Mun fara biyan tallafin korona ga ƙananan ƴan kasuwa - Buhari

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    A nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai tsaye a wannan shafin, kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu gobe idan Allah ya kai mu inda za mu ci gaba da kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da suka shafe ku.

    Za ku iya zuwa har kasan wannan shafin domin karanta abubuwan da suka faru a yinin Laraba.

  2. Labarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa

    Bayanan sautiLabarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Yamma 18/11/2020
  3. Yadda ƴan gudun hijirar rikicin Tigray na Ethiopia ke rayuwa a Sudan

    Hukumar kula da ƴan  gudun hijira ta Sudan ta ce yawan ƴan Ethiopia da suka tsere wa rikicin Tigray zuwa ƙasar sun kai 36,000, yayin da rikicin kan iyaka ke kazancewa.

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Sudan ta ce yawan ƴan Ethiopia da suka tsere wa rikicin Tigray zuwa ƙasar sun kai 36,000, yayin da rikicin kan iyaka ke kazancewa.
    Shugaban hukumar Abdulla soliman ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP cewa adadin na ci gaba da ƙaruwa kuma suna tunanin gina wa ƴan gudun hijirar da ke kwarara sabon sansani a jihar Gaderef.

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban hukumar Abdulla soliman ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP cewa adadin na ci gaba da ƙaruwa kuma suna tunanin gina wa ƴan gudun hijirar da ke kwarara sabon sansani a jihar Gaderef.
    Tun a watan 4 ga Nuwamba ake gwabza fada a yankin Tigray da ke arewacin Ethiopia tsakanin dakarun Ethiopia da kuma na TPLF.

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Tun a watan 4 ga Nuwamba ake gwabza fada a yankin Tigray da ke arewacin Ethiopia tsakanin dakarun Ethiopia da kuma na TPLF.
    Daruruwan mutane aka kashe a rikicin wanda ya tursasawa dubbai tserewa zuwa Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Daruruwan mutane aka kashe a rikicin wanda ya tursasawa dubbai tserewa zuwa Sudan
  4. Yadda Matasa ke kwaikwayon motsa jikin Pantami ministan sadarwar Najeriya

    Isa Pantami

    Matasa musamman a arewacin Najeriya sun koma kwaikwayon motsa jikin ministan Sadarwa na ƙasar Shiekh Isa Ali Pantami.

    A ranar Talata ne ministan ya nuna wa ma’aikatan da ke karkashin ma’aikatar da yake jagoranta yadda za su motsa jiki a wani taron aiki da suka fara a ranar Litinin.

    Shafin ma'aikatarsa ya wallafa hoton ministan yana nuna yadda za a yi motsa jikin, wanda ya ja hankalin matasa.

    Wasu sun wallafa hotunansu a shafin Facebook suna irin motsa jikin ministan

  5. Gwaji ya sake tabbatar da Salah yana ɗauke da korona

    Salah

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakamakon gwajin da aka sake yi wa ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ya nuna yana ɗauke da korona yayin da ya tafi bugawa ƙasarsa Masar wasa.

    Ɗan wasan mai shekara 28, a makon da ya gabata ne gwaji ya tabbatar da yana ɗauke da korona.

    A ranar Laraba, hukumar kwallon Masar ta tabbatar da ɗan wasan ya kamu da korona.

    A ranar Lahadi ne kuma Liverpool za ta karɓi bakuncin Leicester City kafin ta haɗu da Atalanta a gasar zakarun Turai a ranar 25 ga Nuwamba.

  6. Gwaji gida-gida ya ƙara yawan masu HIV a Kamaru

    An samun ƙaruwar masu kamuwa da ƙwayar cutar HIV, mai haddasa kanjamau.

    An samu ƙaruwar ne bayan gudanar da aikin gwajin kwayar cutar ta HIV a cikin gida wanda za a ci gaba da yi har zuwa ranar 1 ga watan Disamba, a lokacin da ake bikin ƴaki da cutar a duniya.

    Sai dai kuma Ma’aikatar kiwon lafiya ta ce tana kokarin shawo kan wannan matsalar.

    Ku saurari rahoton da wakilinmu a Kamaru Mohaman Babalala ya aiko mana daga Yaounde.

    Bayanan sautiGwaji gida-gida ya ƙara yawan masu HIV a Kamaru
  7. Mun fara biyan tallafin korona ga ƴan kasuwa - Buhari

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta fara biyan tallafin korona na Survival Fund ga ƙananan ƴan kasuwa.

    A shafinsa na Twitter, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce an fara biyan mutum 101,567 kuɗaden tallafin na wata wata daga kasuwanci 16,253.

    Gwamnatin Najeriya ta ɓullo da shirin ne domin tallafi ga matsakaitan masana'antu naira biliyan 75, don ƙarfafa musu bayan iftila'in annobar korona.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Amurka ta ƙaƙaba wa Iran sabbin takunkumai

    Amurka ta sanar da sabbin takunkumai kan kamfanonin man Iran da sufuri da cibiyoyi da wasu ƴan ƙasar da suka haɗa da ministan leƙen asiri Mahmoud Alawi.

    Ma'aikatar baitil-malin Amurka wacce ta sanar da ɗaukar matakin ta ce jagoran ƙasar Ali Khamenei na amfani cibiyar Iran ta "Mostazafan" wacce ya kamata ta zama ta bayar da tallafi amma yana azurta ofishinsa da karya makiyansa.

    A martaninsa, shugaban Iran Hassan Rauhani, kamar yadda kafofin Iran suka ruwaito ya ce "waɗannan matakan ba takunkumi ba ne, illa yaƙin tattalin arziki da tattalin arzikin yawon buɗe ido.

  9. ASUU ta ce malaman jami'o'i su nemar wa kansu mafita don ba ranar koma wa makarantu

    Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya ta umarci dukkan malaman jami'o'in da su nemi wata hanya ta dogaro da kai saboda nuna halin ko in kula da ta ce gwamnatin ƙasar ta nuna game da biyan buƙatunsu.

    Farfesa Haruna Musa, shugaban Ƙungiyar Malaman Jami'o'in Najeriyar reshen Jami'ar Bayero ta Kano ya tabbatar wa BBC da batuna a wata hira ranar Laraba.

    Ƙungiyar ta kuma yi kira ga iyaye da su kansu ɗaliban jam'o'in da ka da su sa ran yiwuwar koma wa makaranta a nan kusa.

    ASUU ta kuma nuna damuwarta kan dakatar da biyan albashinsu har na tsawon watanni takwas.

    Bayanan sautiHirar Bilkisu Babangida da Farfesa Haruna Musa

    Sau da dama ƙungiyar ASUU ta sha fitar da sanarwa a rubuce inda take nesanta kanta da duk wani shafin bogi da ke wallafa saƙonni a madadinta.

    Ku latsa nan don karanta cikakken labarin yadda ɗalibai suka harzuƙa da batun.

  10. An kama mutum uku da 'suka sace' wata yarinya a Kano

    ƴan sanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce ta kama mutum uku bisa zarginsu da hannu a ɗauke wata yarinya daga gidansu tsawon kwanaki.

    Sai dai a nasu ɓangare 'yan uwan yarinyar sun ce ba ɗauke ta aka yi ba, sace 'yar su aka yi.

    Yanzu haka dai yarinyar mai kimanin shekara goma sha hudu tana asibiti tana karɓar magani, kasancewar lokacin da aka gano ta tana cikin wani mawuyacin hali.

    A cewar mahaifin yarinyar sace ta aka yi a kan hanyarsu ta zuwa sayen jigida tare da ƙawarta kwana 13 da suka gabata.

    Ya ce sun shiga halin firgici saboda rashin dawowar ta gida, sannan ya ce suka bayar da cigiyarta a ofishin ƴan sanda na Hotoro da kuma wurare da dama, amma ba a sameta sai a farkon makon nan bayan da wani maƙwabcinsu ya tsegunta musu cewa tana cikin wani gida a unguwar Tinshama.

    Alhaji Musa Garba mahaifin yarinyar ya ce sun same ta a wani gida cikin mummunan yanayi.

    Tuni dai rundunar ƴan sanda jihar Kano ta ce ta kama mutum uku kan wannan lamari, sai dai a cewar kakakin rundunar ba sace ta aka yi ba ƙawaye ne suka tafi gallafiri da ita.

    DSP Haruna Abdullahi ya ce sun kai samame gidan da aka sami yarinyar inda ya ce har ma sun tarar da wasu kayayyaki.

    Lokacin da wakilin BBC ya je ofishin ƴan sanda na Hotoro ya tarar 'yan sanda na ɗaukar bayanai daga yariyar da kuma waɗanda ake zargi, kafin a kaita asibiti.

  11. Mata ƴan sanda za su fara sa hijabi a New Zealand

    New Zealand Hijab

    Asalin hoton, INSTAGRAM/NEW ZEALAND POLICE

    Rundunar ƴan sandan New Zealand ta samar da hijabi ga jami'anta mata don ƙarfafa wa mata Musulmai su shiga aikin.

    Sabuwar jami'ar da aka ɗauka aiki Constable Zeena Ali za ta zamo mace ta farko da za ta fara sa hijab ɗin a matsayin kakinta.

    Wani mai magana da yawun rundunar ya ce suna son ƙirƙirar tsarin shigar da kowa cikin aikin don yi wa al'ummar ƙasar mai mabanbatan mutane adalci.

    Wasu rundunonin kamar na Metropolitan Police a Landan da kuma Ƴan sandan Scotland sun samar da hijabi a matsayin kaki.

  12. An fara gasar ƙwallon ƙafa ta mata a Saudiyya

    Mata a Saudiyya

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, An bar mata su fara kallon wasan ƙwallon ƙafa a filayen wasa tun a shekarar 2018

    An fara gasar ƙwallon ƙafa ta mata a Saudiyya inda tawaga 24 ke neman cin kofin.

    Ba za a haska wasannin a talabijin ba, amma kafofin yaɗa labaran Saudiyya suna yaba wa lamarin da cewa wani mataki ne na ci gaba na sanya mata a harkar wasanni - wanda aka daɗe ba a bayar da damar yi saboda dokokin addinin Musulunci da ƙasar ke bi.

    A wannan makon ne dai kuma ake gudanar da gasar ƙwallon golf ta duniya ta mata a Saudiyyan.

    Masu sukar gwamnatin Saudiyya mai ci a yanzu sun yi watsi da wannan matakin a matsayin abin da suka kira wanke kai da nuna wa duniya cewar ƙasar na kare haƙƙin ƴan adam - da nufin lulluɓe batun ci gaba da tsare mata da dama masu fafutukar kare haƙƙin ɗan adam da ake yi.

  13. Mece ce mafita kan matsalar tsaro a arewacin Najeriya?

    Al'ummar shiyyar arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da bayyana damuwa game da taɓarɓarewar tsaro da yankin ke ƙara tsunduma.

    Hare-haren 'yan bindiga da matsalar satar mutane tana ƙara munana a baya-bayan nan.

    A farkon wannan mako kawai, an kashe a ƙalla mutum 16 a Kaduna, cikinsu har da hakimi, yayin da aka sace gomman mutane da suka haɗar da wasu 'yan sanda masu muƙamin ASP a tsakanin Katsina da Zamfara.

    Ganin waɗannan matsaloli, ko anya gwamnati za ta iya magance wannan al'amari?

    Ibrahim Isa ya duba wannan batun, sai ku latsa lasifikar da ke ƙasa don sauraron rahotonsa:

    Bayanan sautiRahoton Ibrahim Isah kan rashin tsaro a arewacin Najeriya
  14. Iraƙi da Saudiyya sun buɗe iyakar Arar a karon farko a shekara 30

    Iyakar Arar

    Asalin hoton, AFP

    Iraƙi da Saudiyya sun sake buɗe iyakar Arar karon farko cikin shekara 30.

    Sake buɗe kan iyakar domin ba da dama ga mutane da kuma jigilar kayayyaki wata babbar alama ce da ke nuna ci gaban da aka samu a alaƙar ƙasashen biyu.

    A shekarar 2015 ne Saudiyya ta sake buɗe ofishin jakadancinta da ke Bagadaza.

    Saudiyyan ta yanke alaƙar diflomasiyya da Iraki bayan mamayar da Saddam Hussein ya yi a Kuwait cikin shekarar 1990.

  15. An kama matashi da zargin garkuwa da kuma kashe 'yar shekara 8 a Kano

    Habibu Sani

    Asalin hoton, Kano Police Command

    Rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai shekara 24 da ake zargi da yin garkuwa da kuma kashe wata yarinya mai shekara takwas, a cewar rahoton kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN.

    An kama Habibu Sale ne ranar 7 ga watan Nuwamba bisa zargin kashe Asiya Tasi'u a ƙauyen Chikawa na Ƙaramar Hukumar Gabasawa duk da cewa ya karɓi kuɗin fansa naira N500,000 daga wurin iyayenta.

    DSP Abdullahi Kiyawa, kakakin rundunar 'yan sandan Kano, ya ce wanda ake zargin ya aikata laifin ne tun a watan Yunin 2020.

    Ya ce bincike ya nuna cewa Habibu Sale ya binne gawar Asiya a wani ƙabari da ke wajen garin Chikawa bayan karɓar kuɗin fansar.

    An kama matashin ne bayan 'yan sanda sun yi ta bin sawunsa zuwa jihohin Jigawa da Abia da Kaduna da Katsina da Birnin Tarayya Abuja, a cewar Abdullahi Kiyawa.

  16. Dakarun Habasha sun ƙwaci gari biyu a yankin Tigray

    Dakarun Habasha sun kama gari biyu a yankin Tigray na arewacin ƙasar, inda sojojin gwamnatin yankin ke yaƙar na gwamnatin tarayya.

    Shugaban Tigray ya tabbatar da ƙwace yankunan amma ya ce 'yar matsala ce aka samu kuma yi ci alwashin yin nasara kan dakarun Habasha.

    Firaministan Habasha ya ce dakarunsa na ƙara nausawa zuwa babban birnin yankin mai suna Mekelle.

    Abu ne mawuyaci a iya tantance haƙiƙanin abin da yake faruwa a Tigray saboda katsewar layin salula da na intanet.

    Ana gwabza tashin hankalin ne a rikicin da aka shafe shekaru ana yi tsakanin babbar jam'iyyar siyasa mai mulkin Tigray, Tigray People's Liberation Front (TPLF) da kuma gwamnatin Habasha.

    A jiya Talata ne wa'adin kwana uku da gwamnati ta bai wa shugabannin yankin ya cika kuma Firaminista Abey Ahmed ya ce nan gaba kaɗan za a kawo ƙarshen "rashin doka da oda".

  17. Sabbin bayanai sun nuna rigakafin korona ta Pfizer ba ta da wata illa

    Rigakafi

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu sabbin bayanai kan rigakafin cutar korona da kamfanin Pfizer da BioNTech suka samar sun nuna cewa maganin yana da inganci sosai sannan ba shi da wata illa.

    Yanzu masu kula da lafiya a duniya za su iya fara ƙoƙarin amincewa da maganin domin amfani da shi a yaƙin da ake da cutar ta korona.

    A gwaje-gwajen da masu nazari a kamfanin na Pfizer suka yi, maganin yana da tasirin gaske kan mutane daban-daban ba tare da wata babbar illa ba.

    An yi gwajin maganin kan mutum sama da 43,000 a ƙasa shida.

    Wakiliyar BBC ta ce kamfanonin Pfizer da BioNTech na fatan samar da kusan alluran rigakafin sama da miliyan 50 a shekarar nan.

    Sannan zuwa ƙarshen shekarar 2021, kamfanonin za su samar da rigakafin fiye da biliyan ɗaya.

  18. A karon farko, an ji ta bakin shaidu a shari'ar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, Barista Sadau Garba

    Bayanan sautiLatsa hoton sama don sauraron jawabin lauyan El-Zakzaky, Barista Sadau Garba

    A karon farko, shaidu sun bayar da bahasi a shari’ar da ake yi wa shugaban ƙungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) ta 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zinah a Babbar Kotun Jihar Kaduna.

    Laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa sun haɗa da tayar da zaune tsaye da tunzura jama’a lokacin da mabiyansa suka yi artabu da sojoji a birnin Zariya a 2015 yayin muzahara. Sai dai sun musanta zargin.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun bayyana cewa mabiyansa fiye da 300 ne suka rasa rayukansu a dirar mikiyar da sojoji suka yi masu sannan aka aka ji wa Elzakzaky mummunan rauni a ido.

    Tun lokacin ne ake tsare da shi da matar tasa amma wata kotu a kwanakin baya ta wanke wasu mabiyansa fiye da 100 daga aikata laifi.

  19. Trump na shan suka kan janye dakarun Amurka a Afghanistan

    Sojojin Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Manyan ƴan jam'iyyar Republican da kuma ƙawayen Amurka sun nuna damuwa kan sanarwar cewa za a janye dakarun Amurka masu yawa daga Afghanistan da Iraƙi.

    Amurka za ta janye dakarunta 2,500 daga ƙasashen biyu zuwa tsakiyar watan Janairu, kamar yadda hukumar tsaro ta Amurka ta sanar.

    Shugaba Donald Trump ya daɗe yana kira ga dakarun su koma gida sannan ya soki shigar da Amurka ke yi cikin harkokin wasu ƙasashe.

    Shugaban ƙungiyar Nato ya yi gargaɗin "mummunan sakamako". Shi ma Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawan Amurka, Mitch McConnell, ya kira shirin "kuskure".

    Mista McConnell - wanda cikakken mai goyon bayan Trump ne - ya kuma gargaɗi shugaban game da "duk wani sauyi na manufofin harkokin wajen ƙasar" kafin ya bar ofis.

    Har yanzu Mista Trump bai amsa shan kayen da Joe Biden ya yi masa ba, kuma ana sa ran za a janye dakarun ne kwana biyar kafin Biden ya shiaga ofis.

    Mr Trump is yet to concede to Democrat Joe Biden, and the cuts are scheduled to take place five days before Mr Biden takes office on 20 January 2021.

  20. Baƙuwar cuta ta kashe mutum fiye da 50 a iyakar Kogi da Enugu

    Yahaya Bello

    Asalin hoton, @LugardHouse

    Bayanan hoto, Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi

    Kwamishinan Lafiya na Jihar Kogi, Saka Audu, ya ce waɗanda suka mutu sakamakon wata baƙuwar cuta a Jihar Enugu ne da ke maƙwabtaka da jiharsa.

    Yayin hirarsa da kafar Channels TV, kwamishinan ya ce mutum 46 ne suka mutu, ba 50 ba kamar yadda rahotanni suka ce da farko.

    A jiya Talata ne Majalisar Dokokin Kogi da ke tsakiyar Najeriya ta ce mutum 50 ne suka mutu sakamakon wata "baƙuwar cuta" a jihar, a cewar rahoton jaridar Premium Times.

    Ɗan majalisa Anthony Ujah mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Olamaboro - inda aka yi mace-macen - shi ne ya gabatar da ƙudiri gaban majalisar na neman agajin gaggawa daga gwamnatin tarayya da na jiha ranar Talata.

    A cewar ɗan majalisar, kamar yadda Premium Times ta ruwaito, cutar da ba a san irinta ba na zuwa da alamun ciwon kai da jan idanu da rashin jin yunwa da kasa yin fitsari ko bayan gida da farfaɗiya da kuma kisa.

    Mista Ujah ya ce mazauna yankin Etteh a Olamaboro sun shiga ɗimuwa biyo bayan ɓarkewar cutar.

    Ya ƙara da cewa har yanzu ba a san abin da ke haddasa ta ba kuma waɗanda suka kamu suna mutuwa ne a cikin mako guda da kamuwa da ita.

    "Rahotannin da nake samu daga mazaɓata sun tabbatar da cewa fiye da mutum 50 ne suka mutu 'yan shekara 25 zuwa 40 tun daga watan Satumba," in ji shi.

    Wani ƙarin abin tsoro shi ne, a cewarsa, "cutar ta ƙi jin dukkanin maganin gargajiya da kuma kulawar da ake bai wa mutane a cibiyoyin lafiya a matakin farko".

    Tuni wasu mutum 35 suka mutu a Jihar Delta da ke kudancin ƙasar sakamakon cutar da hukumomi suka ce shawara ce, sannan wasu kusan 50 suka mutu a Enugu.