PDP ce jam'iyya mafi nagarta a Najeriya – Atiku
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma jigo a ɓangaren adawa, Atiku Abubakar, ya yi kurarin cewa jam'iyyarsu ta PDP ce "mafi nagarta" a ƙasar.
Atiku wanda ya yi wa PDP takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019, ya ce ya kamata dukkanin ɓangarorin siyasar Najeriya su zama ƙarƙashin shugabancinta "saboda ita ce jam'iyyar da ta yi amanna da ɗorewar Najeriya".
Atiku ya bayyana haka ne a yau Litinin cikin wani saƙon Twitter da ya wallafa a shafinsa.
"Jam'iyyar PDP na da ayyukan da za ta yi a lungu da saƙo na Najeriya kuma ina shawartar dukkanin 'yan Najeriya daga ɓangarori da su yi amanna da PDP, wadda ta yi amanna da ɗorewar Najeriya," in ji Atiku.
Wannan batu na Atiku na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa kan gwamnonin jam'iyyar ya rabu game da wanda zai gaji Uche Secondus a matsayin shugabanta, wanda wa'adinsa ke ƙarewa a watan Disamba mai zuwa.