Yadda mahara suka kashe mutum 16, suka lalata dukiya a jihar Kaduna

An wallafa

Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta tabbatar da kashe aƙalla mutum goma sha shida a wasu yankuna na jihar tsakanin ranar Litinin zuwa Talata.

Lamarin ya faru ne a ƙananan hukumomin Zangon Kataf, Igabi da kuma Giwa.

Sanarwar da Kwamishin Tsaron Cikin Gida na jihar Samuel Aruwa ya aike wa manema labarai ta ce 'yan bindiga sun kashe Hakimin garin Gidan Zaki da ke Masarautar Atyap ta Ƙaramar Hukumar Zango Kataf, Haruna Kuye tare da ɗansa Destiny Kuye ranar Talata.

A ɓangare guda, Mr Aruwan ya ce jami'an tsaro sun ba su rahotannin kisan mutum biyu da sace wasu da dama a harin da 'yan bindiga suka kai a ƙauyukan Fatika, Ƙaya da kuma Yakawada da ke ƙaramar hukumar Giwa.

Kazalika, gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kisan mutum 12 a ƙauyen Albasu da ke ƙaramar hukumar Igabi a harin da suka kai ranar Litinin.

Mutanen da aka kashe su ne:

Amadu Mallam Idi GefefeIsah GomaAwwalu GomaBabangida IliyasuLado IliyasuYa'u JumareHamza Umaru Shehu JibrilTukur AlbasuMusa Adamu Muruzuwa Mr Aruwan ya ƙara da cewa suna tsammanin an kashe wata mata da ba a kai ga sanin ko wace ce ba.

Gwamnatin jihar ta Kaduna ta ce jami'an tsaro na ci gaba da sintiri a yankunan ƙananan hukumomin da lamarin ya faru.

Yadda lamarin ya faru a Albasu

Tun da fari mai unguwar Albasu Alhaji Nuhu Abubakar ya tabbatar da kisan aƙalla mutum 12 a harin na ranar Litinin baya ga fashi da kuma lalata dukiya mai yawa.

Ya ce an kai harin ne da misalin ƙarfe 12:30 na ranar ta Litinin.

Ya ƙara da cewa babu zato babu tsammani "kawai muka ga babura suna shigowa babu adadi ɗauke da maharan masu yawan gaske, kuma ba su yi wata wata ba su ka fara harbe-harbe a cikin ƙauyen namu."

"Kuma minti biyar da shigowarsu muka buga wa jami'an tsaro waya suka ce suna shirin zuwa, amma har tsawon awanni babu wani ɗauki da muka samu'.

"Sai ma wasu yan sanda da ke tsaron wani gidan gona da ke makwabtaka damu su ne suka kawo dauki, bayan sun fara harbi ne daga nesa sai maharan suka gudu.

"Daga baya ne jami'an tsaro su ka shigo kauyen bayan maharan sun dade da tafiya, aka yi wa gawa goma 12 Sallah".

Baya ga asarar rayukan da su ka samu, Alhaji Nuhu Abubakar ya ce maharan sun kwashe musu shanu da babura sun kuma lalata musu dukiya mai yawa.

A kan haka mai anguwar ya bukaci gwamnati da ta taimaka ta tsare musu rayukansu, inda a cewarsa sun hakura da batun samar musu da ababen more rayuwa.

Ko a ranar Lahadi 'yan bindiga sun kai hari a maraban Kajuru, inda suka sace mutum biyu tare da kashe wani mutun daya, kamar yadda yake dauke a sanarwar da ma'aikatar tsaron cikin gida ta jihar Kaduna ta fitar.

Bugu da kari sanarwar ta ambato batun sace daliban jami'ar Ahmadu Bello da ke da ke Zaria su takwas a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kuma fashi da makami na dada karuwa a arewa maso yammacin Najeriya, musamman jihohin Kaduna da Katsina da kuma Zamfara.