Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Za mu magance matsalolin tsaro - Buhari

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Kwararar 'yan gudun hijira daga Najeriya a Kamaru ta ƙara yawan yara marasa takardar shaidar haihuwa

    Kwararar dubban 'yan gudun hijira daga Najeriya da maƙwabtanta zuwa cikin Kamaru sun ƙara yawan yaran da ba su da takardar shaidar haihuwa a jihohin arewacin ƙasar.

    A dalilin haka ne hukumar kula da ‘yan gudun hijira (UNHCR) ta shirya wani taron wayar wa iyayen yaran kai domin kauce wa wannan lamari.

    A yanzu haka rashin samar wa yara takardar shaidar haihuwa ya zama wani ƙudirin doka da ‘yan majalisar dokoki ke tattaunawa a kai domin samar da hanyoyi mafiya sauki wurin samar wa yara takardar.

    Sansanin Minawawo ne ke da mafi yawan 'yan gudun hijira da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.

    Da ma dai an daɗe ana kokawa kan yaran da ba su da takardar shaidar haihuwa a arewacin Kamaru, inda yake fama da rikicin 'yan tawaye da ke son ɓallewa daga ƙasar.

  2. Mutum fiye da 30,000 ne ke gudun hijira a Sudan saboda yaƙi a Habasha

    Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce fiye da mutum 30,000 ne suka tsallaka Sudan daga Habasha ko kuma Ethiopia sakamakon yaƙin da ake yi a yankin Tigray.

    Babban jami'in UNHCR Jens Hesemann, shi ne ya faɗa wa BBC hakan, yana mai cewa adadin na ƙaruwa kullum.

    "Yanayin ta'azzara yake ƙara yi kullum, a jiya kaɗai mutum 2,300 ne suka isa ƙasar, shekaran jiya kuma 5,000," in ji shi.

    Wurin saukar mutane na hukumar ya cika maƙil har ma an fi ƙarfinsa.

    "Mutanen yankin suna da kirki ta yadda suke taimaka wa 'yan gudun hijirar da ɗan abin da suke da shi, su ma hukumomi suna tallafawa sosai, suna nema mana filin da za mu sauke su," Mista Hesemann ya bayyana.

    'Yan gudun hijirar na fargabar abin da ka iya faruwa idan suka ci gaba da zama a yankin na Tigray, inda yaƙi ya ɓarke tsakanin Gwamnatin Tarayyar Habasha da kuma gwamnatin yankin.

  3. Ƙungiyar ƙwadagon Najeriya ta umarci gwamnati ta janye ƙarin kuɗin man futur

    Ƙungiyar 'yan ƙwadago a Najeriya ta Nigeria Labour Congress (NLC) ta buƙaci gwamnatin ƙasar ta janye ƙarin kuɗin man fetur da ta yi nan take.

    Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Ayuba Wabba ya saka wa hannu jiya Litinin, NLC ta yi watsi da ƙarin tana mai sukar gwamnati.

    Ta ce ƙarin na baya-bayan nan zai sake tsananta halin ƙuncin da mutane ke ciki a ƙasa baki ɗaya.

    A cewar NLC: "Abin takaici ne a riƙa ɗaura wa 'yan Najeriya wahalhalu sakamakon gazawar gwamnatoci wurin kula da matatun mai na ƙasa."

    Ta ƙara da cewa "wannan lamari ya sa ana ɗiga ayar tambaya game da dalilan da gwamnatin ta bayar na cire kuɗin tallafin man fetur".

  4. 'Yan bindiga sun kashe hakimi da ɗansa tare da raunata matarsa a Kaduna

    'Yan bindiga a Kaduna sun kashe Hakimin garin Gidan Zaki da ke Masarautar Atyap ta Ƙaramar Hukumar Zango Kataf tare da ɗansa.

    Mutanen da ake zargin 'yan fashi ne, sun shiga garin da asubahin yau Talata, inda suka kashe Hakimi Haruna Kuye da kuma ɗansa Destiny Kuye, a cewar sanarwar da Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ya fitar.

    Sanarwar ta ce sojoji sun shaida wa gwamnatin jihar cewa 'yan bindigar sun harbi 'yar dagacin a yatsa sannan suka sari matarsa a hannu, wadda ke samun kulawa a asibiti.

    Rahotannin sun ce aƙalla mutum biyar ne suka isa garin ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 da gatari sannan suka yi ƙoƙarin cinna wa gidan wuta tare da wata mota.

    Haka nan, an kashe wani tsohon Mai Garin garin Kyemara Gari mai suna Albarka Addu'a a Maraban Kajuru bayan 'yan bindiga sun sace shi da kuma wani daban.

    Kazalika, gwamnatin Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum 11 a harin da aka kai ƙauyen Albasu na Ƙaramar Hukumar Igabi jiya Litinin, inda ta ce wasu mutum huɗu sun jikkata.

  5. Buhari na jagorantar taron Majalisar Tsaro ta Ƙasa

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jagorantar taron Majalisar Tsaro ta Ƙasa a fadarsa ta Aso Rock Villa da ke Abuja, wanda ake yi duk wata huɗu.

    Daga cikin masu halartar taron akwai Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, da Sakataren Gwamanti Boss Mustapha, da Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Farfesa Ibrahim Gambari, da Ministan Shari'a Abubakar Malami.

    Sauran sun haɗa da Ministan Tsaro Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, da Ministan Harkokin Waje Geoffery Onyeama, da Ministan Ayyukan 'Yan Sanda Muhammad Maigari Dingyadi.

    Sai kuma shugabannin tsaro na rundunonin sojan ƙasar da na 'yan sanda da na farin kaya da masu tattara bayanan sirri.

    Taron nasu na zuwa ne yayin da aka kashe ko kuma sace kusan mutum 50 cikin ƙasa da mako ɗaya a arewacin Najeriya.

  6. Yaro 29 aka kashe a yaƙin Yemen a 2020 – Save the Children

    Kungiyar ba da agaji ga ƙananan yara ta Save the Children ta ce ƙananan yara da aka kashe da kuma jikkata su a Yemen a bana sun fi na kowace shekara yawa sakamakon yaƙin da Saudiyya ke jagoranta a ƙasar.

    Yaƙi na daɗa ƙazancewa a biranen Hudaida da Ta'iz a yakin da gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan Saudiyya ke yi da 'yan tawayen Houthi.

    A cewar Save The Children, a watan da ya gabata kaɗai, hare-haren ɓangaroran biyu sun kashe ƙananan yara 29.

    Wakiliyar BBC ta ce a kan haka ne ƙungiyar ta yi kira ga shugabannin kasashen G-20 da su tursasa wa bangaroran biyu zama a teburin sulhu.

    Ta kuma buƙaci ƙasashen duniya irin suBurtaniya da su daina sayar wa Saudiyya da makamai.

  7. Wanda ya yi wa Buhari tattaki daga Gombe zuwa Abuja ya samu kyautar miliyan biyu da mota

    Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe da ke arewacin Najeriya ya bai wa mutumin nan da ya yi tattaki daga Gombe zuwa Abuja don murnar cin zaɓen Shugaba Buhari a 2015 kyautar mota.

    Kazalika, gwamnan ya bai wa Dahiru Buba Dukku kuɗi naira miliyan biyu, kamar yadda yake ƙunshe cikin wata sanarwa da Ismal Uba Misilli mai bai wa gwamnan shawara kan kafafen yaɗa labarai ya fitar.

    Dahiru Buba mai shekara 50, yanzu haka yana fama da ciwon ƙafa kuma an ba shi kyautukan ne a Abuja jiya Litinin.

    A kwanakin baya, mutane sun yi ta kiraye-kirayen gwamnati ta kai masa ɗauki sakamakon ciwon ƙafar da ke damunsa.

    Gwamnan ya ba shi kyautar ne "saboda tsananin ƙaunar da yake yi wa jam'iyyar APC" mai mulkin Najeriya, a cewar sanarwar.

  8. Kotu ta ɗaure uwa da 'ya'yanta shekara 24 a gidan yari a Najeriya

    Wata kotu ta ɗaure uwa da yaranta biyu sakamakon kama su da laifin yin safarar wata matashiya mai shekara 19 zuwa ƙasar Rasha, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na NAN.

    Kotun da ke Benin na Jihar Edo a kudancin Najeriya ta yanke wa matar mai suna Helen Ehiozee shekara 10 a gidan yari, inda 'ya'yanta Endurance Ehiozee (namiji) mai shekara 37 da Vivian Ehiozeee (mace) mai shekara 31 aka yanke musu hukuncin shekara 14.

    An yanke hukuncin ne a jiya Litinin bayan an shigar da ƙarar a shekarar 2017, a cewar NAN.

    Mai Shari'a Geraldin Imadegbelo ya bayyana cewa mutanen sun karya sashe na 15 da 16 na kundin dokar hana safarar mutane ta 2003.

    NAN ya ce matashiyar - wadda ba a ambaci sunanta ba - 'yar shekara 27 a yanzu, an yi safararta ne a 2012 zuwa Rasha tun tana shekara 19 domin yin karuwanci.

  9. Babban mai yaƙi da rashawa a Ghana ya ajiye aikinsa 'saboda yi masa karan-tsaye'

    Shugaban sashen yaƙi da cin hanci da rashawa a Ghana, Martin Amidu, ya ajiye aikinsa yana mai cewa an yi masa karan-tsaye.

    An yi ta zumuɗi a lokacin da Shugaban Ƙasa Nana Akufo-Addo ya naɗa Mista Amidu a 2018, sai dai mutane ba su ji daɗin abin da ya farun ba.

    A cikin jawabin da ya yi na barin aikin, tsohon antoni janar ɗin ya ce bai samu cikakken 'yanci ba na gudanar da aikin nasa.

    Kazalika, ya zargi Shugaba Akufo-Addo da yi masa katsalandan duk da cewa ofishin shugaban bai mayar da martani ba zuwa yanzu.

    Haka nan ya ce shi da wasu ma'aikatan ofis ɗinsa ba a biya su albashi ba tun da aka ɗauke su aiki.

  10. Trump ya so ya kai wa tashar nukiliyar Iran hari

    Jaridar New York Times ta ruwaito cewa mashawartan Shugaba Trump sun gargaɗe shi a makon da ya gabata da kar ya kai hari kan tashar nukiliyar Iran.

    An ruwaito cewa Trump ya nemi shawarar babban mai ba shi shawara kan harkar tsaro game da yiwuwar kai wa Iran hari ranar Alhamis da ta gabata.

    Sai dai daga baya Trump ya canza ra'ayi bisa tsoron abin da hakan zai haifar a Gabas ta Tsakiya.

    New York Times ta ce shugaban ya fara neman shawarar ne bayan wani rahoton hukumar kula da makaman nukiliya ta IAEA ya bayyana cewa Iran na ci gaba da inganta makamashin uranium, wanda ake haɗa nukiliya da shi.

    Ana tunanin harin zai faɗa ne kan tashar Natanz, wurin da IAEA ta ce "uranium ɗin Iran ya ninka sau 12 na wanda aka amince mata a ƙarƙashin yarjejeniyar da Trump ya cire Amurka daga ciki wadda aka ƙulla a 2018".

    Kawo yanzu babu wani martani kan rahoton daga Fadar White House.

  11. Mutum 157 sun kamu da korona a Najeriya ranar Litinin

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu karin mutum 157 da suka kamu da cutar korona a ranar Litinin a ƙasar.

    Hukumar ba ta ruwaito mutuwa ba a cikin sabbin alƙaluman.

    Jihar Legas ce mai adadi mafi yawa da mutanen 97 da suka kamu, sai Oyo mai mutum 37, Kaduna mai mutum 9 da Bayelsa mai 3.

    Sauran jihohin su ne: Edo (3), Ekiti (3), Ondo (2), Osun (2) da Filato (1).

    Da wannan sabbin alkaluman, jumillar wadanda cutar ta kama a ƙasar sun zama 65,305, an kuma sallami mutum 61,162, sai kuma mutum 1,163 da suka mutu.

  12. Maraba

    Barka da shigowa wannan shafi.

    Za ku kasance tare da UmarMikail ne a wannan hantsi domin kawo muku rahotanni daga sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da makwabtansu.

    Ku biyo ni.