Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

RFI ta yi kuskuren wallafa labarin mutuwar Sarauniyar Ingila

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    Nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu gobe idan Allah Ya kai mu inda za mu shafe yinin Talata muna kawo labarai da rahotanni kai tsaye.

    Za ku iya zuwa har ƙasan wannan shafin domin karanta abubuwan da suka faru a ranar Litinin.

  2. Shugaban yaƙi da rashawa a Ghana ya yi murabus

    Shugaban yaƙi da cin hanci da rashawa a Ghana ya yi murabus yana mai cewa ana yi masa zagon ƙasa a aikinsa.

    Lokacin da aka naɗa Martin Amidu a 2018 ƴan ƙasar Ghana sun yi maraba tare da kyakkyawar fata, amma kuma wakilin BBC a Ghana ya ce sakamakon ya zama wani abin takaici.

    Mai gabatar da ƙarar na musamman ya bayyana koken rashin samun ƴancin gudanar da aikinsa na yaƙi da rashawa a matsayin dalilin murabus ɗinsa.

    Ya zargi shugaban Ghana da yin katsalandan a aikinsa. A baya ma ya bayyana damuwa kan rashin samun haɗin kai daga sauran hukumomin ƙasar tare da bayyana rauni daga ma’aikatansa a ƙoƙarin yaki da rashawa a tsakanin ma’aikatan gwamnati.

    Daga cikin binciken da yake akwai batun dala miliyan biyar na badaƙalar kamfanin Airbus na Turai wanda ya shafi hannun jami’an gwamnati.

    Ƴan Ghana da dama sun ji takaicin murabus ɗinsa.

  3. Tunisia na son a yi taron Musulmi da ƙasashen Yammaci kan addinin Islama

    Shugaban Tunisia Kais Saied da Qatar za su nemi a gudanar da taron tattaunawa tsakanin Musulmai da ƙasashen yammacin duniya don hana haddasa kyamar musulmi bayan hare-haren ta’addanci da akai.

    A yayin ziyarar da ya kai Doha, shugaba Saied ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Qatar cewa gwamnatin Doha da Tunis za su gabatar da buƙatar gudanar da taron tattaunawa tsakanin ƙasashen yammaci da na musulmi da nufin ƙara fahimtar juna da kuma ƙoƙarin shawo kan matsalolin da suka biyo bayan hare-haren masu kaifin kishin addini.

    Ana ganin wannan yunƙurin, wani ɓangare ne na martani ga kalaman da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi cewa addinin musulunci na cikin rikici, bayan hare-haren da aka kai a Faransa.

    A watan da ya gabata ne Macron ya kaddamar da wani shirin kare ƙasarsa daga abin da ya kira “Tsattsauran ra’ayin Islama,” wanda ya janyo masa suka daga ƙasashen musulmi.

    Shugaban Tunisia ya ce wata manufar taron ita ce “kaucewa ruɗanin alaƙanta musulmi da wasu ƴan ta’adda da ke iƙirarin su musulmai ne”

    Ya kara da cewa "akwai bukatar a bambance tsakanin Musulunci da manufofin ta’addanci wanda ba ya da wata alaka da addinin Islama.

    Babu dai wani cikakken bayani game da buƙatar gudanar da taron da kuma lokacin da za a yi.

  4. Kafar RFI ta wallafa labarin mutuwar Sarauniyar Ingila

    Gidan rediyon Faransa RFI ya nemi gafara kan labaran ƙarya da ya ƴada na mutuwar shahararrun mutane kusan 100, ciki har da Sarauniya Elizabeth ta Ingila da kuma fitaccen ɗan ƙwallon Brazil Pele.

    Radio France International da ke yaɗa labarai a harsuna da dama ya wallafa labaran mutuwar ne a shafin Intanet.

    Amma kafar ta ce matsalar na’ura ce ta sa aka wallafa labaran mutuwar fitattun mutanen.

    Sauran waɗanda RFI ta wallafa cewa sun mutu, sun haɗa da tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter da Raul Castro na Cuba da kuma jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei.

    Yawanci dai kafafen ƴada labarai kan tattara tare da shirya labaran mutuwar fitattun mutane domin wallafa su nan take lokacin da aka sanar da mutum ya mutu.

    Kafar ta ce labarai sama da 100 aka wallafa kan kuskure kuma ba a shafin RFI kawai ba har da na abokan hulɗa da suka haɗa da Google da Yahoo.

  5. Kayayyaki sun ƙara tsada a Najeriya - NBS

    Hukumar ƙididdiga a Najeriya ta ce hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kashi 0.5 idan aka kwatanta da watan da ya gabata.

    A watan Oktoba ya kai kashi 14.2 daga kashi 13.7 a watan Satumban 2020.

    Wannan na nufin tsawon watanni 14 ba farashin kayayyaki sai karuwa yake tun Satumban 2019.

    Rahoton NBS ya ce, fashin kayan abinci ya tashi da kashi 0.72 a Oktoba.

  6. Saudiyya za ta bayar da intanet kyauta a Masallatan Makkah da Madina

    Saudiya za ta fitar da wurare 60,000 da za a yi amfani da WiFi kyauta a fadin ƙasar a matsayin wani bangare na shirin Hukumar Fasahar Sadarwa (CITC), kamar yadda jaridar Arab News ta ruwaito a ranar Litinin.

    Kamfanin dillacin labaran Saudiyya na SPA ya ce za a samar da Wifi ne a Masallatan Makkah da Madina da asibitoci da kantina da kuma wuraren shakatawa.

    Za a ba mutane damar yin amfani WiFi kyauta na tsawon sa’a biyu a wasu biranen Saudiyya

    Sannan akwai wani ci gaban fasahar da aka samu inda aka yi tanadin abun hawa mai amfani da lantarki ga masu ibada domin a Makkah zuwa Madina.

  7. Kotun Nijar ta faɗi dalilin haramta wa Hama Amadou takara

    Kotun tsarin mulkin Nijar ta bayyana dalilan da suka ta haramta wa madugun adawar ƙasar takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen ƙasar na watan Disamba.

    Jaridar ActuNiger ta ruwaito kotun tsarin mulki a cikin wata sanarwa na cewa akwai dalilai da doka ba ta amince da su ba a zaɓe.

    Dalilan da kotun ta bayyana sun haɗa da cewa "ba za a amince da mutumin da aka kama da aikata laifi kuma bai yi gyara hali ba, mutumin da aka kama da laifi kuma aka yanke masa hukunci shekara ɗaya a gidan yari."

    "Bisa ga waɗannan sharuɗɗan , Hama Amadou da aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekara ɗaya a gidan yari, bai cancanta ya tsaya takarar zaɓen shugaban ƙasa ba da za a gudanar 27 ga Disamba, a cewar kotun."

    Hama Amadou yana cikin ƴan takara 11 da kotun ta haramtawa takara.

    A watan Satumba Hama Amadou wanda aka yanke wa hukuncin laifin safarar yara a 2014 ya yi gargadin cewa Nijar za ta iya fuskantar rikicin da aka gani a Mali idan har kotun tsarin mulki ta yi watsi da takararsa.

  8. Yadda Pantami ke koya wa ma'aikatansa motsa jiki

    Ministan ma'aikatar sadarwa a Najeriya Dr Isa Pantami ya nuna wa ma'aikatansa dubarun motsa jiki a wani taron da ma'aikatar ke gudanarwa.

    Ma'aikatar ta wallafa a shafin na Twitter hotunan Pantami wanda fitaccen malamin addini ne a arewacin Najeriya, yana motsa jiki tare da cewa "kasancewa cikin koshin lafiya don gudanar da ingantaccen aiki.

  9. Obasanjo ya tafi Habasha domin sasanta rikicin siyasa

    Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya hanyarsa ta zuwa Habasha domin yunƙurin sasanta tsakanin gwamnatin ƙasar da kuma gwamnatin yankin Tigray.

    Yunƙurin nasa na zuwa ne 'yan awanni bayan Shugaban Uganda ya yi tayin tattaunawar sulhu kafin daga baya ya goge saƙon Twitter da ya wallafa.

    Gwamnatin Habasha ta haƙiƙance cewa ba za ta tattauna da jam'iyyar TPLF ba - mai mulkin yanki - tana mai cewa jam'iyyar ta yi fatali da wani shirin zaman lafiya da aka gabatar shekara biyu da suka gabata.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito mai magana da yawun Obasanjo, Kehinde Akinyemi, yana cewa: "Tsohon Shugaba Obasanjo na kan hanyarsa ta zuwa Addis Ababa domin tattaunawa."

    Ya ƙara da cewa "zai je ne domin shiga tsakani," amma bai yi wani ƙarin bayani ba.

    "Duk wani ƙoƙarin shiga tsakani zai ƙara rura wutar aikata laifi ne da kuma rashin bin doka," a cewar Ministan Harkokin Wajen Habasha, Redwan Hussein.

    "Babu wata ƙasa da za ta zira ido kan wani ɓangare nata bayan ya bayyana cewa yana da makaman roka da masu linzami sannan ya ci alwashin kai hari."

  10. Trump ya sake yin iƙirarin cewa shi ya ci zaɓe

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin iƙirari a karo na biyu cewa shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 3 ga watan Nuwamba - ba tare da wata hujja ba.

    Kamfanin Twitter ya maƙala wa saƙon na Mista Trump jan rubutu - kamar mafi yawa daga saƙonnin nasa - cewa: "Hukumomi ba haka suka bayyana sakamakon zaɓen ba."

    "Ni ne na ci zaɓen," in ji Trump a saƙon da ya wallafa da ƙarfe 8:51 agogon birnin Washington (2:51 agogon Najeriya da Nijar).

    A jiya Lahadi ne kuma Trump ɗin ya faɗa a karon farko cewa abokin hamayyarsa Joe Biden "ya lashe zaɓen ne saboda an yi maguɗi".

    Kwana ɗaya bayan kaɗa ƙuri'a Trump ya yi iƙirarin cewa shi ne ya ci zaɓen amma aka murɗe masa. Kazalika, ya kira sake ƙirga ƙuri'un da ake yi a Jihar Geogia da cewa "na boge, saboda ba a tantance sa hannun masu kaɗa ƙuri'ar.

    Tuni BBC ta yi hasashen cewa Joe Biden na jam'iyyar Democrat ne zai lashe Geogia, wanda da ma shi aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri'ar wakilan zaɓe na musamman 306, shi kuma Trump yana da 232.

  11. Sarki Saudiyya ya yi kira a fito sallar roƙon ruwa

    Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya ya yi kira da a fito domin gudanar da sallar Istisqa (Sallar rokon ruwa) a duka faɗin masarautar a ranar Alhamis mai zuwa, kamar yadda wata sanarwar babbar kotun ƙasar ta bayyana.

    Sanarwar ta ce gabatar da sallar roƙon ruwan ta yi daidai da koyarwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad.

    Sarkin ya yi kira ga kowa ya fito domin a yi rokon yafiya da kuma tuba ga Allah game da laifukan da bayi ke yi da kuma neman rahamar ubangiji.

    Tuni kafafen sada zmunta na kasar suka fara wallafa wannan kira na shugaban.

    Akan gudanar da wannan sallah ne a lokutan da aka samu fari na ruwan sama, ko kuma a yi addu'ar neman tsagaitawar ruwa a lokacin da ya yi yawa ya koma yin ɓarna.

  12. Majalisar Peru ta gaza zaɓar shugaban ƙasar

    Majalisar Peru ta gaza amincewa da wanda zai maye gurbin shugaban riƙon ƙwaryar ƙasar, Manuel Merino, wanda ya sauka a ranar Lahadi.

    Bayan muhawara ta dogon lokaci, majalisar ta yi watsi da tawagar shugabanci karkashin jagorancin Racio Silva-Santisteban, marubuci kuma tsohon mai fafutika kan haƙƙin dan Adam.

    Yanzu za a sake sabbin zubin sunayen shugabannin riƙon ƙwarya da manyan ƴan siyasa daga bangarori daban-daban, sannan a kaɗa kuri'a a yau gaba.

    An tilasta wa Manuel Merino barin kujera bayan gaza samun goyon-bayan ƴan majalisa, sakamakon mutuwar biyu daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnati.

    Zanga-zangar ta biyo bayan tsige shugaba Martin Vizcarra ranar Litinin kan zarge-zargen rashawa.

  13. Da gaske wasu masu yi wa ƙasa hidima biyu sun kamu da korona a Kano?

    Babbar jami'ar hukumar yi wa ƙasa hidima ta NYSC a Jihar Kano, Aisha Tasa, ta ƙaryata labarin cewa mutum biyu daga cikin 'yan yi wa ƙasa hidimar da aka tura jihar sun kamu da cutar korona.

    Aisha ta shaida wa wakilin BBC a Kano cewa gwajin da aka yi wa ɗaliban bai fito ba bare a tabbatar da ko suna da korona.

    A ranar Litinin ne rahotanni suka ce dalibai biyu sun kamu da cutar korona jim kaɗan bayan rantsar da su guda 826 na 2020 Rukunin B Tawagar I.

    Ta ce an yi wa dukkanin 826 ɗin gwaji kafin a ƙyale su shiga cikin sansanin hukumar kuma tuni aka kai waɗanda suka kamun wurin da za a kula da su.

    Ta shaida wa taron manema labarai cewa an tanadi dukkanin kayan tsafta kuma za mu tabbatar cewa masu yi wa ƙasa hidima sun yi amfani da su.

    A saƙonsa ga masu hidimar, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci su kasance masu mayar da hankali ta hanyar shiga a dama da su a dukkanin ayyukan da aka tanada.

  14. Sansanin 'yan gudun hijirar Kamaru ƙara tumbatsa

    Sansanin Minawao a arewacin Kamaru ya karbi baƙuncin sabbin ‘yan gudun hijira 6,500 a cikin wata 11.

    Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ce ta bayyana haka, tana mai cewa akwai dalilai da dama da suka jawo ƙaruwar adadin.

    Daga ciki akwai hayayyafar jariran da ake samu akalla 30 a duki mako, da kuma halin matsatsin da tarin wasu ‘yan gudun hijira suka fada bayan sun fice daga sansanin domin radin kansu, abin da ya sa suke sake komawa.

    Hakan ya kai ga zuwa ranar 31 ga watan Oktoban da ya shige an lissafa ‘yan gudun hijira 68,390 a sansanin na Minawao.

    A 2014, 'yan gudun hijirar Najeriya 2,500 ne ke cikin sansanin na Minawao, wanda ke kan iyakar ƙasar da Kamaru.

    Lamarin na ƙara ta'azzara ne a Kamaru yayin da 'yan tawayen yankin rainon Ingila ke ƙara kai hare-hare da kuma ƙungiyar Boko Haram da ke kai nata hare-haren, abin da ke sa mazauna yankunan barin mahallansu.

    A watan da ya gabata ne babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira a Najeriya Basheer Garba Mohammed da Gwamnan Borno Borno Babagana Zulum suka kai ziyara Nijar domin dawo da 'yan gudun hijirar ƙasar gida.

  15. Aubameyang ya koka kan yadda aka "tsare su " awa bakwai a filin jirgi

    Tauraron ɗan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang ya soki hukumar ƙwallon ƙafar Afirka (Caf) bayan abin da ya kira "tsarewa" da aka yi wa tawagar ƙwallon ƙafar ƙasarsa ta Gabon a filin jirgin sama na Gambia.

    Aubameyang ya tafi ƙasarsa ne ta Yammacin Afirka tare da abokan wasansa domin buga wasan neman shiga Gasar Kofin Afirka da Kamaru za ta karɓi baƙunci.

    Sai dai tawagar wadda ta ƙunshi Mario Lemina na Fulham da tsohon ɗan tsakiyar Sunderland Didier Ndong, ta shafe awa shida a tsare a Banjul International Airport bayan an karɓe fasfo ɗinsu.

    Aubameyang ya yi ta wallafa abin da ke faruwa a shafukan zumunta, inda yake mamakin ko an "an yi garkuwa da su ne".

    An yaɗa hotunan 'yan wasan suna barci a ƙasa bayan sun gaji da jira, waɗanda aka ce an tsare su ne tun 11:00 na dare har zuwa 6:00 na safe agogon ƙasar.

  16. An saki sakamakon jarrabawar kammala firamare a Najeriya

    Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta saki sakamakon jarrabawar kammala makarantun firamare ta National Common Entrance Examination.

    Jarrabawar wadda National Examinations Council (NECO) ke shiryawa, da ita ne ɗalibai za su samu damar shiga kwalejojin Gwamnatin Tarayya guda 110 da ake kira Unity Schools a faɗin ƙasar.

    Ɗalibi 92,591 ne suka yi rajistar jarrabawar da aka yi ranar 17 ga watan Oktoba, amma 70,580 ne suka rubuta ta, yayin da 16,714 ba su zauna ba, a cewar rahoton Daily Trust.

    Da suke gabatar da sakamakon a Abuja, shugaban hukumar NECO Godwill Obiom da Ministan Ilimi Adamu Adamu sun ce an gudanar da jarrabawar salin-alin ƙarƙashin kulawar masu sa-ido na ciki da wajen hukumar.

    Ɗalibin da ya fi ƙoƙari ya fito ne daga Jihar Anambra da maki 199 cikin 100, na biyun kuma daga Imo da maki 198, sai kuma na uku daga Ogun, inda ya samu maki 197.

  17. Sudan da Masar sun fara atisayen soji na haɗin gwiwa

    Sudan da Masar sun fara wani atisayen sararin samaniya, wanda suka yi wa laƙabi da Nile Eagles 1, a sansanin sojojin sama na Merowe da ke kudancin Sudan.

    Atisayen haɗin gwiwar zai ci gaba har nan da ranar 26 ga watan Nuwamba.

    Wannan ne atisayen soji na farko tsakanin ƙasashen da ke makwabtaka da juna da ke arewacin Afrika tun bayan lokacin tsohon shugaban Sudan Jaafar al-Nimeri a 1970.

    Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Masar ta fitar, ta ce atisayen zai mayar da hankali kan abubuwa da yawa ciki har da yadda za a koyi kare kai da kuma kai hari da jiragen sojin saman ƙasashen za su riƙa yi.

    Shugaban sojin Sudan da na Masar sun yi wata tattaunawa a ranar Lahadin 31 ga watan Oktoba a Khartoum, babban birnin Sudan, inda suka cimma yarjejeniyar bunƙasa harkokin sojinsu.

    Wannan atisayen na zuwa ne bayan tattaunawar zaman lafiya tsakanin kasashen Sudan da Masar da Kuma Habasha kan aikin Kogin Nilu ta tashi ba tare da cimma komai ba.

  18. Firaministan Eswatini ya kamu da cutar korona

    Firaministan Eswatini, Ambrose Dlamini, ya kamu da cutar korona.

    A jiya Lahadi ne firaministan ya ce ya kamu da cutar kuma ya killace kansa a gida, yana mai cewa bai fara nuna alamunta ba tukunna.

    An yi wa dukkanin na kusa da firaministan gwaji kuma sun killace kansu.

    An yi wa mutum 384 gwajin cutar ranar Lahadi kuma biyu ne suka kamu da ita, a cewar wata sanarwa daga ma'aikatar lafiya.

    Jumillar mutum 6,095 ne suka kamu da korona a Eswatini, 119 daga ciki sun mutu.

  19. Ɓarayi ne suka mamaye gwamnatin Buhari – Ali Ndume

    Sanata Ali Ndume mai wakiltar Mazaɓar Borno ta Kudu ya ce "ɓarayi" na cin amanar Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya "saboda su ne mafiya yawa a gwamnatinsa".

    Da yake magana a cikin shirin Sunday Politics na kafar Channels TV, sanatan ya ce duk da cewa Buhari ya yi bakin ƙoƙarinsa, akwai mutanen da ke yi wa gwamnatinsa zagon ƙasa.

    Da aka tamnbaye shi ko maki nawa zai bai wa gwamnatin jam'iyyarsu ta APC bayan shafe shekara biyar a kan mulki, sai ya ce: "Magana ta gaskiya ba na jin daɗin yadda gwamnatin nan ke tafiya.

    "Babban abin baƙin ciki shi ne, akwai abubuwan da suke faruwa waɗanda bai zama dole sai sun faru ba. Sau uku muna ƙoƙarin ɗaura shugaban ƙasa [Buhari] a kan mulki ba mu yi nasara ba, amma muka yi nasara a karo na uku.

    "Na san Buhari mutumin kirki ne da ke son cigaban talakawa. Sai dai ɓarayi ne suka mamaye gwamnatin, abin da ya sa suke cin amanar tsare-tsaren da yake so ya gudanar."

  20. Cutar korona na kashe mutum fiye da 1,000 kullum a Amurka

    Jihohin Michigan da Washington ne na baya-bayan nan a Amurka da suka saka tsauraran dokoki da zummar daƙile yaɗuwar cutar korona.

    Makarantun sakandare da kwalejoji za su kasance a rufe - sai dai karatu daga gida - da gidajen cin abinci, inda aka hana cin abinci a wurin a Jihar Michigan daga Laraba mai zuwa.

    Kazalika, an hana cin abinci a wuraren abincin a Washington. Wuraren motsa jiki da sinimomi da wuraren kallon kayan tarihi za su kasance a rufe.

    Adadin waɗanda suka kamu da cutar a Amurka sun kai miliyan 11, yayin da aka samu adadi mafi yawa na waɗanda ake kwantarwa a asibiti.

    Adadi na tsakatsaki, fiye da mutum 1,000 ne ke mutuwa a kullum sakamakon cutar kuma jumillar waɗanda suka mutun sun kusa 250,000.

    Gwamnatin Donald Trump ta yi albishirin cewa tana fatan fara raba rigakafin cutar da aka amince da shi nan da watan Disamba – duk da cewa har yanzu ba a amince da shi ba a hukumance.