Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Biden da Kamala sun fara shirye-shiryen karɓar mulki

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan zaben Amurka da ma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin:

    • Firaiministan Ethiopia ya sallami manyan jami'an gwamnatinsa
    • Donald Trump ya ƙi amincewa da shan kaye
    • Yadda ake shirye-shiryen bikin miƙa wa sabon Sarkin Zazzau sandar girma
    • Biden da Kamala sun buɗe sabon shafin Twitter na shirye-shiryen karɓar mulki
    • An rantsar da sabon shugaban ƙasa a Bolivia
    • Joe Biden ya fara ranarsa ta farko a matsayin zaɓaɓɓen shugaba da kai ziyara coci
    • Tsohon Shugaban Amurka George W Bush ya yi wa Biden murnar lashe zaɓe

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. Lahadi ta 13 kenan ana zanga-zangar neman shugaban Belarus ya yi murabus

    A yau, Lahadi ta 13 kenan a jere, ana gudanar da zanga-zangar nuna ƙin jinin Shugaban Belarus, Alexander Lukashenko.

    Jami'an tsaro a gefe ɗaya kuma na ci gaba da kama masu zanga-zangar.

    Wata uku kenan yanzu, al'ummar kasar Belarus na neman shugaba Alexander Lukashenko ya sauka daga mukaminsa - sai dai har yanzu haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.

    Wata kungiya da ke bibiyar abin da ke faruwa a kasar ta ce, an kama sama da mutum 500, kuma mafi yawansu a babban birnin ƙasar Mink.

    Wani bidiyo da ke yawo a intanet ya nuna yadda wasu mutane ke dukan waɗanda ake tsare da su da kulake.

  3. Tsohon Shugaban Amurka George W Bush ya yi wa Biden murnar lashe zaɓe

    Tsohon Shugaban Amurka George W Bush, ya yi wa Joe Biden murnar lashe zaben Amurka.

    Ya bayyana cewa mutanen Amurka na da yaƙinin zaɓen da aka yi a ƙasar zaɓe ne na gaskiya kuma sakamakon zaɓen ya nuna hakan.

    Ya kuma yaba wa abokin takarar Mista Biden, Donald Trump kan jajircewar da ya yi wurin yaƙin neman zaɓe da kuma samun ƙuri'un Amurkawa sama da miliyan 70 a zaɓen gama gari.

    Har yanzu dai Shugaba Trump ya ƙi fitowa ya amince da sakamakon zaben inda yake ci gaba da wallafa saƙonni a shafinsa na Twitter inda yake zargin an yi masa ƙwace a zaɓen.

    Mista Trump bai kawo wasu gamsassun hujjoji ba da za su iya kare iƙirarinsa, amma dai ya nuna nuna yatsa ga ƙuri'un da aka kaɗa ta hanyar akwatin gidan waya a birane irin su Philadelphia da kuma Detroit.

    Manyan jiga-jigan Jam'iyyar Republican sun yi shiru kan batun zaɓen, amma wani rahoton da wata kafar yaɗa labarai ta Amurka ta yi ya nuna cewa surukin Mista Trump kuma mai ba shi shawara, Jared Kushner ya yi ƙoƙarin shawo kan Mista Trump ɗin na ya karɓi sakamakon zaɓen.

  4. Joe Biden ya fara ranarsa ta farko a matsayin zaɓaɓɓen shugaba da kai ziyara coci

    Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka, Joe Biden, ya fara ranarsa ta farko a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka da zuwa coci a safiyar Lahadi.

    Mista Biden ɗin ya samu rakiyar iyalansa a safiyar zuwa cocin St Joseph da ke kusa da mahaifarsa da ke Wilmington a jihar Delaware.

    A makabartar da ke cocin ne aka binne ɗansa Beau Biden, a 2015 bayan ya yi fama da cutar kansar ƙwaƙwalwa.

    Wani jami'in tsaro ya tsaya a wajen cocin yayin da shugaban da mutanen cocin ke gudanar da addu'o'i.

    A yanzu dai, Mista Biden zai zama shugaban Amurka na biyu mai bin aƙidar ɗarikar Katolika bayan John F Kennedy.

    An bayyana cewa zaɓaɓɓen shugaban mai shekara 77 na da riƙon aƙidarsa ta Katolika kuma yana yawan zuwa taron coci.

    A ranar Litinin, Mista Biden ɗin zai bayyana mambobin kwamitin da zai kafa na yaƙi da annobar korona - wanda shi ne babban ƙalubalen da ke gabansa a yanzu.

  5. Sama da 'yan ci-rani 1,600 daga Afrika aka ceto ko kuma suka tsallaka tsibirin Canary

    Hukumomin ba da agajin gaggawa a Sifaniya sun ce, akwai 'yan ci-rani sama da dubu 1,600 da suka fito daga Afrika da walau sun isa tsibiran Canary ko kuma an samu su ceto a teku cikin 'yan kwanakin nan na karshen mako.

    An bayyana cewa sun yin tafiyar ne kan wasu kwale-kwale masu haɗari, da ka iya nutsewa a teku.

    Mai magana da yawun ma'aikatar, ya ce an gano gawar mutum ɗaya kusa da tsibirin El Hierro.

    A watannin baya-bayan nan, ana fuskantar ƙaruwar 'yan ci rani daga Afrika ta yamma da ke ƙoƙarin tsallakwa tsibirin Canary.

  6. An rantsar da sabon shugaban ƙasa a Bolivia

    An rantsar da sabon shugaban ƙasar Bolivia, Luis Arce a La Paz. Sarki Felipe na Sifaniya da shugabannin ƙasashen da ke yankin Kudancin Amurka sun halarci bikin, inda aka rantsar da shugaban shekara ɗaya bayan shugaba Evo Morales ya yi murabus.

    An ɗage zaɓen zagaye na biyu sau da dama a ƙasar sakamakon annobar korona.

    Mista Morales ya yi gudun hijira yayin da aka shafe makonni ana zanga-zanga kan zargin da ake yi masa na almundahana a lokacin zaɓe.

    Ya bayyana cewa zai dawo Bolivia a ranar Litinin. Luis Arce ya kasance ministan kula da tattalin arziƙi a lokacin mulkin Mista Morales.

    Sabon shugaban ƙasar ya bayyana cewa Mista Morales bai da wani gurbi a gwamnatinsa ba kuma ba za a dama da shi ba.

  7. Biden da Kamala sun buɗe sabon shafin Twitter na shirye-shiryen karɓar mulki

    Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Haris ba su tsaya wata-wata ba inda tuni suka buɗe sabon shafin Twitter da zai mayar da hankali wurin shirye-shiryen karɓar mulki.

    Sunan shafin @Transition46 - ma'ana dai yana nufin shirye-shiryen miƙa mulki ga shugaban ƙasar Amurka na 46.

    Tuni suka fara wallafa saƙonni da suka shafi karɓar mulkin da kuma wasu manufofin da suka sa a gaba.

    Haka kuma, sun buɗe wani shafi na intanet wanda ke ƙunshe da shirye-shiryen da za su tabbatar an miƙa mulki ciikin nasara daga gwamnatin Trump zuwa ta Mista Biden.

  8. Yadda ake shirye-shiryen bikin miƙa wa sabon Sarkin Zazzau sandar girma

  9. Daular Larabawa za ta riƙa yanke hukuncin kisa ga masu kashe 'mata masu jawo abin kunya'

    Gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ƙara tsaurara hukunci kan kisan da dangi ke yi wa mata a ƙasar a yunƙurin yin garambawul ga dokokin ƙasar.

    Gwamnatin ƙasar ta ce za ta soke dokar da ta bai wa alƙalai damar yanke hukunci mai sauƙi kan irin wannan kisan.

    Akasari, ana kashe matan ne sakamakon zargin da ake yi musu na janyo abin kunya ga zuri'a ko kuma danginsu baki daya.

    Karanta cikakken labarin a nan:

  10. Donald Trump ya ƙi amincewa da shan kaye

    Har yanzu Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙi fitowa ya yarda cewa ya sha kaye a zaɓen ƙasar da Joe Biden ya samu nasara.

    Sai dai shugaban na ci gaba da wallafa saƙonni a shafinsa na Twitter inda yake iƙirarin an yi masa ƙwace, wanda hakan ya sa shafin na Twitter ya yi wa Trump gargaɗi kan kalamansa.

    Mista Trump bai kawo wasu gamsassun hujjoji ba da za su iya kare iƙirarinsa, amma dai ya nuna nuna yatsa ga ƙuri'un da aka kaɗa ta hanyar akwatin gidan waya a birane irin su Philadelphia da kuma Detroit.

    Manyan jiga-jigan Jam'iyyar Republican sun yi shiru kan batun zaɓen, amma wani rahoton da wata kafar yaɗa labarai ta Amurka ta yi ya nuna cewa surukin Mista Trump kuma mai ba shi shawara, Jared Kushner ya yi ƙoƙarin shawo kan Mista Trump ɗin na ya karɓi sakamakon zaɓen.

    Kwamitin yaƙin neman zaɓe na Mista Trump ɗin da kuma lauyoyin Jam'iyyar Republican sun fara kai ƙara kan zaɓen tun a makon da ya gabata domin ƙalubalantar zaɓen, sai dai kotun ta yi watsi da zarge-zarge da dama.

  11. Sabbin tsare-tsare uku da gwamnatin Najeriya ta yi wa 'yan gudun hijra

    Shugaban hukumar 'yan gudun hijra ta Najeriya, Sanata Bashir Garba Muhammad, ya ce yanzu haka ya fito da wasu tsare-tsare guda uku domin inganta rayuwar 'yan gudun hijrar Najeriya.

    Ya ce "akwai 'yan gudun hijira miliyan 2.5 da suke cikin Najeriya sakamakokn rikicin Boko Haram da ɓarayin daji, inda kuma mutum kimanin dubu 400 suka ƙetara kasashe masu makwabtaka wato Nijar da Kamaru da Tchadi domin neman mafaka."

    Sanata Bashir ya kara da cewa, akwai sansanonin 'yan gudun hijira fiye da 200 a faɗin Najeriya sannan kuma akwai 'yan gudun hijirar da suka shiga cikin al'umma da ba su da ƙididdigarsu.

  12. Firaiministan Ethiopia ya sallami manyan jami'an gwamnatinsa

    Firaiministan Habasha, Abiy Ahmed, ya kori manyan jami'an gwamnatinsa a yayin da ake ci gaba da rikici a yanking Tigray.

    Cikin wadanda aka sallama, har da Shugaban sojojin ƙasa na ƙasar da kuma shugaban hukumar tattara bayanan sirri da ministan harkokin wajen ƙasar, inda tuni aka maye gurbinsu da wasu sabbi.

    An bayar da rahoton cewa an kashe mutane da dama a yayin rikicin, inda kuma mayaƙan da suka samu rauni tuni aka kai su asibiti a yankin Amhara da ke makwaftaka da Tigray ɗin.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa an samu arangama tsakanin dakarun tarayyar ƙasar da kuma dakarun na yankin Tigray a wurare daban-daban har guda takwas.

    Ta kuma bayyana cewa mutum miliyan tara na ckikin barazanar rasa muhallinsu a sakamakon rikicin da ke faruwa.

    An kuma bayyana cewa ba a iya kai kayan agaji yankin na Tigray sakamakon an rufe iyakokin shiga.

  13. Za a fara rigakafin cutar shawara a Jihar Delta bayan mutuwar mutum 35

    Gwamnatin Tarayyar Najeria za ta fara gudanar da dubban rigakafin cutar shawara a Jihar Delta da ke kudancin ƙasar bayan cutar ta haddasa mutuwar mutum 35 a jihar.

    Wata sanarwa da hukumar lafiya a matakin farko ta Najeriya ta fitar a yau Asabar ta bayyana cewa za a gudanar da rigakafin ne ta hannunta tare da haɗin giwar gwamnatin Delta.

    A ranar 24 ga watan Yuli ne aka samu rahoton mutum na farko da ya kamu da wata cuta kuma ta yi ajalinsa, wadda daga baya ta yi ajalin ƙarin mutum 34 a Ƙaramar Hukumar Ika North East.

    An samu ɓullar cutar a Jihar Enugu ma, inda ta halaka mutum kusan 57.

    Gwajin da hukumomi suka yi ya nuna cewa cutar shawara ce ta kashe mutanen, wadda ake kira Yellow Fever a Turance.

    Hukumar NPHCDA ta ce akasarin waɗanda suka kamu da cutar matasa ne 'yan shekara 18 zuwa 25 kuma tuni aka ɗauki samfurin jinin mutum takwas, inda gwaji ya nuna cewa uku daga cikin shida da aka gwada suna ɗauke da cutar ta shawara.

  14. Su wane ne ba su taya Biden murna ba har yanzu?

    Shugabannin ƙasashen duniya na ci gaba da taya Joe Biden murnar lashe zaɓen Amurka - Muhammadu Buhari, Boris Johnson, Benjamin Netanyahu, Nerandra Modi duk sun taya shi zakwaɗi.

    Amma Andres Manuel Lopez Obrador na Mexico ya ce ya yi wuri ya taya Biden murna kuma zai jira har sai an sasanta "dukkanin shari'o'i" da aka shigar kan sakamakon zaɓen.

    To su wane ne kuma sauran manya-manya da ba a ji ɗuriyarsu ba har yanzu? Ga wasu daga cikinsu, waɗanda babu mamaki suna shirya abin da za su ce ne:

    • Kim Jong-un na Koriya ta Arewa
    • Masarautar Saudiyya
    • Xi Jinping na China
    • Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya
    • Jair Bolsonaro na Brazil
    • Viktor Orban na Hungary
  15. Jihohin da har yanzu ba su faɗi sakamako ba

    BBC ta sanar da nasarar Joe Biden ranar Asabar ne bayan ya lashe Jihar Pennsylvania wadda ta cikasa masa maki zuwa 270 na ƙuri'un wakilan zaɓe da ake buƙata. Daga baya kuma aka hasaso ya lashe Nevada ma.

    Sai dai sakamakon ba na hukuma ba ne, an samo su ne daga jihohin da suka gama ƙirga ƙuri'a da kuma na Jihar Wisconsin da har yanzu ake cigaba da ƙirgawa.

    Pennsylvania da Wisconsin da Michigan ne kaɗai jihohin da suka juya wa jam'iyyar Republican baya a wannan shekara zuwa Democrat.

    Amma har yanzu muna jiran sakamako daga jiha huɗu - kuma babu mamaki a samu ƙarin waɗanda za su juya baya daga wata jam'iyyar zuwa wata.

    • Alaska - Donald Trump ne kan gaba da kashi 63% saɓanin na Biden mai 33% bayan an ƙirga kashi 56% na baki ɗayan ƙuri'un. Trump ne ya lashe Alaska a 2016
    • North Carolina - Trump ne kan gaba da kashi 50% saɓanin na Biden da ke da 48.6%. An ƙirga kashi 98% na ƙuri'un kuma Trump ne ya ci jihar a 2016
    • Arizona - Biden ne kan gaba da kashi 49.5%, inda Trump ke da 48.9% bayan an ƙirga kashi 97% na ƙuri'un. Idan Biden ya lashe ta, hakan zai zama juya baya zuwa ga Democrat saboda Trump ne ya ci a 2016
    • Georgia - A nan ma Biden ne kan gaba da 'yar tazara ta kashi 49.5%, Trump na da 49.3% bayan an ƙirga kashi 99% na ƙuri'u. A nan ma, Trump ne ya lashe ta a 2016

    Yayin da duk wannan ke faruwa, Trump ya sha alwashin ƙalubalantar sakamakon a gaban kotu a jihohi da dama.

    Da ma tuni hukumomi suka yanke shawarar sake ƙirga ƙuri'u a Georgia, inda tazara tsakanin 'yan takarar ta yi kusa sosai, kuma haka Trump ke so a yi a Wisconsin ma.

  16. ''Yan daba sun saci bindigar AK-47 guda 100 a Legas yayin zanga-zangar EndSars'

    Kwamitin bincike da Sufeto Janar Mohammed Adamu ya kafa domin bincike kan ɓarnar da aka yi wa rundunar 'yan sandan Najeriya a zanga-zangar EndSars ya ce an sace bindigar Ak-47 kusan 100, a cewar jaridar Punch.

    Shugaban kwamitin mai mamba 10, CP Yaro Abutu, ya shaida wa jaridar a yau Asabar cewa baya ga bindigogin, an kuma saci harsashi guda 2,600 yayin tashin hankalin da ya ɓarke sakamakon zanga-zangar.

    Ya ƙara da cewa an kai hari tare da lalata wuraren 'yan sanda guda 37 a jihar. Kazalika, an lalata abin hawansu guda 367, ciki har da motar silke 10 da kuma ƙanana da ƙirar Hilux na fita fatro.

    Shugaban kwamitin ya ce suna kuma tattara asarar da 'yan sandan suka yi a ƙasa baki ɗaya.

    Jaridar ta Punch ta ce kwamitin zai miƙa rahotonsa ga IGP Mohammed Adamu nan da mako uku.

    Abutu ya koka cewa "abin takaici ne yadda aka aikata ta'asar a ƙarshen shekara, lokacin da aka fi aikata laifuka a faɗin Najeriya".

    "Muna duba abubuwan da suka faru a jiha 17 da aka ƙona ofisoshi da kuma kisan 'yan sanda. Tun da Legas ce cibiyar zanga-zangar, shi ne muka yanke shawarar fara zuwa nan.

    "Ofishin 'yan sanda 37 aka kai wa hari a Legas kuma an gurgunta kusan kashi 30 cikin 100 na ayyukan 'yan sandan a jihar."

  17. Ranar Litinin Biden zai naɗa 'yan kwamitin yaƙi da korona

    A jawabinsa na samun nasarar zaɓe, zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden ya ce a gobe Litinin zai bayyana sunayen 'yan kwamitin yaƙi da annobar cutar korona na sabuwar gwamnatinsa.

    Da ma tun da ranar Lahadi ya bayyana wa magoya bayansa cewa kawo ƙarshen cutar ne zai zama matakin farko da zai ɗauka.

    Kwamitin mai mamba takwas zai ƙunshi masana harkokin lafiya domin daƙile yaɗuwar cutar da tuni ta halaka fiye da mutum 200,000 a Amurka.

    Cikin kwana huɗu a jere, an samu sabbin waɗanda suka kamu da cutar fiye da mutum 110,000 a rana guda.

    Jumillar waɗanda suka kamu da cutar a Amurka sun kai kusan miliyan 10.

  18. Cutar shawara ce ta haddasa mace-mace a Jihar Enugu - Kwamishinan lafiya

    Gwamnatin Jihar Enugu da ke kudancin Najeriya ta tabbatar cewa cutar shawara ko kuma Yellow Fever a Turance, ita ce ta haddasa mace-macen da aka samu a yankin Enugu Ezikeda na Ƙaramar Hukumar Igbo-Eze.

    Tabbacin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Lafiya na Jihar Dr. Ikechukwu Obi ya aike wa manema labarai ranar Asabar.

    Cutar wadda ta ɓarke a watan Oktoba, ta yi sanadiyyar mutuwar kusan mutum 57 a jihar.

    Kwamishinan ya ce an samu tabbacin hakan ne bayan gwajin da aka gudanar. Ya ƙara da cewa cutar shawara ba baƙuwa ba ce a Najeriya.

    A cewarsa: "Alamun cutar na farawa ne ga duk wanda ya kamu da zazzaɓi lokaci guda ko kuma idanunsa suka yi kalar ruwan dorawa cikin kwana 14, kuma ana gane ta ne ta hanyar yin gwaji."

    Ya ci gaba cewa: "Ma'aikatar Lafiyar Jihar Enugu ta kira taron gaggawa a safiyar yau (Asabar) da ƙarfe 10:00 daga hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta NCDC da sauran abokan hulɗa a jihar domin cimma matakan da za a ɗauka na gaba da zummar shawo kan cutar da hana ta yaɗuwa a sassan jihar."

  19. Magoya bayan Trump na zanga-zanga

    Magoya bayan Donald Trump sun hau tituna awanni bayan sanar da nasarar Joe Biden.

    Har yanzu shugaban bai amsa shan kaye ba ko kuma magana a bainar jama'a tun bayan rashin nasarar tasa - a lokacin da yake buga wasan Golf.

    Akasarin waɗanda suke zanga-zangar sun yarda da iƙirarin da Trump ke yi cewa an yi maguɗi a zaɓen - wanda ba shi da wata hujja - amma fa ba duka magoya bayansa ne suka yarda da hakan ba.

  20. Idan yanzu kuka farka...ga abin da ya kamata ku sani

    • Yayin jawabinsa na farko bayan nasarar da ya samu a zaɓen shugaban Amurka, Joe Biden ya ce yanzu lokaci ne na samun waraka. Biden ya faɗa wa magoya bayansa cewa kawo ƙarshen annobar korona ya sa a gaba yanzu. Ya ce gwamnatinsa za ta nuna dattako da adalci da kimiyya da kuma ƙwarin gwiwa.
    • Kamala Harris, abokiyar takarar Biden, ta gode masa bisa ƙwarin gwiwar da ya nuna wurin zaɓar mace a matsayin mataimakiyarsa. Ta jaddada cewa masu zaɓe sun yaye labulen wata sabuwar rana a Amurka.
    • Ana ci gaba da murna a biranen Amurka har cikin dare. An shirya wata walima ko kuma fati a kusa da Fadar White House yayin da magoya bayan Biden ke kade-kade da raye-raye da ihun cewa "Mu ne zakaru".
    • Wasu kuma sun hau tituna a biranen New York da Chicago da Philadelphia da Los Angeles duka domin yin murna.
    • Har yanzu Donald Trump bai amsa shan kaye ba, bai ma ce komai ba a bainar jama'a tun bayan sanar da nasarar Biden a jiya Asabar. Sai dai ya haƙiƙance cewa shi ne ya lashe zaɓen.