Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Biden da Kamala sun fara shirye-shiryen karɓar mulki

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan zaben Amurka da ma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Yadda sakamakon yake a yanzu

    Idan ba ku manta ba, an sanar da Joe Biden ne a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban Amurka saboda ya samu ƙuri'a 270 ta wakilan zaɓe na musamman, shi kuma Trump yana da 214 a lokacin.

    Saboda haka, har yanzu ba a gama ƙirga ƙuri'u ba a wasu jihohin, abin da ya sa har yanzu za a ci gaba da samun ƙaruwar adadin sakamakon.

    A gobe Litiinin ne kuma Shugaba Trump zai kai wata ƙara a gaban kotu domin ƙalubalantar sakakamakon zaɓen.

  2. Shugabannin duniya na bayyana mabambantan ra'ayoyi kan nasarar Biden

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya - kasa mafi yawan al'umma a Afirka - ya mika sakon murna ga Joe Biden, yana mai fatan ganin alaka ta inganta tsakanin Amurka da Nahiyar Afirka baki ɗaya.

    Shugaban Mexico, Andres Manuel Lopez Obrador ya ki taya Biden murna yana mai cewa sai an kammala ƙararrakin da ke gaban kotu tukunna.

    Ayatollah Ali Khamenai na Iran ya ce babu wani sabon abu ko sauyi a sakamakon zaɓen.

    Shugaba Moon Jae-In na Koriya ta Kudu na cikin shugaban ƙasa na baya-bayanan da ya mika sakon taya murna ga zababben shugaba Joe Biden.

    Firaministan Japan Yoshihide Suga ya ce yana son aiki da gwamnatin Biden domin tabbatar da zaman lafiya da ƴanci da wanzuwa a yankin Pacific.

    Shugabannin Tarayyar Turai sun ce suna fatan karfafa alakarsu da Amurka.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, daya daga cikin makusantan Trump mafi karfi, bai ce uffan ba har yanzu.

  3. Cutar korona ba ta halaka kowa ba ranar Asabar a Najeriya

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu karin mutum 59 da suka kamu da cutar korona a ranar Asabar a ƙasar.

    Labari mai dadi shi ne, babu wanda ya rasu sakamakon cutar ranar Asabar.

    Da wannan sabbin alkaluman jimillar wadanda cutar ta kama a ƙasar sun kai 63,790, an kuma sallami mutum 59, 884 sai kuma mutum 1,154 da suka mutu.

    Jihar Kaduna ita ce mai adadi mafi yawa da mutanen 28 da suka kamu a ranar Asabar , sai Rivers mai mutum 9, Ogun da Ondo na da mutum 8-8 da suka kamu da cutar ranar Asabar.

    Jihohin Kano da Neja na da mutum 2-2, yayin da Kwara da Plateau ke da mutum dai-dai da suka kamu da cutar.

  4. Maraba

    Barkammu da hantsin Lahadi, da fatan an tashi lafiya

    Umar Mikail ne ke tare da ku a wannnan safiya domin kawo labarai da rahotanni game da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Sai dai za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da Nijar da makwabtansu.

    Ku biyo ni. Na gode.