A yankin yammacin Amurka sakamakon
farko na nuna cewa manyan ‘yan takarar biyu na ci gaba da kan-kan-kan a wurare
da dama.
Dan takara na bukatar kuri’u 270 na
kwalejin masu zabe domin lashe zaben shugaban kasa.
A yanzu haka Joe Biden na da kuri’u 192
a yayin da Donald Trump ke da kuri’u 114.
Ga yadda hasashe yake a tsakanin manyan
‘yan takarar:
·Joe Biden ana
saran zai lashe jihohi 14 ciki harda birnin Washington DC. Jihohin su ne Vermont,
Delaware, Maryland, Massachusetts, New Jersey, New York, Connecticut, Colorado,
New Mexico, New Hampshire, Illinois, California, Oregon, Jihar Washington da kuma
Washington DC
·Donald Trump ana saran zai lashe jihohi 17. Jihohin su ne Indiana, Kentucky,
Oklahoma, Tennessee, West Virginia, Arkansas, South Dakota, North Dakota,
Alabama, South Carolina, Louisiana, Nebraska and Nebraska 3rd District, Utah,
Missouri, Kansas, Wymong, da kuma Mississippi.