'Mala'iku za su taimaka wa Trump ya ci zaɓe'

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan zaben Amurka da ma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Imam Saleh, Mustapha Musa Kaita and Halima Umar Saleh

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin:

    • Buhari ya nemi haɗin kan sarakuna don biya wa matasan Najeriya buƙatunsu
    • Georgia za ta kammala kirga ƙuri'u zuwa 12:00 na rana agogon ƙasar
    • Ana hasashen Biden zai lashe Jihar Wisconsin
    • Sanatoci na so Buhari ya daina zuwa asibitin ƙasar waje
    • Kotu ta yi watsi da buƙatar Trump na dakatar da ƙirga ƙuri'un Michigan
    • A dakata da ƙirga ƙuri'u in ji Trump

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. Man City vs Liverpool: Za su kece raini a Etihad karawar mako na takwas

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ranar Lahadi Manchester City za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan mako na takwas a Gasar Premier League ranar Etihad.

    Liverpool ce ta daya a kan teburi da maki 16, ita kuwa City tana 11 a teburin gasar bana.

    Ita dai City na fatan cin wasan Premier League biyu a jere a karon farko a shekarar nan, ita kuwa Liverpool idan ta yi nasara za ta hada mki 19 ta ci gaba da jan ragama.

    Ga cikakken labarin a nan:

  3. An saki malamai 11 da aka sace a Kamaru

    An saki malaman nan 11 da aka yi garkuwa da su a wata makaranta da ke arewa maso yammacin kamaru a ranar Talata.

    Wani jami'in makarantun coci a ƙasar ya bayyana cewa ba a biya ko sisi ba kafin sallamar malaman.

    An shafe kwanaki ana zanga-zanga a wajen sansanin da 'yan awaren suka ajiye malaman da suka sace.

    Labarin sakin malaman na zuwa ne rana ɗaya bayan an gudanar da jana'izar ɗalibai bakwai da 'yan bindiga suka yi wa kisan gilla a watan da ya gabata a makarantar su da ke Kumba a kudu maso yammacin ƙasar.

    Jami'an yankin sun ɗora alhakin harin kan 'yan aware waɗanda suka daɗe suna rikici domin ɓallewa daga yankin rainon Ingilishi na ƙasar.

  4. Kotu ta yi watsi da buƙatar Trump na dakatar da ƙirga ƙuri'un Michigan

    Wata alƙali a Jihar Michigan, ta yi watsi da koken da Trump ya gabatar na a dakatar da ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa ta hanyar akwatin gidan waya a jihar.

    Alƙalin, Cynthia Stephens, ta yi watsi da koken inda ta ce an makaro wurin gabatar da ƙarar - sa'o'i kaɗan kafin a kammala ƙirgar - kuma an kai ƙarar mutumin da bai kamata a kai ƙararsa ba kan lamarin- sakamakon sakataren harkokin wajen jihar bai da iko kan ƙirga ƙuri'un.

    Kwamitin yaƙin neman zaɓen Trump sun so a dakatar da ƙirgar ne har sai an samu wasu masu sa ido kan zaben 'yan Jam'iyyar Republican sun ƙaru a wurin ƙirgen.

  5. Saƙonnin WhatsApp za su iya ɓacewa bayan kwana bakwai

    whatsapp

    Asalin hoton, Getty Images

    Manhajar Whatsapp za ta fito da wani sabon tsari na bai wa masu amfani da manhajar damar ɓatar da saƙonnin da aka turo musu ko kuma suka tura bayan mako guda.

    Manhajar ta Whatsapp, wadda mallakar shafin Facebook ce, na da mutane masu amfani da ita biliyan biyu a faɗin duniya, haka kuma kamfanin ya ce wannan matakin zai taimaka wajen sirrinta saƙonnin da aka aika.

    Sai dai manhajar ta ce waɗanda aka aika wa saƙon za su iya su ɗauki hoton saƙon da aka turo musu ko kuma sake aika saƙon ko hoto ko bidiyon da ba sa so manhajar ta goge.

    Ana sa ran zuwa ƙarshen watan Nuwamba ne masu amfani da manhajar ta Whatsapp za su fara amfani da wannan tsarin.

    Ku latsa nan domin karanta cikakken labarin.

  6. Sanatoci na so Buhari ya daina zuwa asibitin ƙasar waje

    ..

    Asalin hoton, BAYO OMOBORIOWO

    Majalisar Dattawan Najeriya ta aika da gargaɗi ga fadar shugaban ƙasa kan kada Shugaba Buhari ya ci gaba da zuwa ƙasar waje domin neman magani.

    Sanata Ɗanjuma La'ah, wanda shi ke wakiltar Kaduna Ta Kudu, shi ne ya aika da gargaɗin inda ya ce asibitin fadar shugaban ƙasar zai gyaru ne kaɗai idan shugaban ya daina zuwa ƙasar waje domin neman magani.

    Sanata Danjuma, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar da ke kula da hulɗa tsakanin ɓangarorin gwamnati, ya aika da gargaɗin ne ga babban sakataren fadar, Tijjani Umar, a lokacin da ya hallara gaban kwamitin domin kare kasafin kuɗin 2021.

    Jami'in fadar shugaban ƙasar ya gabatar da kasafin biliyan 19.7 a kasafin 2021, kuma a cikin kasafin, za a yi amfani da biliyan 1.3 wajen gyara asibitin fadar shugaban ƙasar.

  7. Muna da yaƙinin Biden ne zai lashe zaɓe – Kwamitin yaƙin neman zaɓensa

    Abokin hamayyar Shugaba Trump a zaɓen Amurka Joe Biden, na kara samun rinjaye a muhimman jihohi a fafatawar da yake ta zama sabon shugaban Amurka.

    Shugabar yaƙin neman zabensa ta buƙaci jama'a su ƙara haƙuri sannan su kwantar da hankalinsu amma ta ce suna da yaƙinin cewa Mista Biden zai yi nasara a kan Trump.

    Ɗan kankanin rinjayen da shugaban ke da shi a Georgia na raguwa yayin da ake ƙara ƙirga ƙuri'u.

    Ɗan takarar Democrat yana da rinjayen da bai taka kara ya karya ba a Arizona da Nevada.

    Mista Biden a yanzu yana da kuri'u dari biyu da hamsin da uku na wakilai na musamman, abin da ke nufin yana bukatar ƙarin kuri'u 17 kafin ya samu damar fitar da Trump daga White House.

  8. Sakamakon baya-bayan nan na zaɓen Amurka

    Skamakon zaben Amurka
  9. 'Mala'iku za su taimaka wa Trump ya ci zaɓe'

    .

    Asalin hoton, TWITTER/ODAS

    Mai bai wa Shugaba Trump shawara kan harkokin addini, Paula White-Cain, ta jagoranci gudanar da addu'a inda take buƙatar "mala'iku" su zo daga Afrika da yankin South America domin taimaka wa Shugaba Trump cin zaɓe.

    Paula White, ta bayyana cewa tana jin ihu da kuma waƙoƙi na nasara.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙirga ƙuri'un zaɓen shugaban ƙasa a ƙasar, kuma ana cikin fargaba ganin cewa ɗan takarar Jam'iyyar Democrat, Joe Biden na kan gaba a zaɓen da ake ci gaba da kirga ƙuri'u.

    Mista Trump, wanda ɗan Jam'iyyar Republican ne, tuni ya fara zargin abokin karawarsa Joe Biden inda ya ce yana ƙoƙarin yin maguɗin zabe.

  10. Labarai da dumi-dumi, Ana hasashen Biden zai lashe Jihar Wisconsin

    Ana hasashen Joe Biden na Jam'iyyar Democrat ne zai lashe Jihar Wisconsin.

    Hakan zai ba Mista Biden ɗin ƙuri'u 10 na wakilan masu zaɓe kuma ya ƙara tazarar da ke tsakaninsa da Trump.

  11. Georgia za ta kammala kirga ƙuri'u zuwa 12:00 na rana agogon ƙasar

    Lamura na tafiya cikin sauri a Georgia ba kamar yadda aka yi zato ba a baya ba.

    Sakataren harkokin wajen jihar, Brad Raffensperger ya bayyana cewa akwai sauran ƙuri'u 90,000 a kammala a ƙirga a daren jiya, amma a safiyar yau, ya bayyana cewa ba su wuci ƙuri'u 25,000 suka rage ba a ƙirga.

    A wata tattaunawa da ya yi da WSB-TV a Atlanta, Raffensperger ya bayyana cewa: "Zuwa 12:00 rana na yau ya kamata a ce mun kammala," ƙarfe 17:00 agogon GMT.

    Ana sa ran yankin Fulton, zai kammala ƙirga nan da awa ɗaya.

    An ba Biden tazara da kusan ƙuri'u 18,000 a jihar, kamar yadda rahotanni ke nunawa.

    Idan Biden ya lashe Georgia, damar da Trump zai samu ta cin zaɓe idan za a je zagaye na biyu ta ragu matuƙa.

  12. Buhari ya nemi haɗin kan sarakuna don biya wa matasan Najeriya buƙatunsu

    ..

    Asalin hoton, Buhari Sallau

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi goyon bayan masu sarautun gargajiya wajen ƙoƙarin gwamnatinsa na biya wa matasan ƙasar buƙatunsu.

    A ranar Alhamis ne shugaban ya nemi hakan a wani taro da ya yi da masu riƙe da sarautun gargajiyar wanda aka yi a fadarsa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

    ''Mun ji koken-koken matasanmu da ƴaƴanmu kuma muna duba buƙatunsu,'' a cewar Shugaba Buhari.

    Ga cikakken labarin a nan:

  13. A dakata da ƙirga ƙuri'u in ji Trump

    A yayin da ake kai wa dab da samun sakamako, Shugaba Donald Trump ya wallafa saƙo a Tuwita cewa ''A DAKATAR DA ƘIDAYAR NAN"!

    A wani jawabinsa na ranar Laraba, Trump ya bayyana zaɓen a matsayin ''ha'intar Amurkawa'' ya kuma yi kira da ''a dakatar da ƙidaya,'' duk da cewa bai bayar da hujjar an yi maguɗi ba.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Tuni kwamitin ya ƙin neman zaɓen Trump ya shigar da ƙara don a dakatar da ƙirga ƙuri'u a jihohi da dama - ba tare da gabatar da hujjojin da ke nuna an yi maguɗi ba.

    Sannan kwamitin yaƙin neman zaɓen ya buƙaci a sake ƙirga ƙuri'un jihar Wisconsin.

  14. Hotunan jana'izar ɗalibai da malaman da aka kashe a wata makaranta a Kamaru

    Ga wasu hotunan jana'izar da aka yi wa dalibai bakwai da masu ɗauke da makamai suka kashe a birnin Kumba na yankin renon Ingila a ranar 24 ga watan oktoba 2020.

    jana'izar ƴan makaranta a Kamaru

    Asalin hoton, MMI Info

    jana'izar ƴan makaranta a Kamaru

    Asalin hoton, MMI Info

    jana'izar ƴan makaranta a Kamaru

    Asalin hoton, MMI Info

    jana'izar ƴan makaranta a Kamaru

    Asalin hoton, MMI Info

  15. An tsawaita dokar ta ɓaci a Tillabery ta Nijar

    presido Niger

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta sake tsawaita wa'adin dokar ta ɓaci da wata uku nan gaba a fadin jihar Tilaberi, da ke iyaka da Mali da kuma Burkina Faso.

    Hukumomi sun dauki wannan mataki ne a taron majalisar ministocin kasar, saboda abin da suka kira taɓarɓarewar lamuran tsaro a yankin.

    Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage ƙasa da kwanaki 40 da soma gudanar da babban zaben kasar.

  16. Ana ci gaba da daukar matakan kulle a Turai

    Turai

    Asalin hoton, Getty Images

    Girka ta zama kasar Turai da a baya-bayan nan ta sake sa dokar kulle domin hana bazuwar cutar korona.

    Firaministan kasar Kyriakos Mitsotakis ya ce dokar kullen za ta fara aiki ne ranar Asabar amma a wannan karon makarantun Firamare za su ci gaba da kasancewa a bude sabanin a lokacin da aka sa dokar a farkon barkewar annobar.

    An tilastawa akasarin kasashen Turai daukar irin wadannan matakan amma ba su yi hakan ba sai da cutar ta ta'azzara.

    Sannan kuma sa takunkumi ya zama dole musamman a cikin jama'a.

    Ingila ma ta saka dokar kullen a zagaye na biyu inda bankin kasar ya zuba kusan dala biliyan dari biyu don rage tasirin da dokar za ta yi kan tattalin arzikin kasar.

    Cyprus ma ta sake saka dokar hana fita cikin dare inda wuraren shan barasa da cin abinci da kuma shagunan kayayyaki za su rika tashi da wuri.

  17. Gobara ta tashi a wani gidan mai da ke Legas

    NEMA

    Asalin hoton, NEMA

    Rahotani daga jihar Legas na cewa gobara ta kama a gidan Man Oando dake unguwar Marine Beach a jihar Legas.

    Kawo yanzu babu rahoton samun asarar rai ko jikkatar wasu.

    Hukumar kashe gobara ta jihar da hadin guiwar sauran hukumomi na kokarin shawo wutar dake ci gaba da ci a yanzu haka.

    NEMA

    Asalin hoton, NEMA

  18. Tarayyar Turai ta caccaki Isra’ila sakamakon rushe girajen Falaɗinawa

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Kungiyar Tarayyar Turai ta yi kira ga Isra'ila ta daina rushe gidajen Falatsiinawa a gaɓar yammacin kogin Jordan.

    Isra'ila dai na ci gaba da lalata gidaje a kauyuka da kuma tantunan mutanen da ke zaune a yankin da ta mamaye.

    Kusan mutum tamanin, sama da rabinsu yara ƙanana sun rasa matsuguni.

    Masu sa ido na MDD sun ce an lalata gidaje da dama a abin da suka kira ta'adi mafi girma da aka yi cikin shekaru.

    Isra'ila ta ce an gina gidajen da ke kusa da Tubas ba bisa ƙa'ida ba a yankin da ake horas da sojoji.

  19. Kuri'un Trump na ci gaba da raguwa a jihohin da yake kan gaba

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Rinjayen da Shugaba Donald Trump ya samu na kara raguwa a Georgia - daya daga cikin jihohin Amurka da ke da matukar mahimmanci ga tabbatuwar burinsa na sake darewa kujerar mulki.

    A yanzu dai Joe Biden na ƙoƙarin kamo abokin hamayyar tasa duk da cewa akwai saura kusan kashi huɗu na kuri'un da ba a kirga ba.

    Masu sharhi kuma sun ce ragowar kuri'un da aka kada ta gidan waya da alamu za su fadaɗa damar ɗan takarar jam'iyyar ta Dimokrat.

    A Arizona ma Joe Biden ne ke da rinjaye sannan an bayyana shi a amatsayin wanda ya lashe jihar Michigan ana kuma tunanin ya yi nasara a Wisconsin.

    Wannan dai ya buɗe masa hanyar samun kuri'u 270 na wakilan kwalejin zabe da kowane dan takara ke bukata domin shiga fadar White House.

  20. An zartarwa mutane biyu hukuncin kisa saboda yi wa ƴar shekara 14 fyaɗe

    Ana yawan samun irin wadannan laifuka a Somalia

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Somalia ta zartarwa mutane biyu hukuncin kisa bayan samunsu da laifin yi wa wata matashiya ƴar shekara goma sha hudu fyaɗe.

    Mutanen da suka haɗar da Mohamed Abdi Faray da Abdirahman Mohamed Isaq sun amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa, da suka hadar da garkuwa da matashiyar da kuma yi mata fyaɗe a garin Bosaso.

    A baya-bayan nan dai ana samun karuwar irin wadannan laifuka a Somalia, sai dai mahukunta na cewa suna iya bakin kokarinsu don shawo kan wannan matsala.