Facebook da Twitter sun ɗauki mataki kan Trump
Facebook ya mayar da martani game da iƙirarin da Trump ya yi maras tushe na lashe zaɓe.
Mai magana da yawun Facebook ya faɗa wa NBC News cewa: "Daga sanda Trump ya fara iƙirarin nasara, mun fara ɗago sahihan bayanai zuwa saman shafin Facebook da Instagram ta yadda kowa zai san cewa har yanzu fa ana tsaka da ƙirga ƙuri'a kuma ba a bayyana wanda ya yi nasara ba."
Har yanzu ana cigaba da ƙirga miliyoyin ƙuri'u a jihohin da fafatawar ta fi zafi kamar Pennsylvania da Michigan da Wisconsin da kuma sauran waɗanda ka iya sauya sakamakon zaɓen.
Jami'an zaɓe sun ce za a iya ɗaukar kwanaki nan gaba ba a sanar da wanda ya yi nasara ba a waɗannan jihohin.
Tun farko Twitter ya ɗauki irin wannan matakin domin daƙile maganganun Trump marasa tushe game da zaɓen.
Shafin ya maƙala gargaɗi a jikin saƙon da Trump ya ce - ba tare da wata hujja ba - "suna ƙoƙarin sace ƙuri'u".