Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An kama mutum biyu bisa zargin cin naman 'yan sandan da suka ƙona a Oyo

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Lahadi idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan labaran da muka wallafa ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. Shugaban Lebanon ya koka kan cin hanci da rashawa

    Shugaban ƙasar Lebanon, Michel Aoun, ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ya yi wa ƙasar katutu, haka zalika, ya yi zargin cewa ƙasashen ƙetare na katsalandan kan harkokin mulkin ƙasar.

    Ya bayyana hakan ne a yayin da yake yi wa ƙasar bayani, a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar matsin tattalin arziƙi.

    Mista Aoun ya sha alwashin tabbatar da binciken ƙwaƙwaf a babban bankin ƙasar domin bankaɗo cin hanci da kuma buɗe hanyar kawo sauyi.

    A ranar Juma'a ne aka bayar da rahoton cewa wani kamfani da ke gudanar da bincike kan ayyukan babban bankin ya dakatar da binciken sakamakon bai samu cikakkun bayanai ba ko kuma haɗin kan da yake buƙata.

    Masu sharhi na zargin cewa shi kansa Mista Aoun na da jari mai tsoka a wani kamfani da 'yan Lebanon din da dama suke ganin cewa yana tattare da cin hanci.

  3. Tarihin Shehu Usman Ɗan Fodio

  4. Dakarun Ethiopia na ci gaba da kutsawa yankin Tigray

    Gwamnatin Ethiopia ta ce dakarunta sun kara samun nasarar kutsawa arewacin yankin Tigray, tare da kwace garin Adgrat daga hannun mayakan yankin.

    Mayakan yankin na Tigray sun ce ana ta kashe fararen hula a wannan rikici, amma ba su gabatar da wata hujja ba da za ta tabbatar da hakan.

    Ganin cewa an katse hanyoyin sadarwa a yankin, yana da wahala a tantance irin waɗannan zarge-zargen.

    Tuni dai ƙungiyar tarayyar Afrika ta aike da wasu tsofaffin shugabannin ƙasashe uku domin su shiga tsakanin, yayin da MDD ke ci gaba da kiran a tsaigaita wuta domin kai kayan agaji cikin yankin.

  5. An kama mutum biyu bisa zargin cin naman 'yan sandan da suka ƙona a Oyo

    Rundunar 'yan sanda reshen jihar Oyo, ta tabbatar da kama mutum biyu kan zarginsu da cin gasashen naman 'yan sandan da aka ƙona yayin zanga-zangar EndSars.

    BBC ta tuntuɓi mai magana da yawun 'yan sandan jihar Oyo, Fadeyi Olubenga, inda ya tabbatar da cewa an tasa ƙeyar mutum biyun a yau Asabar a Ibadan babban birnin jihar.

    Ya ce an ƙaddamar da binciken neman waɗanda suka yi wannan aika-aikar ne bayan wani bidiyo da aka rinƙa yaɗawa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda mutane suka kashe 'yan sanda da ƙona su, da amfani da adda suna daddatsa naman su suna ci.

    Ya kuma bayyana cewa an tafi da waɗanda ake zargin zuwa hedikwatar 'yan sanda da ke Abuja domin ci gaba da gudanar da bincike.

  6. Covid-19: Iran ta ƙara saka matakai masu tsauri a ƙasar

    Hukumomi a Iran sun sake fito da wasu sabbin tsare-tsare masu tsauri a yunƙurinsu na yaƙi da abin da suka kira "bullar korona karo na uku".

    A yanzu haka dai an bayar da umarni ga duka shagunan da ba na sayar da muhimman kayayyaki ba a faɗin birane 160 da su kulle.

    Haka kuma za a hana motoci shiga da fita biranen da aka tsaurara dokar.

    Iran ce ƙasar da wannan cuta ta fi yi wa ɓarna a yankin Gabas Ta Tsakiya. Sama da mutum 40,000 ne suka mutu a ƙasar sakamakon annobar, sai dai wasu na ganin adadin mamatan ya wuce hakan.

  7. An kama 'yar wasan fim ɗin Indiya Bharti Singh kan tabar wiwi

    Hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a birnin Mumbai na Indiya ta kama 'yar wasan barkwancin nan, Bharti Singh, a gidanta a safiyar yau.

    An yi awon gaba da ita bayan an samu tabar wiwi a gidanta inda. Haka kuma jami'an sun gayyaci mai gidanta, Haarsh Limbachiyaa, domin amsa tambayoyi.

    Kamun nata na zuwa ne a daidai lokacin da ake gudanar da bincike mai zurfi kan zarge-zargen da ake yi na amfani da miyagun ƙwayoyi a masana'antar Bollywood.

    Ms Singh dai ta yi fice a irin rawar da take takawa a fina-finan barkwanci.

    An dai fara gudanar da irin wannan binciken ne tun bayan mutuwar ɗan wasan Bollwood ɗin nan, Sushant Singh Rajput, a watan Yuni inda mutuwarsa ta sa aka kai samame gidajen masu harkar fim da nishaɗantarwa a ƙasar.

  8. Za a bar matan Saudiyya su shiga harkokin yawon buɗe ido

    Gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewa a hanzu an ba mata dama su shiga harkokin yawon buɗe ido wanda hakan ya haɗa da shirya yawon da kuma gayyatar wasu daga ƙasashen waje.

    Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa an saka wannan dokar ne a ranar Juma'a, kuma gwamnatin ƙasar ta yi haka ne domin bai wa mata damar samun ayyukan yi.

    Ƙarƙashin wannan tsarin, matan ƙasar da za su shirya yawon buɗe ido na da damar bayar da hayar mota da kuma hayar masauki da nishaɗantarwa da kuma kula da wuraren da masu yawon buɗe ido za su je a ƙasar.

    Sai dai a sharuɗan da ƙasar ta bayar, dole ne mai kamfanin da zai shirya yawon buɗe ido ya zama asalin ɗan ƙasar Saudiyya ne, mace ko namiji, ko kuma mai zuba jari a ƙasar da ke da lasisi, kamar yadda dokar ta ce.

    A 'yan shekarun nan dai an bai wa mata damar yin abubuwa da dama kamar tuƙin mota da zuwa kallon ƙwallo da fita ba tare da muharrami ba.

    Matakan sun jawo ce-ce-ku-ce daga ƙasashe daban-daban na Musulmi da ma wasu 'yan ƙasar na Saudiyya

  9. 'Titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maraɗi alheri ne ga Nijar'

  10. Hare-haren roka sun kashe mutum takwas a Kabul

    Mutum aƙalla takwas ne suka mutu wasu fiye da 30 suka jikkata sakamakon harin rokoki da aka kai rukunin gidaje a birnin Kabul na Afghanistan.

    Roka fiye da 12 aka harba daga wata mota zuwa cikin birnin, a cewar ma'aikatar harkokin cikin gida.

    Ƙungiyar IS ta yankin ta ɗauki alhakin harin, wanda aka kai awanni kafin tattaunawa tsakanin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo da wakilan ƙungiyar Taliban.

    A farkon makon nan ne gwamnatin Donald Trump ta sanar da cewa za ta janye dakaru 2,000 daga Afghanistan nan da watan Janairu.

    An soki matakin da cewa gaggawar janye su za ta jawo daƙile shirin gwamnatin ƙasar na kawo ƙarshen ta'addanci daga ƙungiyoyin 'yan bindiga.

    Masu sharhi da dama na ganin sojojin Afghanistan ba su da ƙarfin yin yaƙin da kansu idan sojojin ƙasashen waje suka fice.

  11. An naɗa Amina Sani Daura shugabar ƙwallon ƙafar mata ta Najeriya

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF ta tabbatar da naɗin Amina Sani Zangon Daura a matsayin sabuwar shugabar ƙwallon ƙafar mata ta Najeriya.

    NFF ta bayyana cewa Amina za ta maye gurbin Ruth David bayan wani kamfani mai suna Philiphs Consulting - wanda aka bai wa aikin zaɓo kociyar - ya bayar da shawarar ɗaukarta.

    "Amina Daura ta nuna hazaƙarta wurin cigaban ƙwallon mata tun daga tushe zuwa matakin ƙasa baki ɗaya kuma ta tabbatar wa kwamitin zaɓen irin ƙwarewarta," a cewar sanarwar da Ademola Olajire ya sanya wa hannu.

    Mutum 11 ne suka nemi aikin jan ragamar tawagar ta Super Falcons, ciki har da 'yan Najeriya guda bakwai, a cewar NFF.

    Sabuwar shugabar na da ƙwarewar fiye da shekara 15 kuma ta yi aiki ne da ƙungiyar Helping Hands Foundation for Child Education kafin zamanta kociyar tawagar.

    "Za ta jagoranci tabbatar da bunƙasa ƙwallon mata a kowane mataki tare da taimaka wa kociyan tawagar mata da kuma samar da damarmaki ga matan da haɓaka iliminsu," a cewar Olajire.

  12. Ana zanga-zangar kisan wani baƙar fata a Brazil

    Masu fafutikar adawa da wariya a Brazil na zanga-zanga a gaban babban kantin Carrefour bayan ƴan sanda sun aikata ƙazamin kisa kan wani mutum baƙar-fata da ke aiki a kantin.

    A kudancin birnin Porto Alegre, inda lamarin ya faru a daren Alhamis, 'yan sanda sun yi amfani da ƙarfi wajen tarwatsa dubban masu zanga-zangar. A Sao Paulo ma, an lalata rukunin kantunan Carrefour.

    Mutumin da jami'an tsaron suka kashe ɗan shekara 40 ne mai suna Joao Alberto Silveira Freitas. An cafke masu kula da kantin da Carrefour ta kora.

    Sai dai Mataimakin Shugaban Brazil, Hamilton Mourao ya alakanta kisan da rashin ƙwarewa irinta jami'an tsaro sannan ya dage kan cewa ba a nuna wariya a Barzil.

  13. Joe Biden na barar kuɗin shirin karɓar gwamnati

    Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Joe Biden na neman kuɗin gudanar da shirinsa na karɓar gwamnatin ƙasar saboda Trump ba ya bayar da haɗin kai domin miƙa mulki ga tawagarsa.

    Cikin wata yekuwar neman tallafi da Biden ya wallafa a shafinsa na Twitter, ana neman magoya baya ne da su tara kuɗin saboda Donald Trump ya ƙi amsa shan kaye.

    "Ga abin da zai faru: Saboda Shugaba Trump ya ƙi amsa shan kaye kuma yana jan ƙafa wurin miƙa mulki, ya zama dole mu tara kuɗin da kammu," in ji Biden.

    "Muna buƙatar taimakonku, idan za ku iya ku taimaka wa shirin Biden da Harris [mataimakiyarsa]."

    A gefe guda kuma, Donald Trump ya sake fuskantar gagarumin koma-baya a ƙalubalantar sahihancin sakamakon zaɓen da yake yi.

    'Yan majalisar Jihar Michigan na jam'iyyar Republican ta Trump sun faɗa masa cewa ba su samu wasu gamsassun bayanai da za su iya yin watsi da nasarar da Joe Biden ya samu ba a Jihar, don haka dole a jingine duk wata matsala da za ta haifar da barazana.

    Kafin wannan lokaci, Gwamnan Georgia na Jam'iyyar Republican Brain Kemp ya tabbatar da Biden a matsayin wanda ya lashe kuri'un wakilan zaɓen Jihar, bayan jami'ai sun tabbatar da sahihancin nasarar ɗan takarar na jam'iyyar Democratic.

  14. Ɗan Kenya ya samu ladan 400,000 na lashe gasar gudu ta Jihar Kaduna

    Ɗan ƙasar Kenya John Muiruri Mburu ne ya zama zakara a gasar gudun famfalaƙi ta duniya da ake yi a Kaduna ɓangaren tseren kilomita 21, a cewar rahoton shafin www.kick442.com.

    An ƙaddamar da gasar ce mai suna Kaduna Marathon, wadda ta ƙunshi ajin tseren kilomita 10km da 5km da kuma 21kma, a yau Asabar.

    An bai wa John Mburu dala 10,000 (kwatankwacin kusan naira 400,000) a matsayin kyautar zama zakara.

    A sauran azuzuwan gasar, Mohammed Sani Musa na Kaduna ne ya lashe gasar gudun kilomita 5km.

    Ita kuma Kangyang Solomon ta Jihar Filato ta lashe ɓangaren mata na gudun kilomita 10km, yayin da ɗan shekara 15 Gyang David ya lashe tserensa na farko a matakin ƙasa.

    Shugaban ƙungiyar wasan ƙwallon Volleyball ta Najeriya, Injiniya Musa Nimrod wanda ya halarci gasar, ya yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna da Nilayo Sports game da yadda suka shirya gasar.

    Wasu daga cikin manyan 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle da suka fafata sun haɗa da Shehu Mu’azu da Ismael Sadjo da kuma Danjuma Gyang.

    Kusan mutum 7,000 ne suka nemi shiga gasar ta Kaduna Marathon 2020.

  15. 'Umarni kawai ake jira na fara amfani da rigakafin korona'

    Kamfanin Pfizer na Amurka da ke samar da magunguna da abokin huldarsa BioNTech sun ce umarni kawai suke jira na amincewa da fara aiki da rigakafinsu na Korona.

    Hukumar tantace sahihancin abinci da magunguna ta kasar ta ce tana fatan amincewa da soma bayar da rigakafin daga tsakiyar Disamba.

    Pfizer da BioNTech sun ce a shirye suke su soma rarraba rigakafin da zarar an ba su dama.

    Sai dai wakiliyar BBC kan kiwon lafiya ta ce har yanzu akwai jan aiki wajen wadatuwar rigakafin don amfanin kowa.

    Ta ce akwai sharuɗɗan da sai an cika su kafin a amince da soma amfani da rigakafin kuma waɗanan sharuɗɗan kamfanin ke kokarin ganin ya cika a Amurkar da sauran ƙasashen EU da ma Burtaniya.

  16. 'Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya kusa da tashar jirgin ƙasa ta Kaduna

    Wani hari da 'yan bindiga suka kai a Rigasa mai tashar jirgin ƙasa a Jihar Kaduna ya yi sanadiyyar kashe mutum ɗaya a daren jiya Juma'a.

    Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa ba su yi barci ba a daren jiya, inda suka tsere zuwa cikin gari da iyalansu sakamakon harbe-harbe da aka ɗauki lokaci ana yi tsakanin 'yan bindigar da jami'an tsaro.

    Kwamared Muntari Sale ya ce an yi jana'izar wanda aka kashe sannan kuma ɗaya yana kwance a asibiti sakamakon harbin da aka yi masa, yayin da mutanen suka yi garkuwa da wani mutum ɗaya.

    "Sun zo da misalin ƙarfe 8:00 na daren Juma'a a nan Titin Turaki kuma saboda muna kusa da wurin sai muka gudu cikin gari muka nemi mafaka," in ji Muntari Sale.

    Babu wata tazara mai nisa tsakanin wurin da aka yi artabun da kuma tashar jirgin ƙasa ta Rigasa, wadda mutane ke rige-rigen zuwa domin tsira daga tarkon masu garkuwa da matafiya a kan titin Abuja zuwa Kaduna.

    Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun isa wurin ne a kan babura masu yawa, inda suka farfasa motocin 'yan sanda.

    Ya zuwa yanzu gwamnatin Kaduna ba ta ce komai ba game da harin.

    Tsakanin Litinin zuwa yau Asabar, an samu rahoton mutum kusan 20 da aka kashe a Jihar Kaduna, ciki har da Hakimin Gidan Zaki da ɗansa a Zangon Kataf.

    A ranar Litinin, 'yan bindiga sun kashe mutum 12 a Albasu ta Ƙaramar Hukumar Igabi tare da raunata wasu da dama.

  17. Babban ɗan Trump ya kamu a cutar korona

    Babban ɗan Donald Trump ya kamu da cutar korona, a cewar mai magana da yawunsa.

    Gwaji ya nuna Donald Trump Jr, mai shekara 42 ya kamu da cutar ne a farkon wannan makon kuma yana killace a wani gidansa na farauta tun bayan hakan.

    "Bai nuna wata alamar cutar ba zuwa yanzu kuma yana bin dukkanin umarnin likitoci," a cewar wata sanarwa.

    Donald Trump Jr ne na biyu a cikin 'ya'yan shugaban da suka kamu da cutar.

    A watan da ya gabata ne Barron Trump mai shekara 14 ya kamu da cutar, amma nan da nan ya warke.

    Ɗan farin na Shugaba Trump ya taka muhimmiyar rawa yayin yaƙin neman zaɓen mahaifinsa a takarar shugaban ƙasa da aka yi.

  18. Gwamnatin Najeriya ta amince da buƙatun ASUU

    Bayan shafe watanni ana tattaunawa da kuma jan-ƙafa, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta amimnce da buƙatar ƙungiyar ASUU ta malaman jami'a.

    Gwamnati ta cire ASUU daga tsarin biyan albashi na Integrated Payroll and Personnel Information System (IPPIS) sannan kuma za a biya albashin malaman da aka riƙe saboda ba sa aiki.

    Da yake magana bayan kammala tattaunawar awanni a jiya Juma'a, Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya ce Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan bashin albashin malaman na watan Fabarairu zuwa Yunin 2020 ta tsohon tsarin biyan albashin.

    Ya ƙara da cewa gwamnati ta yi tayin ƙara yawan alawus da ake bai wa malaman daga biliyan 30 zuwa 35 tare da ƙara yawan kuɗin da ASUU ta nema na farfaɗo da jami'o'i daga biliyan 20 zuwa 25.

    "Kuma muna sake duba yadda za a biya malaman kan tsohon tsarin albashin har zuwa lokacin da sabon tsari na UTAS zai kammala," in ji shi.

    "Sannan mun amince cewa albashin da ba a biya ba yana cikin dokar ‘no work, no pay’ wato 'ba aiki ba albashi' wadda aka fara aiki da ita, amma ni da Ministan Ilimi muna ƙoƙarin samun amincewa domin cire takunkumin."

    Ana sa ran wannan matsaya tasu za ta kawo ƙarshen yajin aikin wata takwas da malaman jami'ar ƙarƙashin ƙungiyar Academic Staff Union of Universities (ASUU) suka shafe suna yi.

    Tuni ɗaliban jami'o'i masu zaman kansu suka koma azuzuwa domin cigaba da ɗaukar darussa.

  19. MDD za ta tsugunar da masu guje wa yaƙi 200,000 a Ethiopia

    Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres ya bukaci a samar da mafakar jinƙai domin taimaka wa farar hula da suka maƙale a yaƙin yankin Tigray na Ethiopia

    Babban sakataren ya yi gargaɗi kan matsanancin hali da tasirin da wannan yaƙi tsakanin gwamnatin tarayyar Ethiopia da kuma gwamnatin yankin Tigray ka iya haifarwa.

    A lokacin da yake magana a birnin New York, Mista Guterres ya ce gwamnatin Ethiopia ta yi watsi da duk wani kokari na shiga tsakani kuma ana ci gaba da gwabza yaƙi da ke sanadin rayukan daruruwan mutane.

    MDD na shirin karbar ƴan gudun hijira kusan 200,000 a maƙwabciyar ƙasar Sudan a watanin masu zuwa. Yanzu haka akwai mutum 30,000 da suka shiga ƙasar.

    Afirka ta Kudu da ke jagorancin ƙungiyar hadin-kan Afirka ta AU na kokarin tura wakilan wanzar da zaman lafiya yankin domin sasanci.

  20. An fara gasar gudun famfalaƙi ta duniya a Jihar Kaduna

    Tuni aka buɗe gasar gudun famfalaƙi ta duniya a yau Asabar, 21 ga watan Nuwamban 2020 a birnin Kadunan Najeriya, wadda jihar ta shirya.

    Tsohuwar tauraruwar gasar Olympics a Najeriya, Mary Onyali ce ta ƙaddamar da gudun kilomita 21, wanda shi ne babban ɓangare na gasar.

    Su ma mata ba a bar su a baya ba domin kuwa tuni suyka fito a safiyar yau ƙarƙashin jagorancin Rabi Saulawa, shugabar ƙungiyar Jam'iyyar Matan Arewa.

    Sai dai su tattaki suke yi domin kiraye-kirayen kawo wasu matsaloli da ke damun al'umma kamar shan miyagun ƙwayoyi.

    Daga cikin wadanda suke shiga gasar akwai tsohuwar tauraruwar gasar Olympics a Najeriya, Mary Onyali.

    Kazalika, akwai gwanayen tsere 23 daga ƙasashen Afrika guda tara da suka isa Kaduna.

    Gwanayen da suka fito daga ƙasashe irin su Kenya da Kamaru da Habasha da dai sauransu, na cikin shauƙi da farin cikin wannan gasa da za a samu kyaututtuka.

    Sai dai za a gudanar da wannan gasar a dai-dai lokacin da al'ummomi ke nuna damuwa kan taɓarɓarewar sha'anin tsaro a Kaduna.