Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mun fara biyan tallafin korona ga ƙananan ƴan kasuwa - Buhari

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Cutar ƙanjamau na yaɗuwa a Kamaru

    Ƙwayar HIV mai haddasa cutar ƙanjamau na dada ci gaba da yaɗuwa a Kamaru.

    Alkaluman da ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana sun nuna cewa kashi 36 na mutanen da suka manyanta ne suke fama da wannan cutar.

    An bayyana haka ne a dalilin zagayowar watan yaƙi da yaɗuwar ƙwayar HIV a karo na biyar da ake shiryawa a Kamaru kafin ranar 1 ga watan Disamba a lokacin da bikin yake zama na ƙasa-da-ƙasa.

    Sai dai kuma ma’aikatar lafiya ta ce tana ƙoƙarin shawo kan wannan lamari.

  2. Isra'ila ta kashe sojojin Syria a hari ta sama

    Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe mutum 10 a Syria a yau Laraba bayan wani hari da ta kai kan abin da ta kira ramuwar gayya na samun wasu abubuwan fashewa a kan iyakarta da ke Tuddan Golan.

    Hare-haren na zuwa ne 'yan awanni kafin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya isa Isra'ila domin tattaunawa kan dakarun Iran da ke yaƙi a ƙasashen waje da ake kira Dakarun Quds.

    Kamfanin dillancin labaran Syria na SANA ya ce harin ya kashe soja uku tare da raunata wani. Sauran waɗanda aka kashe ɗin mayaƙa ne 'yan ƙasashen waje da kuma 'yan Syria.

    Ana ganin ita ce ziyarar ƙarshe da Mista Pompeo zai kai yankin kafin Shugaba Donald Trump ya bar karagar mulki a watan Janairu mai zuwa.

  3. Amurka ta saka wa jagororin Al-Shabab takunkumi

    Amurka ta saka takunkumi a kan manyan shugabannin ƙungiyar Al-Shabab mai tsattsauran ra'ayin Musulunci da ake zargi da kai hari kan sansanin soja a Kenya.

    An kashe wani sojan Amurka da 'yan kwangilar kayayyakin soja biyu yayin da aka kai kan Sansanin Simba a Tsibirin Manda.

    Shi ne hari na farko da Al-Shabab ta kai kan sojojin Amurka a Kenya.

    Amurka ta ce ta sanya Abdullahi Osman Mohamed da Maalim Ayman a jerin sunayen 'yan ta'adda na duniya.

    Ta ce Mohamed, shi ne ƙwararre kan abubuwan fashewa na ƙungiyar da kuma sashen yaɗa labarai, yayin da Mista Ayman kuma ya shirya kai hari kan Sansanin Simba.

  4. An dakatar da ma'aikacin ofishin jakadancin Najeriya a Jamus bisa zargin lalata

    Ofishin jakadancin Najeriya a Jamus ya dakatar da wani ma'aikacinsa bisa zargin yunƙurin lalata da wata mace a Berlin, babban birnin ƙasar.

    Yusuf Tuggar, shi ne jakadan Najeriya a Jamus kuma ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin.

    Matakin dakatarwar ya biyo bayan wani bidiyo ne da ya karaɗe shafukan zumunta da ke nuna wani ma'aikaci da aka ce mai gadi ne yana neman yin lalata da wata mata a matsayin ladan yi mata fasfo.

    Ambasada Yusuf Tuggar ya ce ofishin jakadancin Najeriya ba zai taɓa amincewa da halin rashin ɗa'a ba, musamman na yin lalata.

    "Ba za mu taɓa lamuntar yin amfani da iko ba bisa ƙa'ida ba musamman wurin aikata lalata. Mun fara bincike kan lamarin lalata da kuma duk wani abu da ya faru," in jni shi.

    "Ana gudanar da binciken ne cikin sauri da kuma kulawar da lamarin yake buƙata. Idan aka kammala, mai laifi zai fuskanci hukunci."

  5. 'An aikata fyaɗe fiye da 100 a kowace jiha a Najeriya yayin dokar kulle'

    Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce an samu rahotannin fyaɗe fiye da 3,600 a Najeriya baki ɗaya yayin da ake cikin dokar kullen anobbar cutar korona.

    Mataimakiyar Sakataren MDD Amina Mohammed ce ta bayyana hakan, tana mai nuna damuwarta game da yawaitar cin zarafi mai alaƙa da jinsi a Najeriya.

    Jaridar Punch ta ruwaito ta tana magana ne yayin ƙaddamar da wani taron ƙara wa juna sani kan cin zararfin mata da ƙananan yara mai taken Violence Against Women and Girls Situation Room.

    Ta ƙara da cewa MDD za ta ci gaba da aiki da Ma'aikatar Harkokin Mata ta Najeriya domin ƙara tattara bayanai game da cin zarafin mata.

    An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin MDD da Ƙungiyar Tarayyar Turai da Ma'aikatar Harkokin Mata ta Najeriya.

    "Buƙatar irin waɗannan shirye-shiryen na da matuƙar mahimnmanci musamman a lokacin dokar kulle, wadda ta shafi duniya baki ɗaya," in ji Amina Mohammed.

    Ta ƙara da cewa: "Ministar harkokin mata ta ce adadin laifukan fyaɗe ya ninka sau uku idan aka kwatanta da lokutan baya. A lokacin dokar kulle, kowace jiha ta bayar da rahoton fyaɗe fiye da 100, abin da ya sa aka samu sama da 3,600 a ƙasa baki ɗaya."

  6. Trump na shan suka kan janye sojojin Amurka daga Afghanistan

    Shugaba Trump na shan suka kan matakinsa na kwashe kashi 50 cikin 100 na sojojin Amurka daga Afghanistan nan da watan Janairu.

    Hatta 'yan jam'iyyarsa ta Republican na sukarsa bayan da shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa Mitch MacConnell ya yi gargaɗin cewa matakin zai kawo tarnaƙi ga harkokin ƙasashen wajen Amurka.

    Wakilin BBC ya ce ta ɓangaren 'yan jam'iyyar Democrats kuwa, Shugabar Majalisar Wakilai Nancy Pelosi ta ce gaggawar kwashe sojojin zai sa Afghanistan ta sake zama matattarar ta'addanci.

    Shi ma Sakataren Harkokin Tsaron Amurka Chuck Hagel ya ce bai ga dalilin ɗaukar wannan mataki ba ana saura wata biyu a yi canjin gwamnati.

    Ba a Afghanistan kaɗai ba, ko a Iraqi gwamnatin Trump na shirin ɗaukar matakin rage sojojin Amurka kowane lokaci daga yanzu.

  7. Gwamnan Ebonyi ya koma APC ne saboda ƙashin kansa - PDP

    Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana ficewar da Gwamnan Ebonyi, David Umahi, ya yi daga cikinta zuwa APC a matsayin "dalilai na raɗin kansa".

    Gwamnan na cewa ya bar jam'iyyar ne saboda PDP ba ta miƙa tikitin takarar shugaban ƙasa ba zuwa yankinsa an Kudu maso Gabas wato ɓangaren ƙabilar Igbo.

    Sai dai rahotanni sun ambato Umahi na cewa ya koma APC mai mulki ne ba don ya amfana da raɗe-raɗin cewa APC na shirin bai wa yankin Kudu maso Gabas damar yin takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa ba.

    "Gwamnan Ebonyi Dave Umahi ya bar PDP ne saboda dalilai na ƙashin kansa waɗanda 'yan Najeriya za su fahimta nan gaba kaɗan," in ji PDP a cikin wata sanarwa da Kola Ologbondiyan ya fitar.

    Fitar gwamnan daga PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya ya rage wa jam'iyyar PDP tasirin siyasa da take da shi a yankin Kudu maso Gabas bayan shafe shekaru tana mulkin mafi yawan jihohin yankin.

    Yanzu haka APC na mulki a jiha biyu (Imo da Ebonyi), yayin da PDP ke mulki a biyu, sai kuma APGA da ke riƙe da mulki a jiha ɗaya.

  8. Trump ya kori jami'in zaɓe saboda ya saɓa masa kan sakamako

    Shugaba Donald Trump ya yi waje rod da babban daraktan harkar tsaron internet na Amurka, bayan da ya ce ya gamsu da yadda zaɓen shugaban ƙasa ya gudana.

    Trump ya zargi Christopher Krebs da yin kalaman da ya ce "sun yi hannun riga" da gaskiya.

    Da ma an yi hasashen sallamar Mr Krebs bayan da hukumar da ya ke jagoranta ta wallafa a shafinta na internet cewa zaɓen na bana shi ne mafi sahihanci a tarihin Amurka.

    Wakiliyar BBC ta ce abu ne mai ɗaure kai a ce shugaban ƙasa irin Amurka da ke iƙirarin kare dimokuradiyya a ce ya kori babban jami'insa don kawai ra'ayinsu bai zo ɗaya ba kan zaɓe.

    Har kawo yanzu Mista Trump ya ƙi ya amsa shan kaye a hannun zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Joe Biden.

  9. Ƙarin mutum 152 sun kamu da cutar korona a Najeriya ranar Talata

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu karin mutum 152 da suka kamu da cutar korona a ranar Talata a ƙasar.

    Da wannan sabbin alkaluman jimillar wadanda cutar ta kama a ƙasar sun kai 65,457 an kuma sallami mutum 61,337, sai kuma mutum 1,163 da suka mutu.

    Jihar Legas ce mai adadi mafi yawa da mutanen 61 da suka kamu a ranar ta Talata, sai Oyo mai mutun 39, FCT na da 13 sai Yobe mai mutum 10.

    Jihar Bauchi na da mutun 6 da su ka kamu yayin da Kaduna ke da 5.

    Su kuwa jihohin Kano da Kwara da Plateau su na da mutun 4-4 kowannensu

    Jihohin Edo da da Ogun da Rivers ne su ka rufe lissafin masu dauke da cutar a ranar Talata da mutun 2 kowannensu.

  10. Maraba

    Barkammu da hantsin Laraba - ta bawa ranar samu.

    Ku biyo ni Umar Mikail a wannan shafi domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a duniya, musamman a Najeriya da Nijar.