Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An kama mutum biyu bisa zargin cin naman 'yan sandan da suka ƙona a Oyo

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Trump na fuskantar cikas a ƙalubalantar sakamakon zaɓe da yake yi

    Donald Trump ya sake fuskantar gagarumin koma-baya a ƙalubalantar sahihancin sakamakon zaɓen shugabancin Amurka da yake yi, wanda Joe Biden ya lashe.

    'Yan majalisar Jihar Michigan na jam'iyyar Republican ta Trump sun faɗa wa shugaban cewa jihar za ta tabbatar da sahihancin sakamakonta ranar Litinin bayan Mista Trump ya gayyace su Fadar White House.

    Wakilan sun ce ba su samu wasu gamsassun bayanai da za su iya yin watsi da nasarar da Joe Biden ya samu ba a Jihar, don haka dole a jingine duk wata matsala da za ta haifar da barazana.

    Kafin wannan lokaci, Gwamnan Georgia na Jam'iyyar Republican Brain Kemp ya tabbatar da Biden a matsayin wanda ya lashe kuri'un wakilan zaɓen Jihar, bayan jami'ai sun tabbatar da sahihancin nasarar ɗan takarar na jam'iyyar Democratic.

  2. Ƙarin mutum 143 sun kamu da cutar korona a Najeriya

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu karin mutum 143 da suka kamu da cutar korona a ranar Jumma'a a ƙasar.

    Jihar Legas ce ke da adadi mafi yawa da mutum 70 da suka kamu, sai Kaduna mai mutun 25 da kuma Abuja mai 22, da kuma Ogun mai 11.

    Jihar Plateau da Oyo na da mutun 4-4 da suka kamu a kowaccensu, yayin da Ekiti ke da mutum 3.

    Sauran jihohin sun haɗa da Osun wadda ke da mutum 2, da jihohin Edo da Kano masu mutum 1-1 a kowaccensu.

    Da wannan sabbin alkaluman, jimillar waɗanda cutar ta kama a Najeriya sun kai 65,982, inda aka sallami mutum 61,782 bayan sun warke, sai kuma mutum 1,165 da suka mutu.

  3. Maraba

    Umar Mikail ke muku maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye a wannan hantsi na Asabar.

    Ku biyo ni daga yanzu zuwa yammaci kafin na fice. Ina fatan an fara hutun ƙarshen mako lafiya.