Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Shin Trump zai ƙalubalanci Biden a Kotu?

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan zaben Amurka da ma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Lahadi idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan hafin:

    • Trump ya ce akwai 'babban taron' manema labarai a Pennsylvania
    • Joe Biden ya lashe zaɓen Amurka
    • Shin Trump zai ƙalubalanci Biden a Kotu?
    • Dubban mutane na zanga-zangar ƙin jinin Faransa a Senegal
    • Me Trump ya ce bayan Biden ya sha gabansa?

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. Dubban mutane na zanga-zangar ƙin jinin Faransa a Senegal

    Dubban mutane ne ke zanga-zanga a titunan Dakar babban birnin Senegal inda suke nuna rashin goyon bayansu kan zanen ɓatancin da Mujallar Faransa ta yi ga Annabi Muhammad (SAW), da kuma yadda Shugaban Faransar Emmanuel Macron ya goyi bayan Mujallar.

    Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun cinna wa tutar Faransa wuta da kuma hotunan Mista Macron.

    Masu zanga-zangar kuma na kira da a ƙaurace wa kayayyakin da Faransar ke sayarwa.

    A watan da ya gabata, Mista Macron ya ya kare batun 'yancin faɗin albarkacin baki da kuma bayyana ra'ayi a yayin da yake jawabi a taron tunawa da wani malami da aka fille wa kai bayan ya nuna wa ɗalibansa zanen ɓatanci da aka yi game da Annabi.

    Kashi 95 cikin 100 na mutanen Senegal Musulmai ne, kuma ƙasar na da alaƙa mai ƙarfi da ƙasar Faransa wadda ita ce ta 'yanta su

  3. Labarai da dumi-dumi, Joe Biden zai yi wa Amurkawa jawabi da dare

    Zaɓaɓen Shugaban Amurka, Joe Biden, zai yi jawabi a daren yau daga hedikwatar yaƙin neman zaɓensa da ke Wilmington a Jihar Delaware da misalin 20:00 agogon ƙasar, ƙarfe 01:00 kenan agogon GMT.

    Mai ɗakinsa Jill Biden za ta raka sa wurin da zai yi jawabin, kamar yadda kwamnitin yaƙin neman zaɓen nasa ya bayyana.

    Hakazalika, Zaɓaɓɓiyar Mataimakiyar Shugaban Amurkar, Kamala Harris, za ta halarci wurin tare da mai gidanta Doug Emhoff, sai dai babu wani tabbaci ko ita ma za ta yi wani jawabi.

  4. Me Trump ya ce bayan Biden ya sha gabansa?

    Donald Trump ya samu labarin nasarar da Biden ya samu yana cikin buga wasan lambu ko kuma Golf a filin wasansa da ke Jihar Virginia a ƙasar.

    A martanin da ya mayar, Shugaba Trump ya ce " mun san cxewa Joe Biden na sauri ya ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa na ƙarya, haka kuma abokansa 'yan jarida na tayasa: ba su so a faɗi gaskiya," in ji shi.

    Mista Trump din ya sha alwashin daga gobe Litinin lauyoyinsa za su fara shiga kotu domin gabatar da ƙara kan zaɓen na Amurka.

    A wani zargi da Mista Trump ɗin ya yi wanda bai da tushe, ya ce kwamitin yaƙin neman zaɓen Mista Biden "na son a ƙirga ƙuri'u ko da na bogi ne ko kuma waɗanda ba su cancanta su yi zaɓe ba ko kuma ƙuri'un matattu".

  5. Shin Trump zai ƙalubalanci Biden a Kotu?

    A 'yan kwanakin nan, a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙirga ƙuri'un zaɓen Amurka, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wasu kalamai marasa tushe inda ya ce an yi "maguɗin" zaɓe kuma ya sha alwashin zuwa kotu.

    Kalaman nasa sun bar jama'a cikin duhu. Shi da kwamitin yaƙin neman zaɓensa sun kai ƙara kotu a wasu jihohin ƙasar, ciki har da Michigan da Pennyslyvania inda ya buƙaci a dakatar da ƙirga ƙuri'u, amma alƙalan sun yi watsi da buƙatar su.

    Babban ƙalubale a Pennsylvania shi ne matakin da jihar ta ɗauka na ƙirga ƙuri'un da suka iso ranar zaɓe amma tun tuni an aiko su ne su iso ranar zaɓe sai suka makara iso wa. 'Yan Jam'iyyar Republican na ƙalubalantar wannan mataki.

    A jihar Wisconsin, kwamitin yaƙin neman zaɓen Mista Trump ya buƙaci a sake ƙirga ƙuri'un da aka jefa a jihar sakamakon "wasu abubuwa da ba daidai ba da aka gani" a ranar Laraba.

    Haka ma a hihar Georgia, 'yan Jam'iyyar Republican na jihar da kuma kwamitin yaƙin neman zaɓen Mista Trump sun gabatar da ƙara a gaban kotu domin dakatar da ƙirga ƙuri'u sinda suke zargin aka matsala wurin ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa ta hanyar gidan waya.

  6. Trump ya ce 'shi ya ci zaɓe'

    Jim kaɗan bayan Joe Biden ya bai wa Mista Trump tazara mai yawa da ke alamta Biden ɗin ya ci zaɓe, Mista Trump ɗin ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Twitter inda ya ce shi ya ci zaɓen da ƙuri'u masu yawa.

    Sai dai shafin na Twitter ya saka alamar gargaɗi a ƙarƙashin saƙon da Mista Trump din ya wallafa.

    Abin jira a gani a yanzu shi ne ko Mista Trump ɗin zai yi wa Mista Biden murnar lashe zaɓe idan aka sanar a hukumance kan cewa shi ya lashe zaɓen? Lokaci ne kaɗai zai iya tabbatar da hakan

  7. Labarai da dumi-dumi, Joe Biden ya lashe zaɓen Amurka

    Ɗan takarar Jam'iyyar Democrat a zaɓen Amurka Joe Biden ya lashe zaɓen Amurka inda a halin yanzu ya samu kur'iu 273, abokin karawarsa kuma Donald Trump na da 214.

    A yadda tsarin zaɓen Amurka yake, duk wanda ya fara samun ƙuri'un wakilai na musamman da ke zaɓe har 270, shi ya samu nasara a zaɓen ƙasar.

    A nasarar da Mista Biden ya samu a jihar Pennsylvania, hakan na nufin ya ci zaɓen Amurka domin kuwa ya samu ƙarin ƙuri'u 20 daga wakilai na musamman masu zaɓe, wanda hakan ya sa ya samu ƙuri'u 273, ya ma wuce 270 ɗin da ake buƙata.

    Sai dai da alamu Trump ɗin na da niyyar maka Mista Biden ɗin ƙara a kotu biyo bayan wasu zarge-zargen da Trump ɗin ya fara tun a ranar zaɓen inda yake zargin an yi maguɗi, zargin da har yazu bai kawo gamsashiyyar hujja a kai ba.

    A ƙarƙashin tsarin zaɓen Amurka, masu zaɓe suna zaɓar wakilai na musamman waɗanda ke haɗuwa makonni kaɗan su kaɗa ƙuri'a domin tantance wanda zai zama shugaban ƙasa.

  8. Trump ya ce akwai 'babban taron' manema labarai a Pennsylvania

    Shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da cewa akwai wani babban taron manema labarai anjima a Philadelphia, wanda shi ne birni mafi girma a Jihar Pennsylvania.

    A wani saƙo da ya wallafa a baya, wanda tuni aka goge shi, ya bayyana cewa lauyoyi ne za su yi taron.

    Ya bayyana cewa za a yi taron ne da misalin 11:30 agogon ƙasar, ƙarfe 16:30 kenan agogon GMT.

    A yanzu dai ana jiran sakamakon zaɓe daga Pennsylvania, wadda ita ce jihar da Joe Biden ke buƙata a halin yanzu ya lashe zaɓen ƙasar.

    A halin yanzu, Jam'iyyar Democrat wadda Mista Biden ɗin ke takarar a ƙarƙashinta na gaba a Jihar ta Pennsylvania da ƙuri'u 28.833.

  9. Kusan mutum dubu 20 sun fito zanga-zanga a Jamus

    Kusan masu zanga-zanga dubu 20 suka cika wani babban dandali a birnin Leipzig na Jamus, inda suke adawa da dokar kulle da aka sa sakamakon annobar korona.

    An kai wasu daga cikin masu zanga-zangar ne dandalin cikin motoci ƙirar bas daga wasu birane da ke makwaftaka.

    A baya dai birnin na Leipzig ya haramta zanga-zangar, sai dai wata kotu ta amince wa kusan mutum dubu 16 su fito zanga-zangar.

    Wani mai magana da yawun 'yan sanda ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa aka hana zanga-zangar shi ne kauce wa rikici.

    Wasu daga cikin masu zanga-zangar har da masu tsatsauran ra'ayin siyasa, da kuma masu ra'ayin gurguzu na Jamus.

    Rahotanni sun bayyana cewa mawuyaci ne a samu wani sanye da takunkumi cikin masu zanga-zangar.

  10. Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya ya bayar da umarnin kama Rahama Sadau

    Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta bayar da umarnin kamawa da bincikar fitacciyar 'yar fim ɗin nan Rahama Sadau, bayan wani ya kai ƙarar ta ga 'yan sandan kan wasu hotuna da ta wallafa da suka jawo ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).

    Sai dai a bayanan da BBC ta samu, 'yan sandan ba su samu nasarar kama Rahamar ba saɓannin yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito, amma majiya mai ƙarfi ta nuna cewa tana ƙoƙarin haɗa tawagar lauyoyinta da za ta je da su ofishin 'yan sandan domin kai kanta.

    Ga cikakken labarin a nan:

  11. An sako Naziru Sarkin Waƙa daga gidan yari bayan cika sharuɗan beli

    Kotu a Jihar Kano ta saki Naziru M. Ahmad da aka fi sani da Sarkin Waƙa bayan ya cika sharuɗan beli da ta gindaya masa.

    Sarkin Waƙa ya kwana a hannun a gidan yari ne ranar Alhamis sakamakon gaza cika sharuɗan da ya yi.

    Ɗan uwansa Misbahu M. Ahmad ya shaida wa BBC cewa rashin cika sharuɗan da wuri ne ya sa aka tsare shi a bayan kanta.

    Naziru ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Instagram yana gode wa masoyansa a yammacin jiya Juma'a.

    A ranar Laraba ne wata kotu a Kano ta soke belin da aka bai wa fitaccen mawaƙin nan Naziru Ahmed Sarkin Waƙa, inda ta gindaya wasu sababbin sharuɗɗan belin.

    Ana ƙarar Naziru ne kan zargin cewa ya saki wata waƙa ba tare da hukumar tace fina-finai ta Kano ta tantance ba.

    Sharuɗan sun haɗa da cewa sai ya kawo wani Maigari da zai tsaya masa da kuma Kwamandan Hizbah na ƙaramar hukuma a matsayin sharuɗan belin.

    Wani makunsancinsa ya ce sun cika sharuɗɗan, sai dai kuma ba a samu kai wa ga alƙalin da zai bayar da umarnin ba da belin ba saboda ya riga ya tashi daga aiki a lokacin.

  12. Majalisar Habasha ta rushe gwamnatin yankin Tigray

    Majalisar Dokokin Habasha ta kaɗa ƙuri'ar soke gwamnatin arewacin yankin Tigray a wata hatsaniya da ta rikiɗe zuwa tashin hankali.

    Cikin wani zama na gaggawa, majalisar ta ayyana gwamnatin Tigray a matsayin wadda ba ta kan doka sannan kuma ta rushe ta.

    A ranar Juma'a ne Firaminista Abiy Ahmed ya ce an kai hare-hare ta sama kan sansanonin soja a yankin.

    Ana fargabar rikicin zai iya kaiwa ga yaƙin basasa, wanda kuma zai iya shafar ƙasashe maƙwabta.

    Shugabanni daga ɓangaren Tigray sun mamaye Habasha na tsawon shekaru kafin zuwan Abiy Ahmed a 2018 bayan wata zanga-zangar ƙin jinin gwamnati, inda ya daƙile tasirinsu a gwamnatance.

  13. ''Yan sanda su yi amfani da ƙarfin da ya dace don tarwatsa masu zanga-zanga'

    Sufeton 'Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu ya umarci 'yan sanda da su yi amfani da "duk ƙarfin da ya dace" domin daƙile tashin hankali da zanga-zanga.

    Umarnin nasa na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa masu zanga-zangar EndSars na yunƙurin sake hawa tituna.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Asabar, Mohammed Adamu ya umarci dakarun rundunar da kar su ƙyale duk wani tashin hankali domin kare dukiyoyi da rayukan al'umma.

    Zanga-zangar ta EndSars mai neman kawo ƙarshen cin zalin da 'yan sandan Najeriya ke aikatawa, an fara ta ne a watan da ya wuce kuma an dakatar da ita ne bayan ta rikiɗe zuwa tashin hankali a sassa daban-daban, abin da ya jawo kisan mutum kusan 80 ciki har da jami'an tsaro.

    Daga baya buƙatun masu zanga-zangar sun sauya zuwa neman sauya tsarin yadda ake gudanar da shugabanci a ƙasar.

    Tuni hukumomi suka rufe asusun ajiyar wasu fitattu daga cikin masu shirya zanga-zangar. An karɓe fasfo tare da hana ɗaya daga cikinsu fita daga Najeriya sakamakon bincike da hukumomi suka ce suna yi a kanta.

  14. Me ya sa ake samun bambanci a lissafin sakamakon zaɓen?

    Na san ba za ku rasa ganin bambanci ba game da sakamakon zaɓen Amurka tsakanin na BBC da na wasu shafukan kafafen labarai.

    To yadda abin yake shi ne, shafuka daban-daban ka iya amfani da alƙaauma daban-daban, abin da zai sa a samu bambanci a lisaffin wanda ya lashe wata jiha tsakanin Trump da Biden.

    BBC na samun nata lissafin ne daga kamfanin dillancin labarai na Reuters ta hanyar kamfanin zaɓe mai suna Edison Research, wanda ke tattara sakamakon da za a sanar sannan kuma yake aiki da kafafen talabijin na Amurka a cibiyar National Election Pool.

    Me ya sa wasu shafukan ke cewa Biden ya ci zaɓe?

    A jiya, wani kamfanin bayar da sakamakon mai suna Decision Desk HQ ya sanar da Joe Biden a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya hasaso cewa zai lashe Jihar Pennsylvania. Saboda haka shafukan da ke amfani da alƙalumansa - kamar Vox da Business Insider- su mua sun bayyana cewa ya yi nasara.

    Kazalika, wasu kamfanonin da kafafe kamar Associated Press da Fox News sun hasaso cewa Biden zai lashe Arizona, abin da zai bai wa Biden ɗin damar samun ƙuri'un wakilai na musamman 264 - saɓanin 253 kamar yadda kuke gani yanzu a BBC.

    Har yanzu ba mu yi hasashen wanda zai lashe Arizona ko Pennsylvania ba saboda muna ganin ya yi wuri.

  15. Firaministan ƙasar Fiji ya bai wa Biden nasara, har ma ya taya shi murna

    Firaministan Ƙasar Fiji, Frank Bainimarama, ya bai wa Joe Biden nasara a zaɓen shugaban Amurka duk da cewa har yanzu ba a kammala ƙirga ƙuri'u ba.

    Shugaban ƙasar da ke yankin Pacific ya taya Biden murna a shafinsa na Twitter, yana mai fatan jam'iyyar Democrat za ta taimaka wurin ceto duniya daga haɗarin sauyin yanayi.

    Ƙasar ta Fiji na fitar da gurɓataccen hayaƙi ƙasa da kashi ɗaya cikin 100, sai dai tana fuskantar cikar kuguna da zaizayewar ƙasa da kuma guguwa.

    A ƙarƙashin gwamnatin Donald Trump ne Amurka ta zama ƙasa ta farko da ta fice daga yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi a hukumance.

    An ƙulla yarjejeniyar Paris ɗin ne a 2015 domin tsananta yaƙi da barazanar sauyin yanayi. Biden ya ce zai mayar da Amurka cikin yarjejenoiyar da zarar ya zama shugaban ƙasa.

    Taya murnar da Bainimarama ya yi na zuwa ne bayan Firaministan Slovenia Janez Jansa ya taya Trump murna ranar Laraba ta lashe zaɓen.

    Twitter ya saka gargaɗi a kan saƙon na Jansa yana mai cewa "babu tabbas ko hukumomi sun bayyana sakamako a loƙacin da aka rubuta wannan saƙo".

  16. Duk da cewa ba mu san wanda ya yi nasara ba, alamu na nuna cewa...

    Idan yanzu kuke shigowa shafin namu don sanin wanda ya lashe zaɓen, to barka.

    Duk da cewa mu ma jira muke, amma tabbas muna da abin da ya kamata ku sani - saboda cigaba ake yi da ƙirga ƙuri'un.

    Joe Biden na ƙara matsa wa kusa da ƙofar shiga White House, yayin da yake buƙatar ƙuri'ar wakilai na musamman guda 17 kacal kafin ya kunna kai cikin fadar a watan Janairu mai zuwa.

    Da ma dai 270 ake buƙatar ɗan takara ya samu, yanzu kuma yana da 253, yayin da Shugaba Trump ke da 213.

    Joe Biden ne kan gaba a jiha huɗu mafiya mahimmanci da suka rage zuwa yanzu:

    • A Jihar Pennsylvania, inda Biden ke kan gaba da ƙuri'a 28,883, tana da ƙuri'un wakilai na musamman mafi yawa (20) a cikin jihohin da ba a faɗi sakamako ba - kun ga kenan in ya lashe ta zai haura 270
    • Haka abin yake a Arizona, inda Biden ke gaban Trump da 29,861
    • Kai a Nevada ma fa haka zancen yake, tazarar ta kai ta 22,657
    • Sai dai kuma a Georgia, tazarar ba wata ta kirki ba ce, inda Biden ke kan gaba da 7,248 kacal. Jami'an zaɓe kuma sun ce sai an sake ƙirga ƙuri'un saboda tazarar ba yawa
  17. Ko akwai hukumar zaɓe a Amuka? Me ake nufi da Electoral College?

    Kamar yadda wasunku suka sani, ɗan takarar shugaban ƙasar Amurka ba zai samu damar shiga Fadar White House ba sai ya lashe ƙuri'a 270 ta wakilai na musamman wato Electoral College.

    Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tambayoyin da kuke yawaita yi game da zaɓe a Amurka.

    Daga cikinsu akwai ma'ana da kuma yadda Electoral College ke aiki, sai kuma hukumar zaɓe - akwai ta ko babu.

  18. Ba za mu ƙyale Isra'ila ta kafa sansani a kusa da mu ba - Iran

    Yayin da yake magana game da rikicin yankin Nagorno-Karabakh, wani mai magana da yawun rundunar sojan Iran ya ce ƙasarsa ba za ta taɓa ƙyale Isra'ila ta kafa sansanin soja a kusa da iyakarsu ba.

    A wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Mizan, Birgediya Janar Abolfazl Shekarchi ya yi magana game da rahotannin da ke cewa akwai ƙungiyoyin 'yan bindiga daga Syria a rikicin na Nagorno-Karabakh.

    "Ba zai taɓa yiwuwa a ƙyale shaiɗanu ba a wannan yankin da kuma 'yan ta'adda. Iran ba za ta taɓa yarda ƙungiyoyin abokan gaba ba," in ji shi.

    Gwamnatocin ƙasashen Rasha da Faransa da Amurka sun yi gargaɗin kasancewar ƙungiyoyin 'yan bindigar Syria waɗanda aka ce suna taimaka wa ƙasar Azerbaijani a yaƙin Nagorno-Karabakh tsakaninta da Armenia.

  19. Biden ya ƙara bai wa Trump tazara a Georgia

    Joe Biden na ƙara samun tagomashi a Jihar Georgia, inda ake fafatawa a cigaba da ƙirga ƙuri'un zaɓe.

    Cikin dare, ɗan takarar na jam'iyyar Democrat ne kan gaba da ƙuri'a 4,000 bayan an ƙirga kashi 99 cikin 100.

    Yanzu haka kuma Biden ya samu ƙari zuwa 7,248, kamar yadda BBC ta lissafa.

    Georgia (mai ƙuri'a 16 ta wakilan zaɓe na musamman) ta 'yan Republican ce a al'adance kuma wani ɗan takarar Democrat bai taɓa lashe ta ba tun shekarar 1992.

  20. Zanga-zangar EnSars ka iya rikiɗewa zuwa ta'addanci - Gwamna Zulum

    Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Bornon Najeriya ya ce zanga-zangar EndSars "ka iya rikiɗewa zuwa ta'addanci".

    Gwamnan ya shawarci matasa da su yi taka-tsantsan wurin neman haƙƙinsu game da cin zalin 'yan sanda, wanda ya ce "Boko Haram ma ta fara ne daga zanga-zangar ƙinin jinin saka hular kwano ga masu babura".

    Zulum ya bayyana haka ne ga manema labarai a jiya Juma'a jim kaɗan bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa ta Villa game da matsalolin tsaro.

    "Kun ga yanayin da ake ciki yanzu. Kusan mutum miliyan ɗaya ne suka rasa mahallansu kuma matasa da marasa ƙarfi abin ya fi shafa," in ji shi.

    "Wasu daga cikin waɗanda suka jagoranci zanga-zangar ba sa Borno yanzu haka. Suna Abuja ko Legas ko kuma ma ƙasar waje. Wajibi ne mu kula sosai."

    Shi ma Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya miƙa rahoton asarar da zanga-zangar EndSars ta haifar a jihar ga Buhari a jiyan.