Shugaban ƙasar Kamaru ya yi Allah wadai da kisan kananan yaran da aka yi
Shugaban ƙasar Kamaru Paul Biya ya yi Allah wadai da kisan wasu yara ƙanana da aka yi a wata makaranta a yankin rainon Ingila.
Shugaban yakira wannan harin a matsayin “rashin imani da kuma laifi kan yaran da basu ji ba ba su gani ba”.
Ya kuma ce ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar da an kama wadannan mahara don girbe abin da suka shuka.
Shugaban ya kuma aike sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan a shafinsa na Twitter:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Haka shi ma shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya shawarci hukumomi da su tabbatar sun nemo wadanda suka aikata wannan mummunan abu.
“Ya kuma yi kira ga duk wasu kungiyoyi masu rike da makamai da su guji kai hari kan fararen hula domin mutunta dokar kasa da kasa kan ‘yancin dan adam.






