafin maƙwabta su ankara da abin da ke faruwa a cikin daren.
"Da misalin ƙarfe 2:00 na dare sai mahaifimmu ya tashe mu yake faɗa mana abin da ke faruwa, da ɗansa ya bi sahu domin ganin abin da ya faru da mahaifinsa sai shi ma mutumin ya sare shi a ka da hannu kuma ya kashe shi," a cewar wani maƙwabcin marigayin.
Ya ƙara da cewa ita ma matar marigayin da ƙyar ta tsallake bayan da maharin ya kai mata sara bai same ta ba.
Ga alama dai da ma akwai wata jiƙaƙƙiya tsakanin maharin da mamacin, kodayake kawo yanzu babu wani cikakken bayanin abin da ke tsakaninsu a hukumance.
Wasu 'yan bindiga sun sace ɗan uwan Ministan Noma da Cigaban Karkara na Najeriya Alhaji Sabo Nanono.
Mataimaki na musamman ga ministan, Umar Wali, shi ne ya tabbatar wa da BBC labarin, inda ya ƙara da cewa mutanen ɗauke da makamai sun shiga gidansu ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren Lahadi kuma suka tafi da Babawuro Tofai.
Rahotanni sun ce an jikkata wani yaro a gidan kafin su yi awon gaba da ɗan uwan ministan.
Lamuran tsaro na ƙara taɓarɓarewa a Najeriya, inda aka yi garkuwa da mutane da dama tun daga ƙarshen mako zuwa yau.
A yau ɗin, wasu 'yan bindigar suka shiga gidan wani malamin Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma suka yi awon gaba da shi da matarsa da 'yarsa kafin daga baya su saki iyalin nasa.
Wasu 'yan bindiga sun shiga tsakar gidan wani malamin Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria (ABU) da ke cikin jami'ar kuma suka yi awon gaba da shi da matarsa da 'yarsa, kamar yadda kakakin jami'ar Auwalu Umar ya shaida wa BBC.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:50 na daren Lahadi bayan 'yan bindigar sun dira gidansa da ke Samaru, a cewar wata sanarwa da Auwalu Umar ɗin ya fitar a yau Litinin.
"Hukumar tsaro ta jami'ar ta sanar wa da 'yan sanda nan take bayan samun kiran gaggawa kuma da 'yan bindigar suka ga an kusa kama su sai suka shiga daji da mutanen," in ji sanarwar.
"Bayan 'yan sanda sun bi su har zuwa ƙauyen Kasuwar Da'a da ke maƙwabtaka da jami'ar, sai suka saki matar da kuma 'yarsa sannan suka yi gaba da shi."
Auwal Umar ya ƙara da cewa an tsinci kwanson harsasai a wurin da aka yi musayar wuta da miyagun.
Lamarin na zuwa ne kwana biyu bayan an saki ɗaliban jami'ar ta ABU kusan 10 da masu garkuwa suka sace a kan hanyarsu ta zuwa kwas a Jihar Legas ranar 15 ga watan Nuwamba.
Ministan Lafiya da Rigakafi na Saudiyya Dr. Abdullah Al-Asiri ya ce za a yi wa mazauna ƙasar allurar rigakafin cutar korona kyauta.
"Saudiyya za ta karɓi rigakafin domin lafiyar al'umma, saboda haka ba ta saka ta cikin abubuwan da za a karɓi kuɗi a kansu ba," in ji ministan, a hirarsa da kafar Al-Ekhbariya.
Mista Al-Asiri ya yi fatan cewa za a samar da rigakafin ga kashi 70 cikin 100 na mazauna ƙasar nan da ƙarshen 2021.
Tun da farko, jaridar Saudi Gazette ta ruwaito Minista Al-Asiri na cewa Saudiyya na cikin ƙasashen G20 - ƙungiyar ƙasashe 20 mafiya girman tattalin arziki - na farko-farko da za su karɓi adadi mai yawa na rigakafin domin daƙile annobar cutar.
Jami'an lafiyar ƙasar sun haƙiƙance cewa Saudiyya za ta karɓi rigakafi ne kaɗai wadda aka tabbatar da ingancinta.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ƙara wa 'yan sanda 82,779 matsayi ciki har da 16 waɗanda ta ce an kashe su yayin zanga-zangar EndSARS a watan Oktoba.
Wata sanarwa da kakakin rundunar Frank Mba ya sanya wa hannu ta ce su ma guda 70 da aka jikkata yayin zanga-zangar sun samu ƙarin matsayi na musamman.
Sufeto Janar Mohammed Adamu ya ƙara wa jumillar 'yan sanda 82,779 girma zuwa matakin aiki na gaba.
Ƙarin girman ya shafi masu muƙamin Saja guda 56,779 zuwa Sufeto, da Kofur 17,569 zuwa Saja, sai kuma Kurtu 8,431 zuwa Kofur.
Mohammed Adamu ya ce ƙarin girman na cikin matakan da rundunar ke ɗauka na ƙarfafa wa 'yan sanda gwiwar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Matakin na zuwa ne wata guda bayan rushe rundunar SARS mai yaƙi da fashi da makami bayan matasan Najeriya sun tilasta wa gwamnati sakamakon zargin dakarunta da cin hanci da kuma kashe mutane ba bisa doka ba.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce 'yan sanda 16 aka kashe yayin da zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali a wasu jihohi bayan wasu 'yan daba sun ƙona ofisoshinsu da kuma ababen hawa.
Rikicin ya jawo ɓalla gidajen yari biyu a Jihar Edo, inda fursuna kusan 2,000 suka tsere.
Wata kotu a Ingila ta ɗaure wani matashi shekara biyu da rabi a gidan yari saboda kama shi da laifin sauke hotunan fille kai da kuma yadda ake kai harin ta'addanci a kwamfutarsa.
An kama Zakaria Yanaouri mai shekara 21 ne yayin wani samame a gidansu da ke Congreve Road, Worthing ranar 24 ga watan Fabarairu.
Ya amsa laifuka biyar ciki har da mallakar wasu bayanai da 'yan ta'adda ka iya yin amfani da su.
Mai Shari'a Philip Katz QC ya siffanta Yanaouri a matsayin mai tsattsauran ra'ayi wanda yake sauraron "abin da 'yan ta'adda ke faɗa".
Da yake yanke masa hukuncin zaman wata 32 a gidan yari, alƙalin ya yi watsi da iƙirarin Zakaria cewa ya kalli hotunan ne kawai "saboda ya ga abin da ake yi".
Ya ce masu farfaganda sun juyar da tunanin Yanaouri, wanda a baya mutumin kirki ne.
An kai samame kan gidansu ne bayan an dakatar da su shi da danginsa a kan hanyarsu ta komawa Saudiyya.
An ga abubuwan farfaganda na sauya tunani daga ƙungiyar Islamic State (IS) a wata kwamfuta sannan kowane sashe an yi masa kanu da "Dabarun Ta'addanci Kawai", a cewar kotun.
Gwamnatin Jihar Rivers a Najeriya ta sanya dokar hana fita ta awa 24 tsawon mako biyu a fadin jihar sakamakon aruwar ayyukan ƙungiyoyin asiri.
Gwamna Nyesom Wike ne ya sanar da sanya dokar yayin wani jawabi ga al'ummar jihar, yana mai cewa an cimma hakan ne bayan wani taron majalisar tsaro.
Wakilin BBC Umar Shehu Elleman ya ce yanki biyu da dokar ta fi shafa na Rumuokoroda da Rumuodomaya na da mahimmancin gaske a jihar sakamakon ta nan ne ake iya kaiwa ga babban filin jirgin sama na Fatakwal.
"A wani ɓangare na yunƙurin daƙile wannan ɗabi'ar, gwamnati ta saka dokar hana fita ta awa 24 tsawon mako biyu a kan yankin Gadar Sama ta Okoro-nodu har zuwa faɗin kilomita ɗaya daga Cocin Emmanuel Anglican, wadda za ta fara aiki daga Litinin 23 ga watan Nuwamba," in ji shi.
Isra'ila ta tura wakilanta zuwa Sudan a karon farko tun farfaɗo da hulɗarsu da gwamnatin Trump ta jagoranta, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Isra'ila suka ruwaito
Sai dai babu cikakken bayani game da ziyarar, amma a makon da ya gabata ministan leƙen asirin Isra'ila Eli Cohen ya ce wata ƙaramar tawaga da za ta je Sudan domin tattauna batutuwan tsaro.
Daga baya za a tura babbar tawaga domin tattauna batutwan hulɗar tattalin arziki, kamar yadda aka ruwaito shi yana cewa.
Sudan ita ce ƙasar larabawa ta uku haɗi da Haɗaɗɗiyar Daular Labarawa da kuma Bahrain da suka shirya da Isra'ila duk da adawar Falaɗinawa.
Sudan ta kasance babbar mai adawa da Isra'ila tun kafa ƙasar a 1948
Rigakafin korona da kamfanin Pfizer ya samar an bayyana cewa ɗan asalin Najeriya ne ya jagoranci samar da rigakafin a Amurka.
Ofishin jekadancin Amurka a Najeriya ya wallafa hoton likitan Dr Onyema Ogbuagbo a Twitter tare da cewa shi ya jagoranci samar da rigakafin korona na farko mai inganci a Amurka.
Onyema Farfesan magani ne da cuttuka masu yaɗuwa a Jami'ar Yale.
Ya yi digirinsa na farko a Jami'ar Calabar a 2003.
Ministan harakokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan, ya musanta rahotannin da ke cewa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gana da Yarima mai jiran gado a Saudiyya.
Ministan ya ce babu wata tattaunawa tsakaninsu kamar yadda ya faɗa a shafinsa na Twitter.
Sai dai kuma ya ce an yi tattaunawar tsakanin jami'an Amurka da Saudiyya.
Ƙungiyar lauyoyi a Kamaru ta nuna fusatarta dangane da abin da ta kira rashin mutunta aikinta da hukumomi suke yi, da kuma take haƙƙoƙin ƴaƴanta da jami’an tsaro suke yi.
Wannan furucin ya biyo bayan kama wasu lauyoyi biyu da aka yi a birnin Douala ana zarginsu da yin ɓatanci ga jami’an kotu, lamarin da ya kai ga a ranar 10 ga wannan wata lauyoyi da jami’an tsaro suka bai wa hammata iska a cikin kotu a Douala.
Wannan halin da aka faɗa ciki, ya kai ga kungiyar lauyoyi kiran yajin aiki a duk fadin kasa daga ranar 30 ga wannan wata zuwa lokacin da hali ya yi.
Wata babbar kotun tarayya ta bayar umurnin tsare Sanata Ali Ndume a gidan yarin Kuje saboda kasa kawo tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul, Abdulrasheed Maina.
Ndume wanda ke wakiltar Borno ta Kudu shi ya tsaya wa Maina aka bayar da belinsa wanda ake tuhuma da laifin sama da faɗi. Amma ya Maina ya kasa bayyana gaban kotu domin ci gaba da shiri’arsa.
Kafar Channels ta ruwaito cewa, Alƙalin kotun ya bayar da umurnin a tsare Ali Ndume har sai ya cika sharuɗɗan belin. Kotun ta kuma umurci gwamnatin tarayya ta sayar da gidan Sanata Ndume da ke Asokoro domin fitar da kuɗin da aka ƙayyade na belin naira miliyan 500.
Lauyan Ndume ya ce za su kalubalanci hukuncin na kotu.
Darajar Hannayen jari a Najeriya ta faɗi kasa warwas a ranar Litinin bayan alƙalumman da aka fitar sun nuna ƙasar ta samu koma-bayan tattalin arziki.
Haka kuma darajar naira ta ƙara faɗi a kasuwar bayan fage sakamakon ƙarancin dala a kasuwar.
Najeriya ta sake faɗawa cikin matsalar tattalin arziki karo na biyu a cikin shekaru huɗu. Kuma alkalumman da aka fitar sun dora laifin kan tasirin annonar korona da kuma faɗuwar farashin mai a kasuwar duniya.
Ana sayar da dala ɗaya kan naira 484 a kasuwar bayan fage a ranar litinin, a farashin gwamnati kuma 381
Jam’iyyun siyasa 45 sun ƙulla ƙawance inda suka mara wa ɗan takarar jam’iyya mai mulki baya kuma tosohon ministan cikin gida Bazoum Mohamed a zaɓen 27 ga watan Disamba, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar na Agence Nigeriennede Presse ya ruwaito.
An ƙulla Ƙawancen jam’iyyun ne da aka kira ‘Bazoum 2021’ a ranar Asabar a Yamai babban birnin ƙasar, kamar yadda kafar ta ruwaito.
"Zan samu amincewar ku, kamar yadda Shugaba Issoufou Mahamadou ya samu amincewarku da kuma amincewar dukkan al'ummar kasar," kamar yadda Bazoum ya tabbatarwamagoya bayansa.
Zaɓen zai kasance na farko da gwanatin farar hula ta jagoranci zaɓen kuma za ta mika mulki ga wata gwamnatin farar hula tun samun ƴancin kai a 1960.
Shugaba Issoufou wanda ke kammala wa’adin mulkinsa na biyu ana sa ran ya mika mulki ga wanda zai gaje shi a ranar 2 ga Afrilu.
Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce Firaminista Benjamin Netanyahu, ya tafi Saudiyya a asirce a ranar Lahadi
An ruwaito cewa ya gana da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, da Sakataren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo.
An kuma bayyana cewa taron ya kunshi har da shugaban hukumar leƙen asirin Isra'ila da cikin tawagar.
A cikin wani bayani a Twitter, daga daga cikin masu ba Netanyahu shawara ya nuna cewa ziyarar ta faru ba tare da bayar da tabbaci a hukumance ba
Gwamnatin Trump na son janyo ra'ayin Saudiyya ta shirya da Isra'ila.