Kwamishinan Lafiya na Jihar Kogi, Saka Audu, ya ce waɗanda suka mutu sakamakon wata baƙuwar cuta a Jihar Enugu ne da ke maƙwabtaka da jiharsa.
Yayin hirarsa da kafar Channels TV, kwamishinan ya ce mutum 46 ne suka mutu, ba 50 ba kamar yadda rahotanni suka ce da farko.
A jiya Talata ne Majalisar Dokokin Kogi da ke tsakiyar Najeriya ta ce mutum 50 ne suka mutu sakamakon wata "baƙuwar cuta" a jihar, a cewar rahoton jaridar Premium Times.
Ɗan majalisa Anthony Ujah mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Olamaboro - inda aka yi mace-macen - shi ne ya gabatar da ƙudiri gaban majalisar na neman agajin gaggawa daga gwamnatin tarayya da na jiha ranar Talata.
A cewar ɗan majalisar, kamar yadda Premium Times ta ruwaito, cutar da ba a san irinta ba na zuwa da alamun ciwon kai da jan idanu da rashin jin yunwa da kasa yin fitsari ko bayan gida da farfaɗiya da kuma kisa.
Mista Ujah ya ce mazauna yankin Etteh a Olamaboro sun shiga ɗimuwa biyo bayan ɓarkewar cutar.
Ya ƙara da cewa har yanzu ba a san abin da ke haddasa ta ba kuma waɗanda suka kamu suna mutuwa ne a cikin mako guda da kamuwa da ita.
"Rahotannin da nake samu daga mazaɓata sun tabbatar da cewa fiye da mutum 50 ne suka mutu 'yan shekara 25 zuwa 40 tun daga watan Satumba," in ji shi.
Wani ƙarin abin tsoro shi ne, a cewarsa, "cutar ta ƙi jin dukkanin maganin gargajiya da kuma kulawar da ake bai wa mutane a cibiyoyin lafiya a matakin farko".
Tuni wasu mutum 35 suka mutu a Jihar Delta da ke kudancin ƙasar sakamakon cutar da hukumomi suka ce shawara ce, sannan wasu kusan 50 suka mutu a Enugu.