Shugaban ma'aikatan Fadar White House ya kamu da korona
Idan daga barci kuka taso - indai ba da waya kuka farka a hannu ba - ba ku da labarin cewa Shugaban Ma'aikatan Fadar White House ya kamu da cutar korona.
Mark Meadows ne na baya-bayan nan daga cikin na kusa-kusa da Shugab Donald Trump da ya harbu da cutar.
Ya zuwa yanzu ba a san yadda aka yi Meadows ya kamu da cutar ba, amma ya sha fita bainar jama'a ba tare da takunkumi ba a fuskarsa.
Cutar ta halaka fiye da mutum 230,000 a Amurka sannan a ranar Juma'a kaɗai an samu ƙarin 127,000 da suka kamu da ita, abin da ya sa jumillarsu ta kai kusan miliyan 10.