Trump na fuskantar cikas a ƙalubalantar sakamakon zaɓe da yake yi

Asalin hoton, Getty Images
Donald Trump ya sake fuskantar gagarumin koma-baya a ƙalubalantar sahihancin sakamakon zaɓen shugabancin Amurka da yake yi, wanda Joe Biden ya lashe.
'Yan majalisar Jihar Michigan na jam'iyyar Republican ta Trump sun faɗa wa shugaban cewa jihar za ta tabbatar da sahihancin sakamakonta ranar Litinin bayan Mista Trump ya gayyace su Fadar White House.
Wakilan sun ce ba su samu wasu gamsassun bayanai da za su iya yin watsi da nasarar da Joe Biden ya samu ba a Jihar, don haka dole a jingine duk wata matsala da za ta haifar da barazana.
Kafin wannan lokaci, Gwamnan Georgia na Jam'iyyar Republican Brain Kemp ya tabbatar da Biden a matsayin wanda ya lashe kuri'un wakilan zaɓen Jihar, bayan jami'ai sun tabbatar da sahihancin nasarar ɗan takarar na jam'iyyar Democratic.

